YAR'AIKI

1.5K 37 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸

       *YAR'AIKI*
  🌸🌸🌸🌸🌸🌸

~*Love and romantic story*~

*STORY AND WRITTEN BY FATEEMARH ZAHRA EEDREES*

*whattpad @Eedreesfateemarh*

*Page 23-24*

~*SISTERS ZAKUGA KWANA BIYU BANYI UPDATING AKAN LOKACI,WLHY BANDA LFEAA NE,CIWON NE SEYA DUNKAMIN ON AND OFF*~

®🌁

*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..📚📚*
{{Ƙungiya Domin wayar da ƙan mata , Farin jini writer's domin ci gaban, Mata.}}

      ★{{F.J.W.A.}}★📖🖊️

https://www.facebook.com/Farin-Jini-Writers-association-101140968266505/

     *Bismillahi rahmani rahim*

Amsa tayi taciro farar takardan dake ciki tafara karantawa"doctor ciki!!!!,tafadi hakan hade da tashi tsaye.

Doctor mu'az ne ya tashi tsaye yace eh hajiya abinda result yanuna kenan she's positive.

Wasu zufane suka fara ketowa hajiya duk da sanyin A.c dake falon"kuka har na tsawon wata 2 da rabi!!!.

Eh nima abin yadaure mun kai.

Hajiya bata tsaya sauraran shiba tawuce tana fadin zan maka transfer.

Yace ohk sanan ya kama gabansa.

Hajiya harda gudu take ta nufi dakin nafeesa.

Akwance ta tarar da ita nafeesa tana barci.

Wani mugun duka takai mata tana fadin tashi tashi tsohuwar munafuka.

Nafeesa dake kwance tayi firgit ta ta tashi,dan dukan yashugeta sosai.

"Uban waye yamiki ciki?,hajiya tafadi hakan tareda janyo nafeesa tafada kasa.

Nafeesa dataji maganar kamar a mafarki,ciki?,innalillahi wa ina'illahi raji'un shikenan jalil ya cuceta.

Hajiyace ta kuma daka mata wani tsawa nace wa yamiki ciki?

Ciki?,hajiya ni banda ciki wlhy bandashi.

Wasu tagwayen maruka hajiya ta watsa ma nafeesa ajere,tace"toh dan ubanki cikin tsintarsa akeyi kokuma haka kurin yake shiga?

Hawaye ne suke bin kuncin nafeesa,tana kuka tace"hajiya banda ciki wlhy zazzabine kawai.

Saboda tsananin haushi da yakama hajiya batasan lokacin da tafara dukan nafeesa ba tana hamabarinta ta ko ina.

Ihu take tana bata hakuri.

"Zaki fadamin uban daya miki ciki koko Sena kashe ki agidanan?

Kuka take tana fadin"wlhy hajiya banda ciki danallah kiyakuri,kimin rai.

Hajiya taga kamar dukan datake mata baya shiganta batasan sanda ta tasar da ita tsaye ta shake mata wuya hade da mana ta a bango.

Tari tafara tana kuka tana bawa hajiya hakuri amma ina,batasan sanda tafara fadin"jalil ne yamin ciki,wlhy jalil ne yamun ciki.

Dasauri hajiya tasaki wuyanta tana fadin"jalil,yanzuh jalil zaki kallawa sheri toh karyarki tasha karya wlhy,dana ba mazinaci bane,yama rasa wace zeyi zina da ita se *Yar'aki*.

Hajiya ta janyo hanun nafisa tana janta,nafisa tana bata hakuri,amma ko sauraronta batayiba.seda takaita kofar geat sanan tayarda ita,tace"karki sake inkara ganinki acikin gidana.

Kuka tafara yi tana bata hakuri ko sauraronta batayiba ta wuce abinta.tana shiga takwallawa mai gadi kira.

Ya zo dagudu ya durkusa,yina fadin"gani hajiya.

Karka sake inga nafeesa tashigo gidanan inba haka ba dakai da ita sekun barmun gida,kana jina?

"Eh hajiya.

Juyawa tayi cikin fushi tanufi falo tana zuwa ta zube akan kujera hade da rike kanta tana fadin"shiyasa wani lokaci katausayawa mutun ma matsala ne.mema jalil zeyi da kuca ka irrin ta a matsayinta na *YAR'AIKI*.

A dayan bangare ko nafeesa tayi kuka tayi kuka harta godewa allah,ta tsinewa jalil tunda take bata taba nadamar bawa jalil kanta ba kamar yau,yanzuh matsalar ta daya ne ina zataje?

*more comment*
*more typing*

*Real farhana*😍😍

~*pls share🙏*~

YAR'AIKIWhere stories live. Discover now