ikirarin so (2)

1.4K 87 0
                                    

Cikin hanzari ta isa wurin da suke tare da shiga tsakanin su. "Haba dan allah? Baka ganin yadda ka buge shi?" Ta tsawatar mashi ba kamanin masu tsoro ko kadan a fuskarta. Hakan da tayi ya jawo hankalin dalibai da yawa.

Wanni dogon tsaki saurayin ya ja kamin ya raba ta gefen ta ya wuce. Suma abonkansa sakin yaron sukayi kowa ya watse.

Maida hankalinta kan yaron tayi wanda ke tsungune ya rike cikinshi. "Sannu...da ciwo? Allah zaya saka maka" kwata kwata ji take kaman ta fashe da kuka.

Dago fuskar tashi tayi nan taga dan karamin bakin shi a fashe kuma kuncinsa na hagu a dan kumbure kadance war shi yaron very fair yasa wurin yadanyi purple. Amma abin mamaki babu hawaye ko kadan a idanun shi.

Sakin fuskarsa tayi sa'annan ta kamo hannun shi suka mike. Shidai har yanzu biya ce eh abran a'a. Ido kawai ya zuba mata har ta kaisa SS3 anan ta bude jakan ta ta fido da mini first aid kit da daddy ya sayo mata daga japan.

Nan ta hau treating insa. Tabasa pain killers a komi.

"Kaga ba yanxu za'a koma aji ba so ka kwanta zan tashe ka" kada kanshi yayi alaman thom ya kwanta tare da lumshe ido.

Bin fuskar shi tayi da kallo tare a furta subhaanallah

Fari ne shi amma farin nashi ba dau ba. Irin haken nan ne na larabawan da suka amshi hutu shima hutu ya amshe su. Gasa da hanci dogo kaman anzana da ruler. Giran shi da lashes insa baki sidik kuma a cike kaman gashin kanshi da aka aske sama sama. Yaron dai he is so adorable a lokaci guda ya shiga ranta

Tana kallonsa batasan lokacin da awa daya da rabi ta tafi ba seji tayi ana kada bell. Tattabo sa tayi a hankali nan ya bude idonsa wanda yake ash with specks of green an amber.

"Tashi na raka ka class" nanma tashi yayi ba tare da magana ta komo hannunshi

Har kofar JSS3 ta kaisa kamin ta juya.

NA GODE




Shahara (Hausa Love Story)Onde histórias criam vida. Descubra agora