yaa fahd nake so (2)

336 34 2
                                    

"ayau dan uwanka ze dawo ganin gida daka abroad. banaso asamu matsala" ta gama maganar tana gyara zaman ta.

muryar wata mata ce ta katse musu zancen su dan tindaga corridor take ta guda.

"mama!!!" sha'hida ta fada tana mikewa. saurin kaucewa fahd yayi kar ita maman tayi gaba dashi.

murmushi ne ya bayyana a kan fuskar aunty zainobu itama ta mike. "ina mijin nawa!?" cewar mama tana sa kafar ta a parlourn

"ae kin yi wuri. ya hanya?" aunty zainobu ta fada tana wata yar dariya.

seda suka gama gaisawa kowa ya nitsu sannan fahd ya gaida ita.

kamar an tsikari sha'hida tace "mama! kin ga yaya na. shi ne wannan dinnan dana ke fada maki wannan me kama da wani dan film??"

"Au!! kai sannun ka" mama tace ta yunkurin tashi "dago naga fuskar taka sosai.

ajiyar zuciya fahd yayi ya dago kansa. "Wallahi kuwa yar nan da gaske kike. ikon Allah!" ta juya ta kalli Aunty zainobu "ae wannan yafi mijina kyau anya ba zan chanza ba"

duk da aunty zainobu tasan wasa ne amma seda ranta ya sosu jin za'a taba dan nata tilo. wani munafukin murmushi tayi me dan sauti ama bata ce komi ba.

"mama nifa y
ake so" sha'hida ta turo baki "au kin fasa yaya hameed enki?"

gyada kai ta danyi "ni bana fa sonshi dama wasa nake masa ni ya fahd nake so yafi kyau kuma ma ae shi baya chatting iya hadda yake kullum"

"kinji yarinya. kuzo muje karamin dining kici wani abun" aunty zainobu tayi saurin katse sha'hida "fahd dama shike nan"

bece komai ba ya tashi ya ficewar sa. Yanzu ya gane asalin sururtun sha'hida ashe gadar sa tayi.

***
Naji korafin readers ena kuma ina me baku hakuri.

abinda yasa kuka ga ina maku chapters a rarrabe sabida idan ta fiya yawa ba lalle tayi kyau ba ko kuma ma'ana ba.

nagode

pp-panda

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now