Chapter 10

3.1K 158 51
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
Phatymasardauna

*Wattpad*
@fatymasardauna

#Destiny

*(Alhamdulillah! Tabbas ina godiya agareku masoyana, musamman yanda kuke nunamin ƙauna kuma kuke nunawa labaraina, haƙiƙa inajin daɗin hakan, bani da abun ce muku sai godiya, sannan ayau inason sanar daku cewa littafin LAYLERH MALEEK ya tashi daga free book ya dawo na kuɗi, daga wannan pagen kuwa zan dakata da baku free pages, duk wacce takeson samun cigabansa tofa saita biya, inaso kusan banyi hakan dan na ɓata muku rai ko kuma kuga kaman nayi rashin adalci ba, no bahaka bane Laylerh Maleek mallakina ne kuma ina ƙaunar baku duk wani labarina amatsayin free, saidai tanadin danayiwa Laylerh Maleek yasa bazan iya ci gaba da sakinsa free ba, saboda haka am sorry to say, ga waƴanda suke buƙatar cigabansa 300 ne kacal, sannan zaku iya turamin kuɗin ta hanyar account number, ko kuma katin MTN na 300. Ga wacce ta turamin kuɗin ta account number saita min screenshot dan nagani na tabbatar zaku iya tuntuɓana ta Whatsapp Number na 07069917168. Ga kuma Account Number na kamar haka. 0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Ja'iz Bank Kada ku manta na faɗa muku cewa salon Laylerh Maleek daban yake, duk yanda kuke tunanin chakwakiyar cikin littafin ya wuce nan, haka zalika labarin ya shallakewa tunaninku. Nagode sosai duk wacce tabiya 300 ina tabbatar muku da cewa zata samu cigaban labarin Laylerh Maleek. Gare ku mutanen dake zaune a Niger zaku iya tura katinku ga wannan number'n. +227 90899076)*

*CHAPTER 10*

Sako da ƙafarta cikin falon yayi dae dae da buɗe ƙofar part ɗinsa da akayi.
Ganin haka ne yasa tayi saurin komawa baya, cikin hanzari ta lafe ajikin ɗan bangon da tasan wanda ke cikin falon bazae ganta ba.

