BABI NA GOMA SHA BIYAR

1.3K 109 4
                                    

DEDICATED TO AUNTY SALIHA AA ZARIA.

Sai da Mariya ta sami barci sannan yace mini zai tafi sai da safe. Har ya fita nabi bayanshi da sauri nace "Yaya Imran me yasa ka bari ta sani? Ina alkawarin da kayi mini cewar ba zaka taba bari ta sani ba?"

Juyowa yayi ya kalleni kafin yace "ban taba yin abinda Mariya zata yi tunanin da akwai wata alaka a tsakanina dake ba Maryam, dukkan abinda zai nuna mata hakan nayi matukar kokari wajen ganin na boye mata shi, lafiya lau muka rabu na taho aiki.

Har na fara attending to patients na tuno nayi mantuwar laptop ďita kuma akwai muhimmin amfanin da zan yi da ita, har nayi tunanin kiran Abba nace yaje ya ďauko mini na fasa ganin na fishi kusa da gidan, haka na fita na koma ashe rabon zan koma na tarar da tashin hankali ne, tunda nayi knocking banga tazo ta buďe ba nasan ba lafiya ba  don Mariya najin horn ďin motata take fitowa don haka nayi amfani da keys ďin hannuna na buďe gidan.

Ďakinta na fara shiga ban ganta ba sai na shiga ďakina anan na ganta a kwance a cikin mawuyacin hali, nayi saurin isa gareta na tarairayota babu numfashi a tare da ita, sauri nayi na ďauko ruwan sanyi na shafa mata sannan naji taja doguwar ajiyar zuciya, sai da naga ta samu amma numfashinta bai koma normal ba ga alama ciwonta ne ya tashi na ďaga ta zan maidata gado anan naga ruwa na fita a jikinta shine nayi sauri na canja mata kaya na sanarwa su Goggo na kawota asibiti, labour room na wuce da ita inda suna dubata suka tabbatar mini da haihuwa zata yi ga kuma halin da take ciki, a take suka saka mata oxygen da ruwan nakuda.

Ban san me ya haddasa hakan ba sai ďazu da naje gidan, ina ganin aiki take yi a ďakin taci karo da wasikar da kika yiwo mini lokacin rikicin aurenmu kina rokona na sadaukar da son da nake yi miki ga Mariyar don akan gado naga letter na tabbatar kuma ita ta karanta ta sami wannan matsalar".

Ajiyar zuciya na sauke nace "amma kasan sakacinka ne ya janyo hakan, don miye baka yaga wasikar ba tuni ka ajiyeta bayan kasan a kowanne lokaci Mariya zata iya gani? Na sha faďa maka bazan iya yafe maka ba idan har ka bari wani abu ya faru da Mariya ta dalilinka".

Ban jira jin abinda zai ce ba na juya ďakin na barshi anan. Na iske Mariya nata sharar baccinta cikin kwanciyar hankali ga alama dai sauki ya fara samuwa.

Ban zauna ba, banďaki na shiga na ďauro alwala na fara nafila ina rokawa Mariya sauki a wurin ubangiji.

Ban kwanta ba sai kusan asuba, har na fara bacci akan kujera a gaban gadon Mariya naji motsin hannunta a kaina.

Buďe ido nayi nace "sannu Mariya, me kike so?" Murmushi tayi sannan a hankali cikin murya irin ta marar lafiya tace "taimako nake so kiyi mini Maryam".

Matsawa nayi kusa da ita nace "name fa?" A hankali tace "baby zaki ďauko mini na ganshi, ina so na ďaukeshi domin yaji ďumin jikina once a rayuwarshi".

Bata fuska nayi nace "bana son irin wannan Maganar, in dai baby ne zan kawo miki shi ki ganshi, In Allah ya yarda zaki rayuwa da ďanki rayuwa mai tsawo har sai kinga 'ya'yanshi".

Wani irin murmushi tayi mini wanda ba zai taba bacewa a raina ba. Jikina a bala'in mace na ďauki wayata na kira Dr. Abubakar na sanar da shi abinda Mariya take so yace gashinan zuwa.

Ba'a daďe ba ya shigo da wata nurse da baby a hannunta an nannaďeshi cikin farin shawl, yayi wa Mariya sannu, nurse ďin kuma ta mika mata baby bayan na taimaka mata ta zauna sosai yadda zata ji daďin rike yaron, da zasu fita Dr yace "idan ta gama Maryam a maida musu shi".

Ta buďeshi tayi mishi addu'a har a gabanshi, ta daďe tana kallonshi kafin ta rungumeshi ta fara kuka.

Cikin rawar murya nace "menene haka? Haba Mariya me yasa kike son tada mini hankali ne?"

MURADIN ZUCIYAWhere stories live. Discover now