A qasan kujeran da take zaune Leesa ta zauna, ta gaidata cikin ladabi Dan tana matuqar ganin girman shugaba saboda irin halaccin da tayi musu,

"Na dauka tunda Kun tafi ba Zaku taba dawowa ba, kunyi was da hankali na ke da 'yar uwarki Saleeha Amman Babu damuwa duniya ce daga yanzu Babu yaran da Zan sake taimakawa na rufe qofar taimako a kanku"

"Haleesa ce ba Saleeha ba shugaba, kiyi haquri Dan Allah nasan bamuyi Miki adalci ba bamuyi ma kanmu adalci ba Amman kaddara ta Riga fata ne Babu Yanda muka iya, yanzu Haka Mun samu dangin mu saboda sarqan mu da muka Miki alqawarin zamu baki Mun gano iyayen mu dashi"

Ta Ciro IV daga jakarta ta ajiye Mata a gaban ta,
"Kina cikin mutane masu matuqar muhimmanci a rayuwar mu Wanda ba zamu manta dasu ba, kina da Hali da Kuma damar da Zaki nemi kudi damu ki saka mu karuwanci ki samu riba Mai tsananin yawa Amman bakiyi hakan ba, kin tsaya tsayin daka wurin ganin kin Kare Mana mutuncin mu Mun samu ingantaccen rayuwa, haqiqa ke kamar uwa ce a garemu Shugaba Kuma har cikin zuciyar mu muke qaunar ki, wannan Kuma katin aure na ne na kawo Miki gayyata ne ba a matsayin baquwar mu ba saidai a matsayin uwa Wanda zata je Taya 'ya'yan ta farinciki, alqawarin da muka dauka Miki Kuma yanzu 'dan uwan mu zai cika Miki shi a waje sai kizo muje"

Abunku da Mara addini wani guda shugaba ta rangada Wanda qarar shi har tsakar gida ta tafa hannuwa "a hayye nanaye, yau BARIKI tayi riba ai banci ta zama ba Ashe harqan arziqi ne ta kawo ki, to muje" ta fada tana Kama hanyar waje,

Girgiza Kai Leesa tayi tana Murmushi, son kudin shugaba har yanzu Yana Nan tace "kidan rufa jikin ki shugaba babban mutum be sosai"

Babu musu ta dauko wani ficilin gyale ta yafa suka fita, shugaba da kanta ta shimfida ma Sa'ood tabarma ya zauna ita Kuma Leesa ta dauko mata kujera 'yar tsunguno,

Kallo Daya Sa'ood yayi Mata ya dauke Kai Yana Jin kaman yayi amai ga turaren ta Mai warin daga hankali kaman na Koran aljanu, ba don darajan Sarwa ba wallahi ko hanya bazai yarda ya hada su da wannan matar ba, basu tsaya wani dogon gaisuwa ba ya jawo wata qatuwar jaka da ya dauko a mota Bayan Leesa ta Shiga ciki, ya bude ya fara Ciro bundle din 'yan dubu_dubu Yana ajiyewa,

Saida ya ajiye guda ashirin sannan ya Ciro wasu ashirin din ya ajiye a Daya gefen
"Ga alqawarin ki Nan, Daya kudin sarqan Haleesa dayan Kuma na sarqan Saleeha"

Baki bude shugaba take bin kudin da kallo Wai yau ita aka bawa miliyan 4 a bulus ba tare da tayi komai ba, Bata Gama mamaki ba Sa'ood ya Ciro cheque ya rubuta Mata 20 million ya Bata,

"Wannan Kuma rabi ladan kula da Haleesa ne rabi ladan kula da Saleeha, Mun gode qwarai da Kika riqe amanar da Allah ya Baki Allah ya saka Miki da mafificin alkhairi, sannan Abu na qarshe Kuma inaso a kashe gidan Nan, inaso abar duk wani aikin ashsha da akeyi a cikin ta a rufe ta gaba Daya, idan hakan ta faru no Kuma nayi alqawarin Zan taimaka ma kowa a cikin ku da wurin zama da jari ko aikin you Mai kyau Wanda zai dauki nauyin ku harda iyalanku idan akwai maishi sai kuyi tunani akai idan Kun yanke shawara ku fada ma Haleesa ta sanar dani,"

