06

77 6 1
                                    

*Hazak'a Writers Association*

*Tsaka Mai Wuya*

*Khairat Up*

           0️⃣7️⃣

Dariya Aliyu ya yi kafin ya ce ''Amin Mummy na'.

Mummy ta ce ''Ban san yadda aka yi Daddyn Ku ya ke barin Aliyu ya ke yadda ya ga dama ba? Gaba d'aya ba ya yi maka fad'a sai Umar d'ina kawai ya takurawa' ta fad'a ta na shafa kan Umar,shi kuma Umar ya langabe kansa alamar shi din abin tausayi ne.

Aliyu ya tafa hannayen shi sannan ya ce 'ai Mummy ba tun yau ba ni na san ba ni da me ji da ni a gidan nan a matsayina na d'an auta ba a nan-nan da ni sai dai Yaya da kuma Aunty Sabarina ni kuma ko oho to ku san da sa ni gidan granny zan koma sai Ku sakata ku wataya in na koma can.'

'Oho maka kai ka sani ka fi ruwa gudu.' Inji Mummy.

Murmushi ya yi ya kwanta kan kujera me zaman mutum uku ya kunna tv da remote da ke kan center table ,ya kai tashar B4U movies sannan ya kalli Mummy ya ce ''Nima Mummy fa ban damu da ku kula da ni ba ai na saba rayuwa ni kad'ai kin manta boarding ku ka kai ni?.''

Umar ya riga Mummy magana '' Aliyu mazan fama Allah Ya huci zuciyar manya Mummy ma tsokanar ka ta ke yi ai kowa ya san kai ne babban Mummy (sunan Mahaifinta gare shi). Ji ta ke da kai baba sama baba kasa ni ne dai d'an bayan fage.''

Aliyu ya ce 'Au haba dan Allah?.''

Nan suka zauna kuma suka yi ta hira ,tare suka ci abinci har Mummy ta riga su tafiya ta kwanta dan ta ga hirar  ta su ba me karewa ba ce .

'Yaya Umar' Aliyu ya kira sunan dan'uwan shi.

Na'am Auta!.

Yaya ina so na tambaye ka wani abu.

Allah Ya sa na sani.

In Sha Allah ma ka sani Yaya.

Yaya kwana biyu ina lura da kai a kan abubuwan da ka ke yi ,na lura akwai wani abu tsakanin ka da Shahida ban San me ye ba amma na san abu ne me girma ,ina so yanzu ka fad'a min me ye tsakanin ka da Shahida?.

Ko kad'an Umar be yi mamakin furucin d'an' uwan shi ba saboda ya san Aliyu mutum ne me hangen nesa. Saida ya nisa sannan ya furzar da iska ya maida hankalin shi kan kanin shi sannan yace mishi ''Aliyu ban yi mamakin gano ni da ka yi ba amma ina so ka sani ina son ta amma na san bazan same ta ba.''

Aliyu ya ce ''Saboda me?.''

Saboda Daddy ba zai yarje min yin aure yanzu ba.

Kana jin abinda ka ke fad'a kuwa? Yaushe za ka maida kan ka mutum wanda ya isa da kan shi? ,yaushe zaka fara daukarwa kan ka hukunci da kan ka? ,yaushe zaka fara yin abin da zuciyar ka ta ke raya maka?, Yaya Umar wannan rayuwar ka ce kai kad'ai ka wuce yaro kuma ka na aikin ka ,kuma albashin ka Alhamdulilahi .''

''Aliyu duk abin da ka fad'a haka ne amma ka sani Daddy shi ne komai na mu ,shi ne jigon mu,dole mu yi abin da ya ke so,shi ne ya ke da iko a kan mu ,ya na da iko a kan a kan komai na mu da ni da kai da ma kowa da ya ke rayuwa cikin gidan nan dole ne mu bi iyayen mu ,mu yi musu biyayya matukar umarnin su be sa'bawa Allah ba dole mu yi shi saboda haka Aliyu ina so ka sassato ka daina gani ko Daddy ba ya son mu Daddy ya na son mu shi ya sa ya ke nuna isa a kan mu. Hum! Sai da ya sauke ajiyar zuciya tukuna ya cigaba da magana Aliyu na ban fad'awa Shahida ina son ta ba tukuna saboda ina so na kuma nutsuwa tukuna na ,na samu muhalli,na samu soyayyarta tukuna sai na fad'awa Daddy ina son na yi aure kafin nan ka ga ita ma ta yi nisa a karatun ta.

