Chapter 5

1.6K 163 26
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
         
     *LAYLERH MALEEK*

    *Writting by*
Phatymasardauna

                   *Wattpad*
            @fatymasardauna

#Arrogant

                *Chapter 5*

Hannunsa ya kai daidai saitin fuskarta, kallon ƙwayar shinkafan dake manne agefen bakinta yayi, haka  yayi kaman zai cire mata  sai kuma ya fasa, tare da saurin ɗauke kansa daga gareta, lokaci ɗaya ya haɗe fuska kaman bai taɓa dariya ba arayuwarsa.
Tuno wani abu da yayi ne, ya sashi rumtse idanunsa tare da ɗan cizan jajayen lips ɗinsa,  ahankali ya soma girgiza kansa,  haka yakejin zuciyarsa ba daɗi,  wani irin abune yaji yana yi masa yawo acikin jikinsa.
Laylerh kuwa har zuwa yanzu bata buɗe idanunta ba, bugun zuciyarta ne ke ƙara tsananta, yayinda ƙirjinta ke   harbawa da sauri.     
Ahankali taɗan buɗe idanunta wanda  cikinsu ya cika da ruwan hawaye, ɓoyayyar ajiyar zuciya ta saki, tare da ƙoƙarin shanye ruwan hawayen nata, dan batajin zata iya barinsu  sukai ga sauƙa akan fuskarta,  ɗan satan kallonsu tayi,  ganin cewa dukkaninsu hankalinsu ba'a wajenta yake ba ne  yasa ta ɗan matsar da kujeranta gefe, wanda hakan yasa ta ɗanyi nesa dashi,  spoon ɗin dake hannunta  tasa tare da ɗiban abincin ta kai bakinta, ahankali take  tauna abincin, dan hakanan taji duk batajin yunwa,  gefe guda kuwa  zuciyarta ne  ke saƙa mata abubuwa da yawa, azahirance  kuwa so take ta ɗan saci kallon gefen da yake, amma kuma kwata kwata tsoro da fargaban da takeji sun hanata.                      

Ajiye spoon ɗin dake hannunsa yayi,  tare da miƙewa tsaye, baice da kowannensu ƙala ba, ya juya kai tsaye ya nufi bedroom ɗinsa.

Da kallo  Abbu ya bisa  tare da girgiza kai, yasani dama har abada Maleek bazai taɓa sanjawa ba,  tuntuni ya riga daya bari miskilanci da zurfin ciki sun zame masa ɗabi'a,  gashi yanayin aikinsa ya ƙara sanja masa halayya, bazai taɓa faɗin damuwarsa ba komin girmanta, haka zalika koda yaushe fuskarsa babu wadataccen murmushi, then bakomai ke sashi dariya ba, koda kuwa abun yakai na dariya saidai kawai yayi murmushi.
 Ajiyar zuciya Abbu ya sauƙe tare da ci gaba dacin abincinsa, dan baisan sai yaushe ne Maleek ɗin zai sanja ba.

Tashin da yayi ne yasa Laylerh sakin ɓoyayyar ajiyar zuciya, tabbas yana da kwarjini mai tarin yawa, wanda shi yake sawa duk takejin kanta wata iri, bata da wani ƙwarin guiwa agabansa, ɗan lumshe idanunta tayi tare da haɗiye abincin dake maƙale amaƙoshinta, tashinsa shi ya sa taɗan saki jikinta, da kaɗan kaɗan ta dinga tsakuran abinci tana kaiwa bakinta.

