Chapter 6

1.5K 274 38
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

    *LAYLERH MALEEK*

    *Writting By*
Phatymasardauna

                *Wattpad*
        @fatymasardauna

#fanfiction

                   *Chapter 6*

Ahankali ya zuro da ƙafafunsa ƙasa daga kan gadon, ɗan cije red lips ɗinsa yayi, saboda yanda yakeji ajikinsa duk ba daɗi, bayajin idan baisha magani ba zai ji relief daga abun da yakeji, musamman ma ayanzu da yake jin mararsa nayi masa ciwo.
Miƙewa tsaye yayi,  cikin nutsuwa ya ƙarasa gaban wata ƴar ƙaramar drawer dake cikin ɗakin, murfin drawer'n ya buɗe tare da  ciro wasu  tablets, hannunsa na rawa ya ɓalli maganin  tare da watsa su abakinsa,  ahankali ya ƙarasa gaban fridge ɗin dake cikin ɗakin, tare da  buɗewa ya ɗauko bootle water marar sanyi,  ɓalle murfin gorar yayi tare da kafa bakin goran akan soft lips ɗinsa,  sai alokacin ya haɗiye maganin dake bakinsa, asanyaye ya lumshe idanunsa tare da sakin ajiyar zuciya, shi kansa baisan wani irin mutum bane shi, always yana cikin feeling, abun tun baya damunsa har zuwa yanzu ya fara damunsa.
Komawa saman bed  yayi ya kwanta, ahankali yake ta faman sauƙe ajiyar zuciya, sannu ahankali yakejin feeling ɗin na sauƙa, yayinda gaba ɗaya jikinsa ke samun relief,  shiru yayi tare da ƙurawa zanen dake saman ɗakin nasa ido, abubuwa da yawa yake saƙawa acikin zuciyarsa, ahaka  in 15 minute bacci ya ɗaukesa. 

Ɓangaren Laylerh kuwa dama tajima dayin bacci, saidai acikin baccin nata ne ta dinga mafarkai iri iri, kamar yanda ta saba akowani dare saitayi mafarkin wani na musamman, wani wanda take ganin babu irinsa,  wanda kuma bai taɓa bata dama taga  cikakkiyar fuskarsa ba,, saidai ako da yaushe tana cikin aminta cewar  kyawawan idanun da keyi mata gizo mallakinsa ne, wani abun mamakin kuwa shine amafarkin nata na yau ba iya Mr.Beautyful eyes ɗin nata bane yazo kamar yanda ta saka masa suna,  abayansa wani take gani wanda shima bai bata daman ganin full face dinsa ba, wani ne ya kutso cikin mafarkin nata wanda yake neman shiga wani babi na rayuwarta,  zuwan sa ne kuma yasa mr.beautyful eyes ɗinta ke neman rufe mata kyawawan idanunsa.
Aɗan razane ta farka daga nannauyan baccin daya ɗauketa, hakanan taji zuciyarta na bugawa, mafarkin nata ne yashiga dawowa cikin kanta filla filla, wani irin yanayi da tasamu kanta aciki me wuyar fassaruwa ne, yasa ta tashi ta nufi toilet alwala ta ɗauro sannan ta dawo ta sakeyin addu'a ta kwanta.
Wani irin sabon fargaba ne ke neman lulluɓe zuciyarta, hakanan taji tasamu kanta cikin wani ƙaton rauni, pillow'n dake hannunta ta rungume, so take tayi kuka amma kukan yaƙi zuwa, yanda zuciyarta ke bugawa yasa sunan Ya M.Jay ke yawo acikin ƙwaƙwalwarta.
Ahaka dai saida ta ɗauki sama da 20 minute kafun bacci ɓarawo ya kuma ɗaukarta.

Washegari.            

6am daidai ta tashi daga bacci, tana buɗe idanunta kuwa mafarkin ta na jiya ya shiga dawowa kanta,  kanta taɗan soma girgizawa tare da rumtse idanunta, sam batason sake tuna mafarkin, saboda tunasa yanasawa taji zuciyarta ta zama very weak sannan tanaji ajikinta cewa tanason yin kuka.
Cikin sauri tatashi daga kan gadon, agurguje tawuce toilet alwala tayi sannan tazo ta gabatar da sallan asuba.
Koda ta idar da sallan zama tayi tare da ɗaukan Alƙur'ani ta soma karantawa, sanin da tayi cewa idan Abbu Jaheed na gida tana da driver me kaita makaranta.
Suratul Anbiya ta karanta sannan ta rufe Alƙur'anin.
Miƙewa tsaye tayi, cikin nutsuwa tasoma gyara ɗakinta, tana kammalawa kuwa ta  shige toilet, wanka tayi sannan ta fito ɗaure  da towel ajikinta.
Ƙarasawa gaban ɗan madaidaicin drawer'nta tayi, ƴar ƙaramar jakar da Hajiya Asma'u ta bata ta ɗauko, tare da ciro wani body lotion, wanda yake ɗaya daga cikin kayayyakin da Hajia Asma'un ta bata,  anan kan gado ta zauna cikin nutsuwa ta soma shafa lotion cream ɗin ajikinta, tana kammalawa kuwa ta ƙarasa gaban mirror, normal powder ta murza akan fuskar ta, sannan taɗan shafawa jajayen lips ɗinta white lip gloss,  daga haka kuwa ko kwalli batasa acikin idanunta ba ballantana kuma mascara, hakanan ta saba bata da yawan kwalliya, koda yaushe haka take zama fuskarta ba kwalliya, wasu lokutan kuwa haka take zuwa skull ɗin ma ko powder bata shafawa akan fuskar ta.
Anutse ta sanya kayan uniform ɗin ta, yayinda ta haɗa dogon gashinta daya cunkushe waje ɗaya,  saboda rashin saloon ta ɗaure.
Ɗan ƙaramin hijab ɗin skull ɗin nata tasa, tare da ɗaukan  jibgegiyar school bag ɗinta ta goya, kallon agogo tayi  7 am daidai, wanda hakan ke nuna mata cewa kenan tana da sauran 30 minute daya rage mata, ƙarasawa jikin ƙofar ɗakin tayi tare da murɗa handle ɗin  ƙofar ta fice.     

LAYLERH MALEEK Où les histoires vivent. Découvrez maintenant