yaa fahd nake so (1)

301 30 0
                                    

gyada kai yayi yace "yayi kyau".

"kuma Aunty tana kiranka. wae tace kuma muje tare" ta karashe maganar tana jan hannun rigar shi.

***

A chan side en ita Aunty zainobu. yan aiki ne masu dubun yawa suke ta kaikawo cikin gaggawa ana karasa shirya wurin cin abinci.

koda fahd ya tura kofar shiga bangaren seda yayi kicibus da wata me aiki.

"Dan allah yi hakuri! wallahi ban gankaba. ina kwana" ta fada cikin sauri.

sha'hida ce tayi charaf tace "toh ke makauniya ce? zaki ga me Aunty zata miki tinda kika taba yaya na"

aikin ta biye wa sha'hida tasa kuka hawaye daba daba akan fuskarta tana cewa "dan Allah kimin rai"

"yaya zo muje" sha'hida ta fada tana murguda mata baki. ta gefe fahd ya raba ya wuce suga shiga cikin ginin.

yanzu dai fahd yafi shekara daya da rabi yana zuwa gidan kowane hutun makaranta da weekend ama befe so biyu ya shiga side en Aunty zainobu ba.

karo na farko shi ne ranar da yafara zuwa. na biyu kuma da tayi zazzabi ya je ya dubata dan ko gaida ita zeyi bari yake ta fito lambunta shan iska.

wannan karon shi na uku zuwa ama shi se daya gane gyaran da akayi.

Anty zainobu tana zaune a wani kawataccen sitting room me colour en jar kasa da golden da fari. charbin ta na hannu take dannawa lokaci zuwa lokaci.

Salama yayi ya ritsina daga bakin kofar yayin da ita sha'hida ta nufi wurin Auntyn tata.

"yauwa lafiya kalau" aunty zainobu ta amsa a dan kasalance "dama wata magana nake so en gaya maka"

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now