biyaiya ko bauta (1)

524 43 4
                                    

harabar wani gida motar tayi parking suka shiga. duk da gidan ba kato bane ba kallo daya zakayi masa ka gane masu kudi ne a gidan sabida irin adon da tsarin ginnin.

masu aiki ne irin yaran nan maza suka zo sanye a cikin uniform farar riga da dark blue wando suka bude masu kofar motar.

hajiya sa'adatu ce ta fara sauka rike da hannun fahd sa'annan umni itama ta sauka. cikin gidan suka karasa ita hajiya sa'adatu na ta kokarin jan fahd da hira.

ita dai umni a baya kawai take binsu bata cewa kala. a babban parlour na gidan Alhaji suleman da aka fi sani da Alhaji bature yake a zaune ya harde kafa idonsa na manne a can Tv dake makale a bango.

ko da sa'adatu tayi salama be waigo ba seda yaji muryar umni a dago da kanshi.

"a...nafisatu..." ya fada yana mata alama da ta zauna. gaida shi tayi sa'annan ta zauna. "Ga jikan ka fa" hajiya sa'adatu ta fada. zare hannun sa fahd yayi daga na hajiya sa'adatu dan sam bata kwanta a ranshi ba.

"ina wuni?" fahd ya durkusa. "lafiya kalau. mene sunan ka?" hajiya sa'adatu ce ta amsa "fahd sunansa" Alhaji bature bece mata komi ba ya maida hankalin shi wurin fahd "Allah ya maka albarka"

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now