Aliyu ya bi yayan shi da kallo sannan ya ce 'Wane irin so ka ke yi mata?.'

Bazai fad'u ba Aliyu son da na ke yi wa Shahida bazai fad'u ba amman dai na san ina son ta sossai fiye da yadda ka ke tsamani ina na rasa Shahida zan rasa nutsuwa ta komai nawa zai dagule zan iya yin komai saboda Shahida ban san ina da karfi ba sai da Shahida ta bani 'kwarin gwiwa a kan aikin soja duk yadda Daddy ya so na yi aikin ban maida hankali a kai ba amma Shahida ce ta yi ta 'kwarara min gwiwa ta nuna min ta na son na yi aikin kuma gashi har na saba da shi kuma ina jindadin shi.

Jikin Aliyu ya yi sanyi bazai iya yin takarar soyayya da yayyan shi ba sai dai yana mika rokon shi ga Allah Ya zaba musu mafi alkhairi dan ya san Yayan shi mutum ne me rauni ba shi da d'aukar damuwa zuciyar shi me rauni ce . a fili ko cewa ya yi ''Allah Ya za'ba abin da ya fi alkhairi Yaya zan taya ka da addu'a komai zai zo ya zo da sauki.''.

'Amin!'

Yaya bari na shiga na huta fitar sassafe zan yi gobe Monday.

Toh shi kennan sai da safe.

Allah ya tashe mu lafiya.

Amin!.

*

*Bayan Wata Biyu*

A cikin wannan wattanin abubuwa da dama sun faru ciki harda komawar Umar bakin aikin shi kafin ya tafi sai da ya fad'awa Shahida abin da ya ke ji game da ita kuma ba ta ba shi kunya ba ta amince mishi duk da bai da waya sai da ya siya wannan komawar da ya yi kullum in ya samu lokaci da dama ya kan kira Shahida su yi hira ko kuma su yi charting ta watsaap a wannan lokacin sossai suka shaqu da junan su. Yayin da kuma al'amarin  Aliyu da Shahida kullum kara gaba yake yi ta fannin fad'a ba sa jituwa kullum sai Aliyu ya tsokane ta wani zubin ta rama wani zubin ta yi kuka dan Aliyu akwai cinkisa shi ko yana jan ta da tsokana ne kawai dan ya ji muryar ta ko ya ga kwayar idan ta ko kuma ta kula shi wad'anan abubuwan ya ke ajiyewa cikin zuciyar shi da kwanyar kan  shi be daina son ta ba kuma bazai iya furta mata ba saboda d'an uwan shi Umar zai iya yin komai don farin cikin yayan shi wani lokacin ya kan kulle kan shi a d'aki yayi kuka shi kad'ai.

A cikin shekara biyu Umar ya zamo wani babban mutum komai na samartaka ya kara bayyanan mishi girma ya kuma lullube shi ya samu nasarori da dama dan yana da kaifin tunani ga wayo da dabarun ya'kin dan haka team din shi suke ji da shi sossai dan ta dalilin dabarun ya'kin shi sun yi nasarar cafko abokan gaba da dama.

A yanzu haka Umar na da matakin luitanent kuma a karkashin shi ya na da team kadhi hudu team A_D duk a karkashin jagorancin shi.

Aliyu kuma sun kamala makaranta yanzu haka yana bautar kasa a Kogi state da gangan ya ki neman canji na dawowa Kano saboda ya na son yin nesa da Shahida.

Shahida kuma suna level 3 a northwest ta dage ta na karatu sosai dan Yayan ta ya tsaya mata da kakarsu Hajiya Inna.

Daddy ma ya yi retire kuma ya na alfahari da Umar dan ya maida kai sosai a kan aikin tunda gashi har ya samu karin girma saboda kokari da jajircewar shi ba tare da sa hannun kowa ba a cewar shi nasarar shi ta shi ce shi kad'ai ba bu sa hannun kowa a ciki. Tsakanin shi da Aliyu ko gaisuwa ce kawai ba ma ganin shi ya ke balle su saba to shi Daddyn ma tun asali ba ya zama cikin iyalin shi su yi hira ko ya ji  matsalar su abu d'aya ya sani 'Duty first family next'. Ba wai tsakanin shi da Aliyu ba ya damun shi ba ne aa ya na damun shi amma lokaci ya 'kure bazai iya maida hannun agogo baya ba.

TSAKA MAI WUYA(a complicated love story)Where stories live. Discover now