20

176 12 10
                                    

_________________________
       _TSAKA MAI WUYA_
           _KHAIRAT UP_
                _2️⃣0️⃣_

_vote@wattpadkhairi_muhd_

_Asalamu Alaikum ,ina mika gaisuwata da dumbin godiya ga masoya na da wanda na sa ni da wanda ban sani ba ina gaida ku. Wannan shafin zai kasance shafin karshe na free page din litaffin Tsaka Mai Wuya domin ki mallake shi zaki biya #200 kacal 👌._

Domin samun na ki za ki biya ta wannan account din 2098372249
UBA, Sani Ummulkhairi Panisau sai ki turo shaidar biya ta wannan number din don't a sa ki cikin group din  0906 585 6251. Ko kuma ki turo Latin Mtn na #200 ta wannan number din  0906 585 625.

_________________________

*

Wannan rana ita ce ake kira da ba'kar rana don kuwa a ranar na rasa bangare guda biyu wad'anda suke jigo na rayuwata,ban taba kawowa kaina hasashen wannan lokacin ba ,ban taba kawowa kaina zan rasa Yaya Umar ba balle Aliyu karami ba a rana guda in na tuna cewa ki ce sanadin rasa Jnr sai na ji daman ni na rasa rayuwata na bi Yaya Umar d'ina mu hadu a can mu biyu......ban ida tunani na ba wasu zafafafan hawaye suka zubo min a lokacin kuma aka bud'e d'akin aka shigo,fuskokin su kawai na kalla na ji komai ya dawo min sabo a hankali idanuwana suka sauka kan Yaya Aliyu ya rame ya fad'a sai idanuwan shi da suka fito zuruzuru dasu kamar baddo da lafiya Lou ne sai na tsokane shi son raina sai dai yau ba ranar farin ciki ba ne ba rana ne na bakin ciki a tartare damu.

''Sannu Shahida sannu kin ji?.''

Kai na kawai na gyad'a tamkar kadangaruwa ina jin tausayin kowa.

''Shahida ina ke miki ciwo?'' In ji Mummy.

Na ce mata ''Ba ko ina kawai ina son zuwa gida ban san zaman asibitin nan.''

Yaya Aliyu ne ya ce ''Dole sai sun baki sallama zamu wuce da ke in kin koma gidan mai zaki yi a can ?.''

''Ni dai Ku maida ni gida ban.....''

A dan kufule ya ce ''Baza a koma gidan ba tunda ke taurin kai ki ka iya.''

Na sski kuka sossai Mummy da Aunty Farida suka dafa ni ta hagu da dama suna rarrashi na.

Ba zato suka ji na ce musu ''Sun mutu ko? Na rasa su duk su biyun ko? Shi kennan bazan kuma ganin su ba? Hatta Jnr bazan kuma jin d'umin shi ba?.''

Sai lokacin Mummy ta saki hawayen ta suka zubo tamkar daman jiran ta ke yi aka rasa mai rarrashin wani a cikin dakin.

''Da hannuna na kashe Aliyu da hannun........'''

''Ke wace iriyar shashasha ce? Ba ki da hankali ?ke kin isa ki kashe rai daman? Kaddara ce kuma Allah ya rubuta iya kwanakin shi a duniya kenan ban san ki kuma yin shirme irin wannan lokacin su ne ya yi Allahn da ya hallice su ya amshi abin shi sai ki bisu da addu'a kawai ita ce gatan da za ki yi musu kar ki kums kokarin danganta kan ki da rashin Jnr  tsautsayi ne kuma haka Allah ya rubuta ki kwantar da hankalin ki insha Allah komai zai daidaita Allah ya jikan su da rahama.''

''Suka amsa da Amin.''

A cikin raina ko cewa na yi ta yaya zan saki raina na rasa mijina kuma na rasa d'ana?.

Ban san ma sanda na ce ''Yaya ya ce min ya na hanya zai dawo na shirya mishi kayan tarbar shi ,ya ce min ya na so na yana tare dani a ko wane hali bazai barni ba mesa ya karya alkawarin shi? Me yasa zai tafi ya bar ni bamu yi rayuwar da nuka tsara ba? Ya ce min sun ci galaba a kan abokan gabar su zasu dawo ni dai Yayana bai rasu ba yana nan naji a jikina ina tare dashi.''

TSAKA MAI WUYA(a complicated love story)Where stories live. Discover now