Alhaji suleman (3)

472 35 2
                                    

washe gari fahd na gama shirin tafiya makaranta ya je ya zauna a gefen umni da jiya ta hau hada musu kayan su. "na tafi" ya fadi. smile tayi masa "allah yayi maka albarka kaji?"

shima murmushi yayi ya mike ya tafi. besan ko ina zasu ba kuma ko kadan beyi gigin tambaya ba.

yana zuwa makaranta be shiga aji ba ya tafi wannan class room en yana duna littafin sa. ba a dade ba itama zia ta shugo tana ta yake baki.

"good morning ". kallo ya bita dashi har ta ajiye Jakarta ta zauna. "kasan wani abu?"

girgiza kai yayi kawai ita kuma ta kwantar da kanta a kan table. "kasan ae hamid ko?" duk da ya gane wanne take nufi se yace "a'a"

"kasan sa mana. wanda kuka taba gaisawa a waya". alamar "okk" yayi da bakin sa. "yauwa shi"

ta dago da kanta "wae yana sona. but na rasa yadda zan bashi amsa..."

"rabu dashi" fahd fada a takaice. dagowa zia tayi tana kallonsa yayin da shi take duba littafin shi kamar ba shi yayi magana ba.

takaici ya kama zia. shi kadai ta fada ma ya taya ta murna ama se abin ya zama banban "meyasa haka?"

shuru yayi be kula ta ba. littafin hannun shi ta kwace ta ajiye a gefe "I'm asking you...why?"

dago wa yayi yana kallon ta "sabida be dace ace kina soyayya a yanzuba. karat-"

"fahd. baza ka gane ba you're just too young ... i like him alot." zia ta hade hannun ta. "tor meyasa kika fada min tinda kinsan bazan gane ba?"

dafa goshi zia tayi "ba haka nake nufi ba... i mean kai baza ka gane ba. but yan gidan mu zasu gane sabida background en mu daya da shi hamid"

"me ya kawo family background maganar nan?" ya dan bata rai. "fahd he wants to marry me fa. kamar nan da shekara 6 ko 7 fa"

nagode

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now