Cikin isa da kuma izza yake takunsa, sanye yake cikin full shigar uniform ɗinsa na soldiers, wanda sukayi matuƙar yi masa kyau, kana suka bayyana zallan kwarjini da cikar halittarsa, yanayin yanda kayan sukayi matuƙar yi masa kyau ne yasa Laylerh da ta ɗan ɗago kanta tana leƙensa ne ta kafeshi da idanunta, ganin shigar dake jikinsa ne yasata sakin baki da hanci tana kallonsa, tundaga kan ƙafarsa dake sanye cikin wasu haɗaɗɗun baƙaƙen takalma, sosai uniform ɗin suka zauna ajikinsa, yayinda ya ɗaura facing cap wanda yake shima na soldiers ɗinne akansa, sanadin hakanne kuwa yasa rumfar facing cap ɗin ya ɗan rufe idanunsa, ƙawataccen sajen dake kwance akan fuskarsa ne ke wani irin shining, gefe guda kuwa red shining lips ɗinsa ne keta walwalali, wanda hakan shike ƙara ƙawata kyawun fuskarsa, tabbas Maleek kyakkyawane, kuma tsayayyen Namiji me ɗauke da tarin kwarjini da kuma abubuwan burgewa.
Tabbas Batajin zata iya ɗauke kanta daga kallon kyakkyawan Namiji na musamman irinsa, wanda zata iya rantsuwa cewa babu wani namijin da uniform ɗin soldiers ya taɓa karɓansa kamar sa.
Ɗan lumshe idanunta tayi tare da lasan siraran laɓɓanta, duk da cewar basa kusa da juna amma gaba ɗaya ƙamshin daddaɗan turarensa ya cika falon, har takai ga ya ziyarci hancinta, numfashin dake ɗauke da daddaɗan ƙamshin turarensa ta shaƙa, tare da lumshe idanunta, acikin jiki da zuciyarta takejin wani abu nayi mata yawo, kamar yanda jini ke gudana ajikinta haka takejin wani abu na musamman adangane dashi, ganin ya nufi dining area ne yasa ta ɗauke idanunta akansa, har zuwa lokacin kuwa bata rufe bakinta dake a wangale ba, kwarjini da tsantsar haɗuwarsa ne suka mamaye zuciya da gangar jikinta, wanda hakan ya haifar mata da wani irin zazzafan shauƙi me ratsa gangar jiki.
Sake sakin ajiyar zuciya tayi akaro na barkatai, yayinda tayi imani cewa ganinsa da tayi ne sanadiyar rugurgujewan nutsuwarta.
Ɗan ƙara leƙa dinning area'n ɗin tayi, wanda tuni har ya ƙarasa ya zauna, yayinda ya bawa cikin falon baya, gefe guda kuwa su Abbu ne zaune,ciki kuwa harda Alhaji Ahmad Rufa'e wanda saboda wani babban dalili ya kashe zuwansa Kaduna da zaiyi yau ɗin.
Hannu tasa ta gyara hijab ɗin jikinta, tare da ƙoƙarin samawa kanta nutsuwa.
Cikin yanayin sanyi ta fito daga inda ta ɓoye, tare da ƙarasowa cikin falon, kaitsaye dinning area ɗin ta nufa.
Abbu na ganinta ya saki murmushi cikin kulawa yace.
"Good Morning Laylatu."
(Laylatu shine sunan da Abbu ke ƙiranta idan yana cikin yanayin nishaɗi.) Ɗan murmushin daya bayyana kyawawan haƙoranta tayi, cikin yanayin ta na sanyi tace.
"Am sorry Abbu Good Morning!."
Murmushi Abbu yayi tare da cewa. "Morning my daughter, ya jikin naki?."
"Da sauƙi sosai." Tafaɗa tana me gyara zaman school bag ɗin dake goye abayanta.
Kallonta ta mayar ga Alhaji Ahmad Rufa'e, cikin girmamawa tace.
"Abba Ina kwana."
Murmushi Alhaji Ahmad ɗin yayi, kasancewar tana kusa dashi yasashi ɗan dafa kanta, cike da kulawa yace.
"Lafiya ƙalau Laylerh, ya jikin naki?."
Murmushi tayi tare da cewa.
"Da sauƙi."
Kai Alhaji Ahmad ɗin ya jinjina tare da cewa.
"Allah Yaƙara sauƙi!."
Da "Ameen." Ta amsa tare da ɗago kanta, ɗan satan kallon inda Najeeb yake tayi, kasancewar kallonta yake yasa idanunsu faɗawa cikin na juna, da sauri tayi ƙasa da idanunta, hannayenta ta haɗe waje ɗaya tare da soma wasa da ƴan yatsunta, samun kanta tayi cikin wani irin yanayi, bakinta taɗan turo gaba ashagwaɓe tace. "Ina Kwana."
Bai amsa mata ba saima cigaba da kallonta da yayi, baƙaramin kyau ƙananan laɓɓanta sukayi masa ba, musamman ma da tana maganan, wani irin hot feeling ɗinta yaji na ratsa duk jikinsa, lumshe idanunsa yayi tare da ɗan lashe lips ɗinsa, shikaɗai yasan me yakeji agame da Laylerh'n, lallai Laylerh macece wanda da kalma ɗaya kawai zata iya haukata nutsuwa da hankalin lafiyayyen ɗa Namiji.
Jin bai amsata bane yasa taɗan murgaɗa baki, cikin ranta tace.
"Dan kasamu ma angaisheka, bazan sake gaisheka ba to."

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 26, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

LAYLERH MALEEK Where stories live. Discover now