17

96 6 3
                                    

_TSAKA MAI WUYA_
      _KHAIRAT Up_
         1️⃣7️⃣

_Freepage_

_vote@wattpadkhairi_muhd_

_hey! Guy's hope u re ll cool? Are you enjoying Tsaka mai wuya? If yes vote,share,and comment, this book is not for free to have your complete pages just pay #200 naira._

     Safeena ce zaune a gaba na yayin da ta ke ba ni labarin sabon saurayin ta Abeed Sageer dan kasuwa ne, kamar yadda ta fada min bata tsaya a iya nan ba ta ce ''kyakyawa ne,fari ne,ya iya daukar wanka ,yana da kirki da kula da mace ya na bata lokacin shi dari bisa dari kuma ta yards dashi zuciyan ta ya kwanta da shi.'' Na ce '' Na mata murna sossai Allah ya tabbatar da alkhairi. Ta ce ''watan da zai kama za ayi baikon su sossai na yi farin ciki da hakan kuma na nuna mata jindadi na ga me da wannan batu.

Kullum zata zo gidan mu muyi ta hira wani lokacin ma da yammaci tare muke zuwa exercise ni da ita wani lokacin kuma da Yaya Sadeek.

Duk bayan sati biyu in Yaya ya samu sarari ya na zuwa mu gana kuma na bashi kulawar da ya ke bukata tunda na riga da nasan kalan gwanin na wa.

A tsukun nan ne Yaya Aliyu yazo ganin gida kar kuso kuga yada na dinga murna da farin ciki ni kai na ban san Dalili ba ko dan mun jima ba Ku hadu ba? Ko kuma dan mun jima ba mu halin ba wato fada. Ranan da zai zo ina gidan Mummy muka yi mishi tuwon shinkafa miyar taushe ,muka yi mishi dambun shimkafa da kayan lambu a ciki da nikakken nama. Aka yi mishi zobo da kunun aya.Yaya Aliyu na son cimar gargajiya akan ta bature shi sa in zai zo in yana nan abincin shi kennan mun sha yin fada da Yaya Aliyu in Yaya Umar zai dawo to fa ranar ba maganan  girkin gargajiya sai su fried spageeti, fried rice, waye waye shi kuma bai so in ya dinga min mita da ciwon baki kaman zai dake ni wani bin ma sai ya ramkwashe ni ko kuma ya dunguri hanci na nace mishi eh din na ji ba komai ba za mu yi abincin da ya ke so ba ranan aiko wuni ya ke ya na ciwon baki da kunci ko ina ya ke karyawa oho?.

Ina zuba tuwo a Leda ina mulmulawa ina murmushi har sai da Mummy ta ce ''Ha'a Hajiya Shahida wannan fara'ar fa? Kar dai kice min sabida Aliyu ne?.''

Dariya na yi na ce ''Mummy Wallahi na yi kewar fadan shi sossai shi sa.''

''Lallai kam kina da aiki sai kuyi tayi ai.''

Dariya na yi mata kurum muka ksrasa aikin mu.

Da yamma likis Yaya Aliyu ya shigo gida lokacin na koma gida dan na gaji na ce wa Mummy zsn dawo in na yi sallah na huta. To kun san mai ciki ina wanka da ruwan dumin nan ko mai ban shafa ba sai barci.

Bayan sallar magariba Yaya ya zauna ya na cin abinci lomar farko ya kalli Mummy ya ce mata ''Mummy wai wannan yarinyar bazata daina shiga shirgi na ba ko?.''

''Hah! Wa kennan?.''

''Shahida mana.''

''Yanzu kuma me ta yi maka?.''

''Ji shirman girkin da ta yi min.''

''Ai ka San dandanon ta kennan kai Aliyu Neman magna wannan abincin ai bai da aibu kuma tare muka yi da ita ,malami ka ci abincin ka kaje ka huta ka kwanta ban san korafin tsiya.''

Ya ce shirman abinci amman ya tashi da malmalar tuwo da damunbun plate guda guda lolzzz. Sai da ya gama tas tukuna na shigo ina mishi wani irin harara na ce ''Mummy wai ya na ga an tashi da plate biyu na shirman yarinya?.''

Mummy ta gyada kai ta mike ''can Ku karata ban da lokacin shirman nan na ku. Nayi nan.''

Haka ta hau sama ta bar mu muna ta aikawa juna sakon harara da tsaki.

Jin na yi tsaki ya sa ya zaburo na mike da Sauri na yi baya rike da ciki ina mishi dariya.

''Wallahi Shahida ki kiyaye ni ba aure ba ko tattabara ce a kan ki zan sauke miki rashin kunya a kan ki.''

''Oho wani ma ya zama tattabarar mana in da hali ai auran ma rabo ne wanda beda rabo sai ya mutu ko ya kare a gauwro sabida bakin hali da muni.'''

Be kula ni ba kawai ya shige dakin su.ina nan har Daddy ya dawo ya tambayeni jiki na ce ''Alhamdulilahi'' , ya ce ba na jin komai ko na ce mishi ''eh'' shi ma ya haura sama ni kuma na tashi na yi waje na koma gida ko sallama ba mu yi da Mummy ba.

*

Yarinyar nan baza ta taba barin cikin rayuwata ba , nayi nesa da ita a banza ,kullum.tunanin ta addabata ya ke yi mtsw mesa zuciyata bazata bar ni na huta da son maso wani ba ?.

Dakin shi aka bude .Juyawa ya yi ya ga waye.Mummy ce ta ce '' Au ka kadai ina Shahida?.''

Saida ya yamutsa fuskar shi kan ya ce ''Mummy mai zai kawo ta dakia?''

No na yi tunanin kuna hira ne.

Allah ya sauwaka.

Dariya ta yi sossai sannan ta ce OK maybe ta fi gida ka fito ga Daddyn Ku ya dawo sai Ku gaisa.

Mummy dole sai yanzu?.

Aliyu!ban san iskanci stand up and go and greet your father shirmaman banza da wofi kawai tashi kafin raina ya baci.

Shi kennan ba sai Kin yi ta ihu ba har ya ji yaji dadi kina min fada zan je amma sabida ke.

Aliyu Allah ya shirye ka kawai zan ce.

Amin.

TSAKA MAI WUYA(a complicated love story)Where stories live. Discover now