01

333 19 2
                                    

_TSAKA MAI WUYA_
           _KHAIRAT UP_
                  0️⃣2️⃣
*Vote@wattpadkhairi_muhd*.

    A gidan su Safeena suna zaxzaune yaya usman yana yi musu lesson din maths da shahida,safeena,abida duk suns fahimtar karatun shi sabida a tsanake yake koya musu yana level 2 a university din bayero yake .

Tashi suka yi suks yo alwala dan sallar magariba sun idar suna addu'a umman su safeena ta kawo musu abinci suna ci suna yar  hirar su .

Umar ne ya shigo bayan yayi sallsma an amsa mishi da fullas a hannun shi.

Suka hada baki lokaci guda suka gaida shi 'yaya umar ina wuni?'ya amsa musu shima yana Dan murmushi 'lafiya Lou yaran umma da inna an gama lesson din ne?.' Suka yi dariya sannan suka ce 'eh mun gama sai gobe insha Allah'. To madallah Allah ya yarda. Ina kanwar yaya yar shagwaba?. Shaida tayi dariya ta ce 'kai yaya umar ni ba na shagwaba fa' ,yayi dariya ya shige ciki wajan umma ta na kallo a sunna tv. Umman mu ta fi ta kowa. ''Ah Umaru sannu da zuwa ya gida ina mummyn taka?.' Yayi dariya ya tsunguna 'mummyna ta aiko ni wai in kawo miki funkasau'. Kai hajiya kulthum kennan akwai hiduma bata gajiya da abin alkhairi  kace mata nace 'Nagode Allah ya kara budi ya sa ta fi haka.' Yace 'Amin Umma ai na ga yaran ki a falo suna lomar tuwo nima a Sam min in tafi dashi kin san hitlar na hanya kar ya ga bani nan allurar decipline ta motsa.' Dariya umman tayi sannan ta ce ja'irin yaro kawai daddyn naka kake cewa hitlar?.'. '''',hmm umma kennan wallahi daddy ko a tannin takura number guda ne wallahi sannan kuma kinga ya gama sawa a ran shi sai nayi sojan nan nima kums kin fi kowa sanin bana so ki ga fa su usman sun yi gaba sun bar ni duk suna level 2 ni ina nan sai nayi force'''' yadda ya fadi maganar kasan baya so kwata kwata.  Tace '''babu komai umar Allah zai yi maka albarka kuma zai baka nasara sabida biyayyar da kake yi wa iyayen ka ,kayi hakuri zaka ga nasara a gaba ka daina tunanin ko takura maka yake yi aa ya san ya isa da kai ne shi yasa yake nuna iko da isa a kan ka,ksyi mishi biyayya kawai umar komai lokaci ne.'''' Umma to daman ya zan yi ai dole na hakura ki zuba min in je dashi. ''To Aliyu na can ya manta damu.''' Ai kusan dawowa shi ai dan gatan daddy ne.tace ''' kai ma haka'''.

Ta zuba mishi tuwo ya zo tafiya saida ya tsokani Shahida ita kuma tayi dariya kawai ta  mike ta ce '''yaya umar tsayani mu tafi tare ka raka ni gida kar Yaya na ya damu ko kuma be dawo da wuri ba shi sa bezo ya dauke ni ba. ''' hah umma ai na gaya miki wannan yar gata ce wai sai an zo an dauko ta ko a raka ta nan da bayan layi kai Shahida.''''''. Dariya akwai tayi suka fita tare bayan tayi musu sallama. Har gida ya raka ta suka gaida da inna tace '''yau kai ta samo kennan to nagode saida safe ka gaishe da umman taku''' zasu ji inna ke kuma yar shagwaba saida safe. Ta yamutsa fuska sannan ta ce '''bana so fa yaya umar'' ya kwaikwayeta shi ma '''bana so fa yaya umar''' tayi murmushi ta koma daki shi kuma ya fita.

**

Saida ya hadiyi yawu da ya shigo gidan su ya ga takalmin Daddyn su da kyar yayi ta maza ya shiga ciki saidai aka ci sa'a be same shi a falo ba haka ya bashi nasarar shiga kitchen da gudu ya ajiye sakon umma ya shige dakin shi ya watsa ruwa ya sako singilet da boxer's ya fito falo ya koma kitchen again ya juyo tuwon shi ya sa a plate ya soma ci a kan dinning dake nan falo.sai da ya gama tas sannan ya shiga dakin da suke motsa jiki ya samu ruwa ya zuba a jikin shi har fuska sannan ys soma motsa jikin. Ba a fi minti talatin ba Daddyn nashi ya sauko daga dakin shi shima cikin shi ga ta motsa jikin da alama dokar shi ce yin hakan, a hankali ya ce '''very good keep it up jeka huta na ga ka jima kana yi kou?''''. Shi kuma iya haki kaman wanda ya Dade kan injin.

30 minutes Daddy yayi sannan ya shiga yayi wanka ya kuma saukowa ya kalli news sannan ya kira umar.

Da azama ya fito daga dakin shi cikin shiri na barci sannan ya tsuguna a kasa '''Daddy!''''.

My boy ka soma shiri next week zamu wuce an gama yi maka komai.

Wani irin abu ya doki kirjin umar Allah ya sani besan wannan force din kaman zai yi kuka haka ya ce '''Yes Daddy'''.

Shi kuma yace '''Good ina so kayi kokari sossai kaji kou ban san ka bani kunya a matsayi na me babban rank a cikin wannan sabgar kar ma ka soma yi min shirme ka nutsu ka kama wannan aikin da zuciya daya kaji ko?''''.

'''Yes Daddy insha Allah bazan kunyata ka ba.''''.

'''Good boy,you can go na gama magana ka soma shiri duk wani abu da zaka yi kayi cikin daga nan zuwa juma'a daga nan kuma .....ka gane ai. '''

'''Yes Daddy amman ina so ka kaini muyi sallama da Aliyu da aunty sabarina kamin na tafi.'''

'''Wannan ba komai ba ne jibrin zai kai ka.'''

''Nagode Daddy.'''

'''Go to bed ''.

''Yes Daddy.'''

TSAKA MAI WUYA(a complicated love story)Where stories live. Discover now