Shugaba dai ta qane ta kasa magana ta dubi maqudan kudin da aka ajiye Mata tabi ta dubi cheque din hannun ta, Bata taba tunanin zata samu kudi irin haka ba Ashe gwara da ta yarda ta karbe su a hannun saurayin ta alhajin da aka saka Masa su cikin mota shi yayi tunanin ma wata budurwar shi ce ta aifa Masa su shiyasa tunda ya miqa Mata su day yarjejeniyar zai bada kudin kula dasu da abincin su day komai da komai ya gudu Bata sake ganin shi ba har yau,

Kafin ta dawo hayyacinta ta nemi Sa'ood ta rasa har ya tashi daga wurin, wani ihu ta saka ta tattari kudin harda tabarman ta shige ciki dashi tana shewa kaman zata tashi gidan Babu abinda take maimaitawa sai "harqa ta mutu, daga yau harqa ya watse"

Haleesa dariya kawai tayi dajin haka tasan kudi ne kawai yayi aiki a Kan shugaba badon haka ba gwanda ta rasa rayuwar ta Akan ta rasa muqamin ta, sauran kudin taje ta raba masu Helen da sauran kilakan gidan sannan ta Basu IV sukayi musayar number tayi sallan azahar tukunna ta zauna jiran dawowar Sa'ood daga masallaci,

Duk Yanda sukayi da ita taci abinci firr taqi saboda Saida sukayi yarjejeniya da Sa'ood Akan ba zata Sha Koda ruwa ba a gidan karuwai idan ba haka ba a bakacin karatun ta, Yana dawowa ya Kira ta a way tayi musu sallama suka tafi sannan suka biya Yahuza suya spot ya siya Mata drinks da nama da Dan snack suka dauki hanyar komawa Kano,

Daff la'asar suka Isa unguwar su Ameerah, Sa'ood yasa akayi Masa sallama da babanta Dan bayi son barinta ta fara Shiga suyi Mata irin wulaqancin da ya samu sunayi Mata ranan,

Kwarjinin da Sa'ood yayi mishi da Kuma yanayin shi kana ganin shi kasan akwai dala, yasa har qasa baban Ameerah ya tsunguna Yana mishi gaisuwar ban girma Yana qi suyi musabaha, baisan shi ba domin ranar da yazo ya dauki Haleesa dare be Kuma Bai want tsaya qare Masa kallo ba Saida yace Haleesa ta fito daga mota sannan tsananin kunya ya Kama shi dan bai manta ta ba,

Gaida shi tayi cikin mutuntawa da sauri tayi ciki tana qwala ma mamanmu Ameerah Kira, Jin kaman muryan Haleesa yasa Ameerah da qannen ta sukayi saurin fitowa itama dazu da safe tazo wunin gida don auren ta yanzu wata biyu Kenan,

Da gudu Ameerah tazo ta rungume Haleesa daga ta sama tana Nishi, "yarinyar Nan ba kyau ba harda nayi kinyi, Ina Kika Shiga be Haleesa? Ina dai kina lafiya? Baki zo biki na ba nayi missing dinki sosai"

Miqa Mata IV tayi tace "Allah baiyi zanzo nakin bane Amman ga nawa Ina fatan Zaki zo"

" Ba zata je ba tunda qawarki kawai Kika sani kin manta da maman ki" taji muryan maman Ameerah ta Bayan ta Wanda fitowar ta Kenan daga bandaki,

Juyawa tayi ta rungume mama "sorry mama ta daga shigowa na ke na Nima, mama yanzu nasan gidan mu na samu iyaye na Kuma Suma sunce suna son ganin ku yanzu ma tare da Yaya na nake"

"Alhamdulillah, alhamdulillah Daman komai yayi farko zaiyi qarshe Haleesa.............🧚

*Page din yau anyi rungume_rungume da yawa shiyasa duk jikina ya Kama ciwo*😃
*Ayi min afuwa da qarancin pages din kwana biyun nan please*

*Ummu Najma ce 😘*

KAMA DA WANE....(Completed)Место, где живут истории. Откройте их для себя