16

65 7 2
                                    

_TSAKA MAI WUYA!_
      _KHAIRAT UP_
            _1️⃣6️⃣_

_Freepage_

*

Ban yi kokarin ce mishi komai ba kuma na ji bakin cikin marin da ya yi min ba dan komai ba sai dan a gaban wannan matar ya yi min marin. Kun san wani abu kuma? Wallahi ban ji haushin marina da Yaya ya yi min ba ni a tunina kila akwai abin da na mishi ko kuma ita bakuwar bai kamata na yi mata abin da na yi mata ba din hakan ya sa cikin zuciya ta na dinga yin addu'oi ina ambaton sunan Allah kada shaidan ya samu nasara a kai na har ya d'arsa min wani mugun tunani a kan Yaya na kuma sai na ji ji wasai abu na ba bu wata damuwa.

Shahida kin san wace wannan  da ki ka wulakanta? Tamkar ni ki ka Wulakanta. Ji na yi kirjina ya yi min wani irin nauyi na ce ''Dan Allah ka yi hakuri Wallahi ban isa na raina ka ba ka yi hakuri kuskure ne ka ji?.''

Bani zaki bawa hakuri ba wadda kika yi wa ita zaki bawa hakuri.

''Ki yi hakuri kuskure aka samu bazan kuma ba.''

Ta ns harara ta ta ce min ''ta wuce nan gaba in kula da yadda zan na wa mutane.'' Ns ce ''Nagode zan kiyaye insha Allah.''

Amira ki zauna ba ri na cire uniform mu ci abinci sai ki huta ko?.

Shi kennan Umar sai ka fito nima dai ins bukatar na kimtsa.

Ohk Shahida ki nuna mata daya dakin ta gyara.

Toh bismillah!.

Haka ns raka ta ns nuns mata komai na fito ina sakin ajiyar zuciya.

Bin shi na yi dakin ya na cire uniform na amshe na ce ''Ka yi hakuri ka ji ? Kar ka yi fushi da ni kasan ban san bacin ran ka ko kad'an wannan ma akasai aka samu ban san ta na da muhummanci a wurin ka ba ne shi ya sa.''

Juyowa ya yi ya na fuskanta ta sai ya ji tausayi na da kunya ta a lokaci guda rungume ni ya yi a kan fadaddan kirjin shi wanda na ke matukar so kuma ns ke kaunar na jini a jiki a koda yaushe.

Ki yi hakuri ns mare ki.

(Murmushi na saki dan na san daman Yaya na bazai min komai Dan ya muzantsni ba shi sa ma ban ji haushin shi ba.)  Yaya kar ka wani damu ni fa ban ji haushin komai ba Wallahi ,ban wani damu ba ai kana iya min hukunci indai na yi laifi.

Shaheeda wani irin zucuya gare ki? How do u do all this?.

Murmushi kawai na yi na ce in dai ka na tare da ni zan iya jure komai a kan ka.

''Am sorry!''

Hakan nan da na ji wannan Kalmar sai na ji sanyi da dadi a raina na ce mishi ''Nifa ba bu abin da ka yi  min stop saying sorry kawai ka ce I love you.''

Dariya ya yi sossai ya jawo ni jikin shi again ya ce ''Wannan yarinyar sunan ta Khadija Sa'ad Imam(Amira).Ita kadai iyayen ta suka mallaka ogan mu gaba daya ta sojoji ,Amira kawata ce mahaifinta ya yi min hallaci da taimako a rayuwa kuma ya na so na sossai jinin mu ya hadu da juna sossai hakan ya sa ya yarda da ni ya ba  ni amanar yar shi da kulawa da ita kasancewarta sangartaciya kuma er lele babu abin da ta iya na addini sai dai boko,clubing da shaye2 ni ne nan na ja ta a jiki na har na sauya da'biun ta sanda suna nan garin kamin Sir ya yi retire tana zuwa ina mata karin karatun addini kuma Alhamdulilahi ta na saurin ja.Ta nuna ta na so na amma na karya mata lagon ta na ce mata ina da mata kuma an kusa kawo min ita tun Kafin na sanar da ke ina son ki wato tun ina sakin son ki a raina.''

Kissing din kumatun shi na yi kar ka damu Yaya na zan kula kuma zan bata kulawa sossai muddin haka shi je farin cikin ka.

Nagode Mata's ba na son wani ko wata ya koma da korafin kin Wulakanta shi.

Yes sir! Na fada ina Sara mishi.

Gashi ja ya yi kissing tare muka  fita falo na gyara mana wurin cin abinci .

Amira ta fito cikin shiga ta Riga da wando sai dai ta sanya karamin hijab a kai ta doso mu ni kuma da fara'a na tare ta .

Zaunawa tayi muka zuba abinci muna ci muna hira.

''Amira ki yi hakuri dan Allah kin ji a kan dazu .''

''Ba komai Shahida rashin fahimta ne ya gifts ni ma ina mai ba ki hakuri a kan abinda na fada.''

Ba bu komai.

Amira ke da waye kika zo Kaduna?.

Ni da Mummy ne saidai ta je kano ne ni kuma ban gan ka ba bazai yuwu na shigo Kaduna ban gan ka ba kuma ban taya ka murnar aure ba.

Kin kyauta.

Amma gobe zan wuce dan jibi zamu wuce Cairo da Mummy ni ma shirye shieyen biki na ake yi.

Murmushi ya yi ya ce ''wow wane wannan da ya riki tuta.''

Ta dan yi  Jim ta yamutsa fuskarta ta ce '' uhmmm ni ma dai ina ga asiri ya min dan ya doke son da na ke yi maka fa sossai.''

Daman can son be kai zuci ba.

Amarya Shaheeda ki kanainaye kirjin shi ta ko ina ba ya ganin kowa kin yi sa'a ki rike shi da kyau dan akwai kurayen shi a waje rututu.

Nagode kawai na ce na mike na koma kan kujera na bar su suna hira. Saidai kasan raina babu dadi kawai haushin yarinyar na ji ina ji sossai amma ba bu komai lokaci ne .

   (Hmm! Shaheeda sanyin ki ya yi yawa!.)

Washe gari ta tafi ni kuma muka je asibiti aka min gwaji dan ban ji dadi ba amai na kwana ina yi.

Gwajin farko na jini ciki ya bayyana nan take Yaya ya sa aka yi min scanning aka ga wata hudu ne cikin sossai na yi mamakin yadda ban farga ba kuma ban yi laulayi ba sai dai na sauya nayi kiba.

Dadin da Yaya ya ji bazai fadu ba ni kunya ma ya dinga ba ni hatta Daddy sai da y kira ya fada mishi na yi mamaki sossai ashe suna iya yin irin wannan hirar da Daddy? Lallai Daddy ya sauko sossai.Ina zsune ya kira Yaya Aliyu ma ya fada mishi shima ya nuna farin cikin shi.

Cikina na da wata takwas Mummy ta yi ma Yaya futufutu ya maids ni kano zuwana farko kennan tun aure na da Yaya Umar . Gidan Yaya na na wuce duk yadda Mummy ta so na zauna a wurin ta ki na yi.Kullum muna waya da Yaya ina yake gaya min yadda ya ke kewata sossai haka nima.

TSAKA MAI WUYA(a complicated love story)Kde žijí příběhy. Začni objevovat