YAR'AIKI

1.5K 55 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸

      *YAR'AIKI*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*~Love and romantic story~*

*STORY AND WRITTEN BY FATEEMARH ZAHRA EEDREES*

*whattpad @Eedreesfateemarh*

*Sadaukarwa ga kawa yar'uwa wato Zeey kumurya,nagode sisi wanan page nakine kiyi yarda kikeso dashi*

®🌁

*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..📚📚*
{{Ƙungiya Domin wayar da ƙan mata , Farin jini writer's domin ci gaban, Mata.}}

         ★{{F.J.W.A}}★📖🖊️

https://www.facebook.com/Fajin-jini-writers-association-109611777388680/

*31_32*

Babu komai qawas,abinda na miki ayanzuh be kai kwantan kwacin abinda kikamin a makaranta ba,amma yanzuh abu daya nikeso dake,kinsan miyeshii?

Girgiza kai tayi kamar wata karamar yarinya,cikin muryar ta da bata fita sosai tace"Aah bansaniba.

"So nike mucewa mommy fyade yamuki ranar babu kowa agidan,yace kizo ki gyara masa daki,kinacikin gyara ya afka miki,saboda banason tagane kinbasa hadin kai daga baya.kuma bestie kema da lefinki miyesa kika biye masa?bayan kinsan ba sonki yike ba,dan dayina sonki wlhy baze bata ki ba,gashi yanzuh yabarki da ciki,yina can wata kasar yina holewarsa dawasu yan'matan,ze kuma iyacewa ba dansa bane kuma ta zaunu,takarasa zancenta tana goge siririn gwalar data zubomata kan kuncinta

Cikin kuka feenart tace"wlhy sisi bansan miyesa nike yar'da da jalil ba,duk ranar daya nemin sena biya masa bukatarsa,yakaiga ko ganinsa inbanyiba banjin dadi...,takarasa tana fashewa da kuka.

Kara janyota jikinta tayi tana bubuga mata baya ahankali,tace kiyi shuru kinji,ko min darendadewa gaskiya zatayi halinta,ta fada tana zubda kwalla.

Sunfi rabin awa juwairiyya na lallashin ta kafin suka wanke fuskarsu suka bi lafiyar gado,duk da barcin ba dan dadi sukeyinta ba especially feenart dan batayi barcin arziki ba.ita juwairiyya rabi da rabi tayi.

        *************

*KADUNA GARIN GWAMNA*

Aban garen hajiya ko bayan ta kore nafeesa,khareema takira tace tazo tasameta yanzuh-yanzuh.

Cikin tashin hankali aunty khareema tace hajiya lafiya?dan yar'da taji muryar mahaifiyartasu ta tabatar akwai matsala.

Kede nace kizo inajiranki ynxuh nan.bata jira me zatace ba takashe wayar.

Cikin sauri aunty khareema ta shirya ta nufa gidan hajiya.ko baby inteesar a gurin me aikinsu tabarta.tana isa gidan afalo tadin ke hajiya tayi tagumi.

Hajiya naganinta ta mike kamar an tsireta ta janyo hanunta suka zauna a daya daga cikin royal chairs din dake zube a falon.

Aunty khareema tace"hajiya lafeaa?

"Uhm ina lafiya?yarinyar nan nafeesa taje ta kwaso mana cikin shege.

A tsorace aunty khareeema ta dago ta kalli hajiya,jin maganar tayi kamar a mafarki tace cikiiii kuma hajiya?

Eh mana ciki tayi harnan doctor yazo ya dubata.

Kai amma fa da mamaki,domin nafeesa nitsatsiyar yarinyace,sedai in fin karfinta akayi.

Hmm,itadai ta sani nidai na koreta Daga gidana.

Innalillahiwa'inna ilaihirraji'un,aunty kareema ta furta cikin tsananin tashin hankali,haba hajiya yaxakiyi haka,yarinyar dabata da kowa,se mu se Allah.

Bakya tunanin tashiga duniya kota fada hannun daba nagariba.....

To kinsan metacene dayasa nakoreta,hajiya ta katseta cikin karaji.

"To hajiya me tace" aunty kareema ta fada jikinta asanyaye.

Kedai bar tsintanciyar mage,cewafa tayi jalil ne yamata.

Jalil kuma hajiya,

"Shidin,banda iskanci me jalil zeyi da *yar'aiki*"

Amma hajiya dakinyi binkice domin tabbas biri yayi kama da mutum dan akwai ranar da jalil da nafees.....

Kinga malama dakata,kema sharrin zakiyiwa dan'uwanki,tsabar ke shashace Mara hankali.

Hajiya ba haka bane,maganar gaskiyafa ayita idan tazo,dakin.....

Cikin bacin rai,hajiya ta katseta,bakiranki nayi kikara batamun raiba,tashi kibar mun gida.

Amma hajiya....

Nace kibarmun gida,banason kara jin komai daga bakinki,hajiya ta karashe zancen da mikewa tabar mata falon

Cikin takaicin halin mahaifiyarmahaifiyartata,ta mike jiki a sanyaye ta fito.

Zuciyarta cike da tsananin tausayin nafeesa,inama zata ganta,data taimaketa,aunty kareema har hawaye seda tayi saboda tausayin nafeesa.

         

          ********************

          *JALIL*

      Abangaren jalil kuwa hankalinsa gaba daya atashe yake,saboda kiran nafeesa dayake bata dagawa daga baya kuma wayarma gaba daya tadena shiga
Shikuma baze iya koda tambayar hajiyabama,saboda yasan halin ta
Hakan yasa zuciyarsa tabasa shawara kawai yaje naija nadubo ko lafiya take
Yauma kamar kullum yana zaune yana aikin tunanin nafeesan,yaji wayarsa na ruri. Yana dubawa yaga hajiyarsace,cikin zumudi ya daga domin jiyake kamar koda muryar nafessat dinsa zeji.

Hajiyata yanzu nake zancenki araina sekuma ga kirankinan.

Ayya my son ykk ya aiki?

Lpy klu dafatan kowa lafiya,

Kowa lpy klu.

Yayi tunanin zata masa zancen nafeesa amma seyaji shiru bata masaba,hajiya jibi zan shigo insha Allah.

Aaaa lpy kuwa zaka taho kana tsaka da aiki?

Hajiya sonake kawai inzo inganki nayi kewarki sosai,insha Allah jibibi zaki ganni.

Tom shikenan Allah ya kaimu lafiya.

Ameen momcy,sukayi sallama.

Yau jalil ze dawo gida,hajiya ita ta zage tanawa autannata girke girke kala kala,da su drinks.

Karfe 2 jalil yasauka a Nigeria zuciyarsa fess da farin ciki yau ze ga masoyiyarsa abin kaunarsa nafeesat.

~*pls sister's comment nikeso kamar ruwa,kuma ina Baku hakuri kwana biyu kunjini shuru*~

*Real farhana*😍😍

~*pls share*~🙏

YAR'AIKIOn viuen les histories. Descobreix ara