Chapter 2

1.8K 168 13
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

      *LAYLERH MALEEK*

*Writting by*
Phatymasardauna

               *Wattpad*
         @fatymasardauna

#Generalfiction

                *Chapter 2*

Tunaninta ne ke neman juyewa, tamkar yanda taji duniyar na juya mata, idanunta ta kuma rumtsewa da ƙarfi, ƙoƙarin furta wani abu take amma takasa, saidai laɓɓanta dake motsawa ahankali, sannu ahankali bugun zuciya da fitan numfashinta suka soma daidaita, kyawawan idanun ne suka soma ƙauracewa ganinta, hakan yasa ta soma sakin ajiyar zuciya, idanunta ta buɗe
asanyaye ta maida hankalinta ga takardan dake gabanta,  duka questions ɗin da aka rubuta,  babu wanda batasan answer'n saba, saboda  tayi karatu sosai akan test ɗin,  hakan ne yasa  cikin mintuna ƙalilan ta gama amsa tambayoyin.

Teemah dake ta faman rubuta masa shirme acikin paper'n ne ta kuma jawo Hijab ɗinta,   cikin ƙasa da murya tace.   "Laylerh wai bazaki juyo bane, kinataji ina miki magana tun ɗazu."
Laylerh kam bata juyo ba, yima tayi kaman bataji Teemah'n ba, tasan Teemah sarai ƴar rigima ce, yanzu tana juyowa kuma shikenan bazata saketa ba har sai tasa malami ya gansu, maybe ace ma suje suyi kneel down awaje.

Ganin Laylerh bata juyo bane yasa Teemah ta saki ƙwafa, abayyane tace "Wallahi zanyi maganinki Laylerh."  

Mumurmushi kawai Laylerh tayi, tasan halin mutumiyar tata sarai, fitinanniya ce, karatun ma bawai ya wani damunta bane.
 
Mintuna 30 kacal teacher David yace suyi submit, nan yasoma bi line by line yana amsan papers ɗinsu.

Yana ƙarasowa kan Laylerh ya miƙa mata hannu alaman ta bashi paper'n nata, miƙo masa tayi kaman yanda ya buƙata, saidai batare da ta yi aune ba taji ya shafo hannunta, da sauri ta ɗago idanunta ta kalleshi, gani tayi ya wani irin lumshe mata ido, harda lashe laɓɓansa.
Da sauri ta janye hannunta, jin tacire hannunta daga nasa ne yasa shi wucewa sit ɗin Teemah, idanunsa da suka soma sanja kala ya watsawa Teemah harda ƙarin harara, cikin faɗa faɗa yace.  
"Ke bani takardanki."   
Miƙa masa takardan tayi, yana amsa ya juya ya tafi.
Har yakai bakin ƙofar fita daga cikin  ajin ya juyo cikin kakkausar murya yace.
"LAYLERH MAHMOUD GWANI, by 10:00 am kizo office ɗina kisameni."   Baijirayi me zata ceba ya fice daga cikin ajin.

Yana fita Teemah tayi saurin dawowa sit ɗin da Laylerh ke zaune, wani duka ta kai mata tare da cewa.  "Yamiki kyau uwa da uban ƴan latti, wai ke kam Laylerh yaushe zaki daina latti ne?." 
Idanunta masu kyau taɗan lumshe, tare da shafa cikinta da taji yana murɗawa, cikin zazzaƙar muryarta tace. 
"Nibansan meke damunki ba Teemah, wallahi kina da takura, ɗazu da kike ta damuna mezan miki ne?."
"Bansani ba ɗin ƴar rainin hankali."  Teemah tafaɗa tana me gyara zamanta, idanu ta zubawa Laylerh'n, dan ganin wani bushashshen hawaye kwance akan fuskarta.
Hannunta ta kai kan fuskar Laylerh'n ta shafa hawayen, asanyaye tace.  "Kuka?."  
Shiru Laylerh tayi, tare da sunkuyar da kanta ƙasa. 
Kai Teemah ta girgiza, tare da ɗaura hannunta  akan kafaɗan Laylerh'n, cikin kulawa tace. 
"Yau kuma meya sameki, harda kuka?."
Kai Laylerh ta jijjiga alaman ba komai.
Baki Teemah ta cije, tare da cewa "Hmmm kima daina ɓoyewa Laylerh damuwarki abune nayau da kullum, ya riga daya bi jikinki dole sai angane saboda haka kima daina wahalar da kanki wajen ɓoyewa, yauma bakiyi break fast ba kika fito ko?."
Still idanunta taɗan lumshe tare da jinjina kai, alaman "Eh."    Ajiyar zuciya Teemah ta sauƙe, cikin tausayin ƙawartata tace. 
"Ni narasa wace irin rayuwa akeyi agidanku Laylerh, bansan meyasa ake miki haka ba, babu wani mutum ɗaya da yake kulawa dake acikin gidannan, bakya taɓa jin daɗi sai Abbu na nan, suna kyararki suna miki abu kaman ke ba jininsu bace, always suna barinki kina yawo da yunwa, daidai da school wannan baza'a sa driver ya kawoki ba, sai idan Abbu na nanne ma watarana kike samun arzikin shiga mota,  wallahi Laylerh ƴan gidanku basu da kirki, more especially Momy."  
Saurin toshe mata baki Laylerh tayi, hawayen da suka cika idanunta ta goge, cikin raunin  daya bayyana mata tace. 
"Kada kice haka Teemah, bansan meyasa ba raunina baya ɓuya, ako da yaushe ni me rauni ce akan damuwa ta,kada ki bari damuwata ta dameki Teemah, because damuwata ta yau da kullum ne."

LAYLERH MALEEK Where stories live. Discover now