Chapter 9

1.5K 131 27
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     *LAYLERH MALEEK*

  *Writting By*
Phatymasardauna

                    *Wattpad*
             @fatymasardauna

#future

                  *Chapter 9*

Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da fesar da sassanyar iska ta bakinsa, jin yanda sanyin ruwan shower ɗin ke ratsa duk jikinsa ne ya sashi kashe shower'n,  tare da jawo wani fari ƙal ɗin towel  ya ɗaura akan waist ɗinsa, ƙarasawa gaban sink ɗin dake cikin toilet ɗin yayi  tare da ɗauro alwala,  hannunsa ya ɗaura akansa, cikin nutsuwa ya soma ɗan kaɗe gashinsa dake ajiƙe da ruwa,   hannunsa yakai jikin wani hangers  wanda anan jikin hangers ɗin yake rataye duk towels ɗinsa,  ɗaya daga cikin towels ɗin ya ciro  tare da soma goge jiƙaƙƙen gashin kansa,  koda ya gama goge kannasa kuwa, nan cikin wani durstbin ya jefa towel ɗin, sannan kaitsaye ya fice daga cikin bathroom ɗin.
Koda ya fito kuwa nan kan wata chair dake aje agaban mirror ɗinsa  ya zauna, yayinda  gaba ɗaya jikinsa ke ɗauke da danshin ruwa, yayinda gargasan jikinsa suka kwanta lub, daga gefe guda kuwa farar fatarsa har wani shining take, wani ɗan ƙaramin towel  dake aje akan dressing mirror ɗin nasa ya ɗauka, wanda dashi yayi amfani wajen goge naked skin ɗinsa, wani lallausan body lotion  ya shafa, haɗe kuma da shafa  wani body spray me daɗin ƙamshi ajikinsa, wanda gaba ɗaya ƙamshin spray ɗin ya cika ɗakin.        
Cikin nutsuwa ya miƙe tsaye tare da  ƙarasawa gaban sif glass ɗinsa, wanda ke cike da kayan sawansa,  wani simple 3 quater jeans ya ciro tare da  sawa ajikinsa.
Haka Batare daya saka riga ba ya ƙarasa gaban bedside drawer ɗinsa,  ɗan jan murfin drawer'n yayi  tare da  ciro wani ɗan ƙaramin box me kaman akwati.         
Ƙarasawa gaban wata lallausar kujeran dake gefen gadon yayi ya zauna.
Ahankali ya kai hannunsa kan cikinsa daidai inda ya ɗaure da bandage, cikin nutsuwa  ya soma warware bandage ɗin dake nannaɗe akan ciwon dake gefen cikin sa,  ahankali yake ɗan cije jajayen laɓɓansa, tare da ɗan rumtse idanunsa, wanda da dukkan alama ciwon dake wajen na ɗan yi masa zafi.         
Koda ya gama cire bandage ɗin  maida kansa yayi ya ajiye, tare da jingina bayansa da jikin kujera, ahankali yake ɗan sakin numfashi.

Still lumshe idanunsa yayi yana mejin yanda ciwon nasa keyi masa zafi, duk da cewa kuwa yanzu kusan 3 weeks kenan dajin ciwon nasa, kasancewar sunje wani aiki ne cikin rashin sa'a  bullet ya samesa agefen cikinsa.               

Akasalance ya buɗe ɗan ƙaramin farin box ɗin da ya ajiye agabansa, inda ya ɗauko wani sabon bandage da kuma wani magani.
Sanin zafin maganin ya sashi  rumtse idanunsa, ahankali yaɗan soma shafa maganin wani irin zafi da raɗaɗi  ne suka shiga ratsa ƙwaƙwalwarsa,  cije lips ɗinsa yayi, cikin ƙarfin hali haka ya naɗa sabon bandage akan ciwon, duk da kuwa cewar yanajin zugi da zafi ajikinsa amma dole haka ya daure.
Bayan ya gama kintsa kansa ne ya tashi tsaye, inda kaitsaye ya nufi saman makeken gadonsa,  light off ɗin wutan ɗakin yayi,  sannan ahankali ya haye saman gadon, ɗan lumshe idanunsa yayi akaro na barkatai, tare da sakin bayyananniyar ajiyar zuciya, har yanzu yanajin ransa ba daɗi, ga kuma zuciyarsa da ke acunkushe, sam kuma baisan meyasa yakejin hakan ba.            
Tuno da mood ɗinta na ɗazu,  da kuma  sautin kukanta da yayi ne ya sashi sake maida idanunsa ya rufe, hannunsa ya ɗaura adaidai saitin zuciyarsa yana me sauraran, yanda  zuciyar tasa ke bugawa,  wani abu da ya tuna ne ya sanyashi ɗan cije lips ɗinsa, tare da  sakin murmushi har saida laɓɓan bakinsa suka ɗan motsa,  wayarsa dake yashe akan gadon ya ɗauka tare da kunnata, hoton wata kyakykyawar yarinya ne ya bayyana akan screen ɗin wayar, wanda duka dukanta bazata wuce 9 years ba, yayinda yarinyar ke sanye  da riga da wando, fuskarta ɗauke yake da murmushi, wanda hakan ya ƙara ƙawata kyawun fuskarta.     Idanunsa ya zubawa hoton dake mamaye akan screen ɗin wayar,  ahankali yakejin wani irin shauƙi na ratsa duk illahirin jikinsa,  matso da fuskar wayar tasa yayi, ahankali yaɗaura bakinsa akan screen ɗin wayar.  Cikin wata irin sassanyar murya me ɗauke da daddaɗan amo yace.  
"My Baby Boo!!." 
manna wayar tasa yayi akan faffaɗan ƙirjinsa, tare da lumshe kyawawan idanunsa, yayi imani cewa wannan yarinyar itace bugun zuciyarsa, haka kuma  ƙaddaransa natafiya ne dai dai da rayuwarta.
                  
Najeeb.. 
                      
Da tunani kala kala acikin ransa, ya ƙaraso gaban babban pharmacy ɗin, cikin ɗan hanzari ya shiga ciki,  magungunan da Dr. Ishaq ya rubuta wa Laylerh'n ya sayo, koda ya fito daga pharmacy'n  kaitsaye wani supermarket ya wuce, kayan ciye ciye ya sayawa Laylerh'n dangin su choculate da dai sauransu.
Daga supermarket din kuwa gida ya nufa.           
Koda ya shigo compound ɗin gidan, yana gama daidaita parking ɗin motarsa ya fito tare da nufar hanyar da zata sadashi da  falon gidan kaitsaye.
Yana ƙarasawa falon kuwa  ya tarar da su Abbu Jaheed da kuma mahaifinsa suna hira.     
Ganin Najeeb ɗinne yasa Abbu sakin murmushi cikin kulawa yace.   "Najeeb kadawo."           
Kai Najeeb  din ya jinjina tare da  ƙarasowa cikin falon.   
Wrist watch ɗin dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya kalla, cikin yanayin nuna damuwarsa ga Laylerh'n yace.  
"Eh nadawo Abbu, ga magungunan, dan ya kamata ace tatashi tasha, saboda shima zai taimaka mata ƙwarai wajen rage  raɗaɗin ciwon."      

LAYLERH MALEEK Where stories live. Discover now