YAR'AIKI

1.5K 46 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸

      *YAR'AIKI*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*~Love and romantic story~*

*STORY AND WRITTEN BY FATEEMARH ZAHRA EEDREES*

*whattpad @Eedreesfateemarh*

*_Wai'inda basu karanta page 27-28 ba zasu iya duba whattpad yina can😺😺_*

®🌁

*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..📚📚*
{{Ƙungiya Domin wayar da ƙan mata , Farin jini writer's domin ci gaban, Mata.}}

         ★{{F.J.W.A}}★📖🖊️

https://www.facebook.com/Fajin-jini-writers-association-109611777388680/

*page 29-30*

      *Bismillahi rahmani rahim*

Mommy ce tatashi ta hadawa feenart abinci takai mata atire.....

Bayan tagama wankane taci abincin da mommy takawo mata.

Zee baby ko duk ta makal-kale mata.

Itako Juwairiyya takosa zee ta yi barci su samu su zanta da feenart.

Sune har wajan 11pm sanan barci yadauke zee.

Juwairiyya ta kinkimeta ta kaita kan gadonta hade da mata addu'an barci ta shafa mata tagyara mata kwanciya(pls sis arunka kulla da yara wajan barci su,bawai kin shinfide yaro ba kema ki kwanta a'ah kimasa addu'a,kobadan komaiba kariyace agaresa,baze dunka mugayen mafarken da yara suke ba,pls adunka kiyayewaaa).sanan ta dawo ta zauna suna fuskantar juna da feenart.kallonta juwairiyya tayi kafin tace"bestie me kikawa hajiya da har takoreki daga gidanta?

Feenart tabude baki zatayi magana,amma kuka yaci karfinta,tafara kuka tana me cin rai.

Rungumota juwairiyya tayi tana bubuga bayanta alamar lallashi,tace"dan allah kidena kukanan,ko so kike nima inyi?,tafada cikin raunan niyar murya kamar zatayi kuka.

Girgiza kai taahiga yi tace"Juwairiyya ciki ne dani,ciki ne dani har na tsawon wata 2,kuma.....

Ai bata bari ta karasa ba,tace"feenart ciki!!!,ciki kikace fah?.

Feenart cikin kuka tace eh hade da daga mata kai at desame tym.

Innalillahi wa inna'illahi raji'un,juwairiyya tasanar da ubangiji,tana tafa hanuwanta,tace cikin wayeee?

Cikin kuka feenart tace"tace jalil.(niko nace feenart yaudin ma babu yayan).

Ya jalil ne,tafada tana zaro ido waje.

Ta daga mata kai kamar wata karamar yarinya.

Hawaye ne yafara zubowa juwairiyya kan kuncinta tace shikenan yanxuh hajiya tasan cikin waye?

"Eh tasani,amma bata yar'da ba,wai me danta zeyi da *YAR'AIKI* irrina,nan tabawa juwairiyya labari tun daga farko har iyau.

Janyota jikinta tayi,tana bubuga mata baya tace kiyahkuri bestie insha allahu gaskiya zatayi halinta,insha allahu dakafafunsu zasu zo nemanki,kuma karki damu nan gidanma gidankune,anan zaki zauna har allah yasaukeki lafea,kuma muyi rainon danmu agidanan nasan mommy da daddy zasu fahimta,tafada hakan tana murmushi yake wanda hausa sukace yafi kuka ciwo.

Feenart tadago kanta hade da riko hannun juwairiyya tace"Bestie bansan dawani irrin baki zan gode miki ba nagode,nagode sosai.

Babu komai qawas,abinda na miki ayanzuh be kai kwantan kwacin abinda kikamin a makaranta ba,amma yanzuh abu daya nikeso dake,kinsan miyeshii?

~*_sis babu yawa ayi manejii_*~

~*sis comment nikeso kamar ruwa,nasan kuna kokari amma akara dagewa*~😉😉

*more comment*
*more typing*

*Real farhana😍😍*

~*pls share*~🙏

YAR'AIKIWhere stories live. Discover now