10

60 5 2
                                    

_TSAKA MAI WUYA_
          _KHAIRAT UP_
              _1️⃣0️⃣_

_wannan littafin na kud'i ne_

_Vote@wattpadkhairi_muhd_

_free page_

Rana ba ta karya sai dai mafadin ta ya yi a yau ne aka soma rabon iv na bikin Umar da Shahida ta ko ina ba sauki ba ga amarya ba kuma ba ga ango ba dan kai ya dau zafi. Wani irin fitinannan kyau Shahida ta yi dan gyara sossai ta ke samu daga wurin aunty Farida (matar yayyan ta Sadeek an yi bikin su shekara biyu baya da suka wuce bayan ya samu aiki a NNPC kuma ysron su daya.) Fatar ta me kyau da sulbi ta kuma samun gyara sai ta zama tamkar wadda ska sauyawa kamanni ko aka maidata balarabiya.

Sun fito daga gidan su Safeena ne suka yi ragas da tawagar ango wato abokanan shi. Wani irin kallo ango ke bin ta da shi wanda sai da ta ji kunya dan ta sa ni sarai angon na ta ba daga nan bari wurin sakin kayi yanzu sai ya bankado mata abin kunya cikin mutane shi sa tayi wuff ta dauke idanuwan ta daga wurin su ta na murmushi ,Safeena ta ce '' kalli abin ki yarinya wa zai shiga tsakanin Ku zs ki wani yi mana gulma wai dauke kai.'' Mintinin ta Shahida ta yi ta sa hannun ta na sosa wurin dan yayi mata zafi sossai shi ko gogan na ta kallo ya bita dashi tamkar idanuwan shi zasu zazzago kasa dan kallo ,bushewar da aka yi da dariya ce ta dawo da shi hayyacin shi. Wani abokin su ya ce ''Shege Umar Aziz Wallahi ka ji tsoron Allah!.''

Dariya suka kuma yi suna raharsu su ma.

A kan kwana suka hadu da Aliyu ko daga ina ya ke oho ko da suka yi clashing tsokanan shi Shahida ta yi ''Kai baza ka zo ka kwashi gaisuwa daga wurin matar wan ka ba ko?.'' Hararta ya yi ya ce ''Na bi matar wa da gudu kinga Shahida ki bar ni hakan nan ji barki kamar wata dodaniyar ruwa ko yar aljannu ko kyau ni Wallahi ban san me yaya zai yi da ke ba buzuwa da ke kawai.''' Hararshi ta yi ita ma ta ce ''oho dai a haka dai aka gani aka manne yan bakin ciki su rungumi transformer.''

''Safeena ki yi gaba da wannan a bar dan Allah ni duk kunya ma na ke ji ana gani na da ita bayan ana ganin mutunci na.''

Aiko Shahida ta kufulo ta soma yi mishi tsiwa da rashin kunya kamar zata Zane shi yadda ta ke dagewa shi dariya ma fifikarta ta ke ba shi Wallahi har yau dai bazata daina tsiwa ba da tsokana ita fa ta tsokano shi amman dan ya maids mata da martani ta ke mishi haka bari ya kuma harzuko ta.'' In ji Aliyu.

''Kan ki ake ji wai Mahaukaci ya fada rijiya na wuce misalin ki daga ke har wannan sojan mijin na ki Aliyu na ke yarinya ba ragon namiji ba.''

Safeena ce ta ja hannun ta suka yi gaba ''Ku kullum in kuka hadu sai kun yi wannan bala'in haba da Allah ya kamata Ku girma.''

''To sannu innarmu''.

''Au kai na zaki dawo ?''

''Me sa zaki janye ni ba ki bari na rama ba?.''

''Sabida bamu da lokaci ko kin manta abinda mu ke yi?, and kin manta ke ki ka fara tsokano shi?.''

Harar ta galla mata sannan tayi tsuka kamar za ta guntule bakin ta ya yo kasa ta yi gaba.

''Ke dai ki ka sani''In ji Safeena.

*

Aliyu ko wani irin sanyin dadi yaji a ran shi da ya gan ta sossai ta mishi kyau wani irin kishi dan uwan shi ke nukurkusar shi da kuma mamakin kan shi wato shi So ba bu ruwan  sa duk yadda ya so ya yi da kai hska ya ke yi ba cin hakan wa ya ke da a doron duniya sama da yayyan shi Umar? Shi ya sa ya nesanta kan shi daga garesu gaba daya amma duk da haka abin ba bu sauki yanzu ko da ya gan ta sai ya ji wani abu ya doki kirjin shi.''

*

''Dazu fa Mata's kin gama tafiya da ni totally kasa controlling din kai na nayi a gaban su Fahad.''

''Hah!,kai soulmate ni din me na yi da ka kasa controlling kan na ka?.''

''Kin ga yadda komai na ki ya fita I was like gaskiya ns yi dace 100%.''

''Ni kuma na ji haushi fa sabods yadda abokanan ka suka dinga binmu da kallo.''

''Ai ni ko banga aibun hakan ba ya kamata su San matar Umar Azizi ba a bar wasa ba ce ba, ba a banza na kamu da son ki ba.''

Abun da ke hada ta da yaya Umar kennan bai dauki kishi a komai ba burin shi a ce komai na shi is perfect bai san abinda za a kushe mishi wannan shi ne babban matsalan shi wayewa ta yi mi shi yawa,sau da dama Yaya Aliyu kan yi mata fada a kan mayafi ko kaya matsattsu shi kuma yaya Umar encouraging.....katse mata tunani ya yi ta hanyar ce wa ''Soulmate na ji kin yi shiru ko kin fara barci ne?.''

Da kyar ta ce ''Aa ido na biyu Wallahi kawai dai gajiya.''

''Ayya to ki kwanta ki huta ban san na ga amarya ta da wrinkels abokai su min dariya.''

'OK! Sabida abokanan ka ne ka ke so na yi kyau ba don kai ba?.''

''Sai kuma ya duburburce no! Ba haka ba ne kin san ai ke ce first ni za ki yi wa adon na yaba ko?.''

''Seda safe''.

''OK Allah ya tashe mu lafiya.''

''Amin!''.

TSAKA MAI WUYA(a complicated love story)Where stories live. Discover now