YAR'AIKI

1.6K 21 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*YAR'AIKI*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸

~*Love and romantic story*~

*STORY AND WRITTEN BY FATEEMARH ZAHRA EEDREES*

*whattpad @Eedreesfateemarh*

*page 21-22*

*INAWA MASOYAN YAR'AIKI BARKA DA INDEPENDENT DAY💃💃*

®🌁

*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..📚📚*
{{Ƙungiya Domin wayar da ƙan mata , Farin jini writer's domin ci gaban, Mata.}}

★{{F.J.W.A.}}★📖🖊️

https://www.facebook.com/Farin-Jini-Writers-association-101140968266505/

*Bismillahi rahmani rahim*

Murmushi kawai yayi mata sanan yafada mata magungunan dazata siyo tadunka shansu zata samu sauki abinda takeji insha Allah.

Ta siyo tana sha amma,abinda ke bata mamaki shine yau tsawon wata daya kenan bataga period dinta ba.takarawa jalil maganan.

yace ai bawani matsala bane daman yakanyi hakan.

Tagamsu da abinda ya fada shiyasa tacire damuwan abin a zuciyarta.

Yau yakasance friday,nafeesa tatashi dawani mugun zazzabi,dan koda asuba a daddafe tayi sallah dan wani mugun jiri datakeji,ko data idar a kan sallayan barci yadauke ta.

A bangaren hajiya ko taji nafeesa shuru har gari yayi haske,gajiya tayi da jiranta shiyasa ta nufa dakin.
Akwance ta isketa kan sallaya,kusa da ita taje ta dan rusuna hanu takai dan tashinta,amma me setaji jikinta zafi rau kamar wuta,kamar karta tasheta sekuma taga yanayin kwanciyarta beyiba zesata ciwon jiki,tashinta tayi.

Ido tabude ahankali,batasan lokacin da baci yakwasheta ba,gashi yanxuh rana tafito."ina kwana hajiya?

"Lfea lau nafeesa,yanaji jikinki da zafi bakijin dadi ne?

Dagamata kai tayi hade dacewa"eh wlhy tun jiya nike fama da zazzabi ga jiri.

Kallonta hajiya tayi sosai sanan tace"toh shikenan ki kwanta a kan gado bari nakira doctor mu'az.

Tashi tayi dakyar tanufi gado,ta kwanta.

Itakuma hajiya,tafita dan kiran doctor mu'az.

Ba'a wani jimaba doctor mu'az yazo.

Hajiya ce tayi masa iso zuwa palo,bayan sun gama gaisawane tace"doctor daman nafeesa ce me aiki na babu lafeaa.

Doctor mu'az ne yagyara medical glass din dake idonsa yace"ohk meke damunta?

"Cemun tayi zazzabi kuma tana jin jiri.

"Ohk tana inane yanxh?

"Tana dakinta,tafada hade da tashi"bari infada mata tashirya zaka shigo.

Dakin nafeesa tanufa,koda tashiga still barci ta tarar da ita tanayi,tashinta tayi,sanan tafada mata tashirya doctor ze shigo dubata.

Tashi tayi tagyara jikinta hade dasa hijjabin sallahnta.

Hajiya da Dr-mu'az suka shigo,kallonta yayi sosai,a iya nazartarsa kamar ciki ne da nafeesa amma de bari yamata gwajin masu ciki,dan tabatarwa.

Dan karamin roba yabata sanan yace taje tayi futsari aciki takawo masa.

Amsa tayi,tayi kamar yar'da ya umarceta,sanan takawo masa.

Amsa yayi,sanan yacewa hajiya zeje yadawo.

"Toh shikenan,amma abin duk yadaure Mata kai dan a iya saninta masu ciki akewa wanan text din.

Bayan doctor mu'az yadawo ne yafito da wani envelope yace wa hajiya"ga result din text din danayi.

Amsa tayi taciro farar takardan dake ciki tasoma karantawa.......

*more comment*
*more typing*

*Real farhana😍😍*

~*pls share*~🙏

YAR'AIKIWhere stories live. Discover now