Abbu wanda ya kammala cin abincin sa ne ya ɗaura idanunsa akan wayan Maleek, wanda ke aje nan kan saman table ɗin,  sauƙe  idanunsa akan wayan kuwa, yayi  daidai da soma ƙiran wayar da akayi, kallon Laylerh da ke goge bakinta  da tissue Abbu yayi, cikin kulawa yace.   
"Laylerh ɗauki wayarsa ki bisa da shi."
Jin maganan da Abbun ya faɗa ne, yasa lokaci ɗaya ta fara tari  batare da ta shiryawa hakan ba,  da sauri ta ɗauki ruwa tasha, tare da soma mutsustsuka idanunta, kallon da Abbu yayi mata ne yasa asanyaye ta ɗauki wayar tasa dake ta faman ringing.
Miƙewa tsaye tayi tare da barin dining area'n, koda ta ƙarasa cikin falon kaitsaye ta doshi ƙofar da zata sada ta da sashin sa.  
Hakanan takejin ƙirjinta na bugawa da ƙarfi, gaba ɗaya jikinta rawa yake, ahanakali ta ɗaura hannunta akan handle ɗin ƙofar, tare da murɗawa ta tura ƙofar ciki,  asanyaye taɗan kutsa kai cikin falon,   takun farko ta jefa ƙafanta akan wani lallausan carpet me taushin gaske,  ga kuma wani irin daddaɗan sanyi me tafiya da ƙamshi daya daki kan fuskarta,  ɗan lumshe idanunta tayi, tare da  maida ƙofar  ta rufe, idanunta ta baza wajen ƙarewa falon nasa kallo,  komai na cikin falon atsare yake, da dukkan alama  mamallakin falon bayason yawan tarkace, domin daga yanayin tsarin falon nasa zaka fahimci haka,  inda aka zuba wasu haɗaɗɗun cushions masu kyaun gaske atsakiyar falon, sai kuma royal blue nd milk curtains da aka saka ajikin kowacce ƙofa da window dake cikin falon, kasancewar kujerun falon nada kalan royal blue shiyasa curtains ɗinma suka kasance royal blue nd milk,  gefe guda kuwa wani jibgegen tv plasma ne, wanda aka ɗaurasa akan wani glass table me kyaun gaske,  gefe da gefensa kuma wasu fararen flowers ne masu kyau,  kallon haɗaɗɗen turkish carfet ɗin dake malale atsakiyan falon tayi, wanda shima kalan royal blue da milk ne, tsarin falon yayi kyau sosai,  ahankali ta shiga takawa har ta ƙaraso tsakiyan falon, ganin bakowa afalon ne yasa ta ɗan ciji lips ɗinta, idanunta ta sauƙe akan wata haɗaɗɗiyar ƙofa dake cikin falon, wanda da dukkan alama kuma ƙofar bedroom ne.
Kallon wayartasa dake riƙe ahanunta tana ta faman ringing tayi.
Rasa yanda zatayi yasa ahankali ta ƙarasa jikin ƙofar zuciyarta cike da tsoro, ɗan murɗa handle ɗin ƙofar tayi, take kuwa ƙofar ta buɗe, kasancewar dama ba arufeta da kyau ba.
Ganin ƙofar ta buɗe ne yasa ta ɗan zaro danunta waje, sam batayi tunanin ƙofar abuɗe take ba shiyasa ta tura, atsorace batare da ta ƙarasa shiga cikin ɗakin ba, da ƴar siririyar muryarta tayi sallama.
Saidai shiru haka taji, ba ko motsin mutum bare tasa ran za'a amsa mata, sake kwaɗa wani sallaman tayi, still babu amsa.
Jin shiru ne yasa tayi tunanin cewa ko baya cikin ɗakin, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da ƙarasa shigowa cikin ɗakin.
Wani daddaɗan ƙamshin da ya daki hancinta ne, yasa ta kuma  lumshe idanunta tare da jan wani dogon numfashi, tashin farko kenan da taji tana masifar son ƙamshin, dan ko tantama baza tayi ba, wannan ƙamshin shine ƙamshin da taji yana fita ajikinsa.
Ɗan buɗe idanunta tayi ahankali,  inda ta sauƙe su akansa.
Zaune yake agaban dressing mirror yayinda ya bawa ƙofar shigowa  ɗakin baya, sanye yake da white trouser yayinda ya cire rigar jikinsa ya ajiyeta agefe, yanayin yanda ya juya baya ne yasa gaba ɗaya surar bayansa ta bayyana,  wasu ƙananan hairs ne kwance lub akan white skin ɗinsa, yayinda fatar tasa ke wani irin shining, yanayin yanda ya juya baya ya kuma duƙar da kansa ƙasa shiya sanya ba'a iya ganin me yakeyi, kuma shima ba lallai yasan anshigo ɗakin ba.
Idanunta masu kyau ta zubawa fatar bayansa bata ko ƙiftawa, bakomai ya ɗau hankalinta ba kuwa face wani ɗan zanen tattoo wanda akayisa kaman rubutu dake manne a tsakiyan bayansa.
Ahankali taɗan lumshe idanunta, tare da budesu alokaci guda, gaba ɗaya ta shagala da kallon zanen dake kwance abayansa, hakanan taji shauƙin taɓa zanen na fusgarta, cikin nutsuwa ta soma takawa zuwa inda yake, wanda har zuwa yanzu bai ɗago kansa ba, baikuma yi wani ƙwaƙƙwaran motsi ba, da'alama dai baisan da shigowanta cikin ɗakin nasa ba.

LAYLERH MALEEK Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