ikirarin so (3)

1.1K 72 0
                                    

Bayan anfito break yan ajinsu suka zagaye ta suna son kulla abokanta amman ita zia sam hankalinta baya kansu. Yake kawai take masu sabida karda a dauke ta a yar girman kai.

Gannin abin nasu ba me karewa bane yasa zia ta mike tare da fadin "na wuce shop" thom suka amsa sannan tayi gaba.

wani dogon layi ne a wurin kaman na shiga aljanna kallon wurin ma ya ishi mutum yaji jiri balantana ace ma a ciki kake.

Ji tai an tabota ta baya. Juyawa tayi ta hada ido da wannan yaron. Murmushi ta sakar masa hade da shafa mi kanshi "dan aboki na! Wae me'an sunan ka?"

motsa bakinshi ya danyi kamin ya furta "fahd" zia zumburo baki ta danyi "fahd ashe kana magana? Ni sunana zia. Will you be my friend?"

Gyada kai yayi alaman eh. Hakan yasa taji dadi sosai ta kara janshi zuwa wani tsohon class room da ba me zama a ciki.

"Shekarun ka fa?"

"Sha biyu" yabata amsa kai tsaye

Dariya tayi ta kuma tambaya
"Fahd kana sona?" Shuru yayi yana wasa da yatsunshi

Ita kuma ikirarin so zata fara?

Ganin fuskanshi tayi alamin blushing yasa wata dariyar ce ta kufce mata "kar ka damu ni I'm fifteen so bama zae yiyu ba"

Kallo yabita ta shi. Wane ya gaya mata haka?

Hira ta fara mashi me abin daria duk da bashi da fara'a seda ta sasa murmushi. Haka suka shaku a lokaci guda ahankan ma da kyar ya karbi cway da oreo cookies inda ta bashi.

Karaurawa aka kada hakan yasa su katse hirar tasu suyi sallama. Dawowar ta aji aka fara english. Zia ta fahimci daliban nada matsala a wannan fannin hakan yasa ta yanke shawarar koya ma fahd.

Da aka tashi principal ya tsayar da su introduction. Se wurin 2:30 aka bar su suka fito.

Na gode.

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now