Chapter 1

4.5K 320 31
                                    

  🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*Bismillahirrahamanirraheem*

             
             *LAYLERH MALEEK*

     *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Blood Brother, My Happiness, My Sweetheart, nd My Heartbeat (AUWAL) I love you so so much my big bro, wish you quick recovery darling👏🏻.*

               *FOLLOW ME ON*
                           *Wattpad*
                      @fatymasardauna
#Firstlove.

*Friday 31/October/2020*

      *(📿Happy Jumma'at Mubarak To All Muslims Ummah, May Allah Bless You And Your Family.🕋)*

                *CHAPTER ONE*

*(SOYAYYA wata irin ƙaddarace, da take ɗaure akan wuyan kowa, sannan kuma wata abace da ba'a iya ganin launinta da ido, hakanne ma yasa  ba'a iya sauyata, saidai idan taso takan tashi daga sunanta na SO ta koma ƘIYAYYA. Acikin  kowani rayuwar ɗan Adam akwai salon ƙaddarori masu tarin yawa, akowacce duniya akuma koda yaushe ƙaddara tana tafiya ne daidai da  rayuwa, haka kuma tana rayuwa da mu cikin  farinciki ko akasin haka, abu ɗayane yake tafiya acikin zuƙatanmu, shine MURADI, FATA, da kuma son samun ABUNDA ZUCIYA KESO. Sannan  kuma babu wani bawa wanda ke iya gujewa ƙaddaransa, Lallai ƙaddararmu tana gudana ajikinmu kamar jini, akowace rana abubuwa mabanbanta suna faruwa, to haka itama ƙaddara takan iya sauyawa ako da yaushe, wannan rayuwar daban take da saura, komai yana cikin zuciya da tunanin LAYLERH MALEEK.)*
  ***       ***       ***
Cikin sauri take ƙoƙarin sanya uniform ɗin makarantar ta, sosai take sauri dan  tasan idan ta tsaya wasa zatayi latti, wanda zuwa yanzu  batasan da wani baki zata fara faɗan  excuse ɗinta ba, ga masu gadin makarantar, domin tasan zuwa yanzu suma sungaji da karɓan excuse ɗinta.
Ɗan madaidaicin sket ɗin makarantar nata tasanya, wanda yake da ɗan tattara ajikinsa,  wanda idan kasanya sa, zaka jawosa har saman cikinka, dan iyan high waist ɗinnan ne, bayan ta saka sket ɗinne.
Cikin sauri sauri ta zura wata farar rigan long sleeve ajikinta, ahanzarce ta tura rigar acikin sket ɗin, take ta zuge zip ɗin sket ɗin,  hakan da tayi ne kuma yasa ba'a ganin ƙasan rigar makarantar nata.
Sauri sauri ta maƙala aninayen dake jere agaban rigar,  farin safa ta sanya aƙafafunta, tare da ɗaukan  wani toms ɗinta me kalan baƙi ta sanya.
Dayake sket ɗin makarantar tata da kaɗan ya wuce guiwanta, hakan yasa safan da tasa aƙafanta yaɗan taimaka wajen suturta fatar ƙafanta.

Kyawawan fararen idanunta  ta ɗago, tare da  sauƙesu  akan agogon bangon dake saƙale jikin bangon ɗakin.  
8:15 am daidai ta gani, jitayi ƙirjinta yayi wani irin bugu, take taji zuciyarta ta karye, shikenan yau ma ta sakeyin latti kamar sauran ranakun,  by 8:00 am daidai ake kulle gate ɗin makarantar tasu,  da zaran an kulle kuwa babu me shiga, idan kazo late saidai ka koma gida,  duk da tasan cewar tana samun alfarmar shiga makarantar daga wajen masu gadi koda an kulle, saidai yau bata tunanin cewa zasu dubeta ma bare har su karɓi roƙonta.

Cikin azama ta zura  ɗan madaidaicin hijabin makarantar ajikinta, wanda duka tsayinsa baiwuce guiwan hannunta ba,  kallon kanta tayi amadubi, tare da kafe madubin da ido, kyakkyawar fuskarta take kallo ta cikin madubin, sannu ahankali idanunta suka ciko da hawaye, lumshe idanun nata tayi, wanda hakan ya bawa hawayen dake ciki daman gangarowa.
Da sauri ta share hawayen, ta  ɗauki ƙatuwar hand bag dinta ta goya. 
Text book ɗin ta da tayi assigment acikinsa jiya, wanda ta ɗaurasa bisa kan mirror ta ɗauka,  da sauri tafice daga cikin ɗakin.

Koda ta bude ƙofar ɗakin nata ta fito, nan cikin babban falon gidan, da kai tsaye za'a ƙirasa da aljannar duniya ta samu kanta, falo ne tankameme wanda tsarinsa da haɗuwarsa ya zarce misali, kallo ɗaya zakayiwa falon ka tabbatar da cewar mamallakansa ba ƙananan masu arziki bane,  saboda wasu irin haɗaɗɗun royal cushions masu uban kyau da tsada da aka ƙawata cikin falon dasu, adon jikin royal cushions ɗin ma kaɗai abun kallo ne,    tsakiyan falon kuwa wani irin haɗaɗɗen lallausan turkish carpet ne a malale, wanda kana takawa ƴan yatsun ƙafanka na lumewa aciki, tsabar laushi, ta cikin falon acan gefe kuwa wani irin ƙawataccen dinning area ne me azabar kyau da tsaruwa, an kewaye gaba ɗaya wajen da haɗaɗɗen decoration me kyau, wasu irin haɗaɗɗun labule kewaye da kowani ƙofa da window dake cikin falon, ga kuma wasu irin flowers masu kyau da aka saka akowani kusurwan falon, wanda sai shinning suke suna ɗaukar ido, still daga
cikin falon kuwa wani irin tangamemen tv plasma ne keta aikin ɓaɓatu shi kaɗai,  bayan plasman dake magana shi kaɗai babu wani halitta acikin falon, sai  sanyin A/C dake ta busawa.
Kan dinning area' n ta kalla, wayam haka taga saman table ɗin  babu ko cokali, bare kuma  food flask, da dukkan alama dai yau ɗinma ba'a rage mata break fast agidan ba.

LAYLERH MALEEK Where stories live. Discover now