BABI NA GOMA SHA UKU

1.3K 104 6
                                    

DEDICATED TO AUNTY SALIHA AA ZARIA.

Anyi biki lafiya, amarya ta tare a ďakinta. Ummie bata da laifi don tana bani girmana nima kuma na rike girman nawa.

Ina dai ganin buduri ni Maryam, yadda Najib ke rawar kafa akan Ummie abin har namaki yake bani sai dai hakan bai taba damuna ba.

Sati guda yayi yana hutu, a cikin wannan sati gudan kuwa idan har ka ganshi ya fito parlour to amaryarshi tana ciki, idan kuwa zata yini a ďaki tare zasu yini, don ma tana da kunya da kawaici don na lura bata cika son suna barina ni kaďai ba don ko a kitchen nake zata zo tace "Aunty Maryam me zan tayaki?"

Sai nace "a'a ina amarya ina aiki? Ai hutu ya kamace ki don haka ki kwanta ki huta abinki" sai taki. Haka nan ko a ďaki nake zata biyoni har ďaki tana mini hira.

Gaskiya a yadda ake faďin kishiya sai nace ni kam nayi sa'a nayi dace da ta kwarai.

Ko da ta gama aikinta na kwana bakwai na karbi aiki bata canza zani ba, mun cigaba da yadda muka saba, yana ďakinshi ina nawa.

Ummie ta saba da 'yan uwana don ko ina zani tare muke zuwa. Hajiyarsu Najib bata taba banbantani da ita ba wai don tana tata, kullum nasihar mu zauna lafiya take yi mana ta kance "ku duka nawa ne babu wacce nafi so akan 'yaruwarta.

Ummie kada kiga ke 'yata ce itama Maryam tawa ce tunda wanda ya aurota ďana ne".

Tun Mariya na shareta har ta hakura ta gane yarinyar mai halin kwarai ce, sai ya zamana ma ta kira Ummie sun sha hirarsu sai dai tace a gaisheni.

Period nake yi, wannan karon yazo mini da bala'in ciwon da na daďe ban yi ba. Najib ya kaini asibiti, sai da ya kira Yaya Imran ya sanar mishi shine yace mu haďu office ďin Dr. Koguna.

Dr. ta dubeni tace "Maryam ina mamaki, masu irin larurarki da sun yi aure suke rabuwa da ciwon, amma ke gashi an ma daďe da auren ko?"

Na kalli Najib shima ya kalleni ya kauda kai. Sai Yaya Imran ne ya amsata da "eh, sun ma fi shekara da auren" tace "to ina ganin zan baki wasu tests mu gani don mu san inda matsalar take".

Ta rubuta mini magani haka nan ta cike lab request form ta miko mini tace lallai naje nayi su a washegari sannan ta sallamemu.

Muna tafe zuwa inda Najib yayi parking mota, suna gaba ina biye dasu a baya sai dai sun ďan bani tazara kaďan.

Yaya Imran ne ya cewa Najib" kada dai kace mini har yau baka bawa Maryam hakkinta na aure ba?" Tsaki yayi yace "to yaya zan yi Imran? Na sani ina ďaukar alhakinta amma ba zan iya bane sai naga kamar naci amanar ka ne".

Tsaki shima Yaya Imran ďin yayi yace "shirme kenan, ni wannan batun tuni ya wuce a wurina, idan nayi la'akari da ďan da Mariya zata haifa mini, ina ganin hikimar Ubangiji don wani baya taba haihuwar ďan wani.

Ban taba tunanin hakan ba, to Allah yayi Mariya ce matata uwar 'ya'yana duk da Maryam naso, amma nayi hakuri ina mai fatan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a garemu baki ďaya, ni nasan akwai hikimar Ubangiji cikin al'amuran mu don haka  ka gyara gidanka gudun faďawa halaka, hakkin Maryam zai iya kai ka wuta"

Najib yace "nagode Imran, In Sha Allahu zan yi kokari na gyara". Sai da yaga tafiyarmu sannan ya koma bakin aikinshi.

Kulawa sosai Najib ke bani har na warke. Tafiya ce ta kamashi zuwa Abuja ta sati ďaya, yaso tafiya da Ummie to tana fama da laulayin ciki, ni ke kula da ita don haka ya sallamemu ya tafi.

Kullum sai mun yi waya da shi har sati ďaya ta cika. A ranar da zai dawo Ummie ta takura wai sai mun je mun yi lalle kwalliyar sannu da zuwa.

Dariya nayi nace "ai ke ya kamata kiyi kwalliya Ummie domin kece amarya, ni kwalliyata tuni ta dushe" tace "ban yarda ba Allah kawai ki tashi mu tafi".

Dole naje aka rangaďa mana kunshi, ni jan lalle kawai nayi ita kuwa harda fulawa aka zana mata, mune har da yin kitso. Ummie sai tsokanata take yi wai na fito shar nama fita yin kyau.

Nace "haka kike gani yarinya amma yau ai inaga angonki ba zai gane ki ba".

Haka muka koma gida muna ta zolayar juna.

Mun yi shirin taron maigida zuwanshi kawai muke jira, karfe takwas Sabi'u kaninshi yazo yana shaida mana wai Najib na asibiti yayi accident.

Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raji'un kawai nake ambato ita kuwa Ummie tuni ta fara kuka tana cewa shikenan tasan ya mutu Sabi'u ke boye mana, lallashinta ya fara yi yana cewa "ku kwantar da hankalinku don abin yazo da sauki, karaya ce ya samu a kafarshi ta dama sai bubbugewa da yayi da ciwuka da yaji, ai an auna arziki tunda abin yazo da sauki".

Sabi'u ne ya tuka mu zuwa asibitin. Kamar yadda yace ne mun samu abin yazo da sauki sosai, sai 'yan ciwuka a jikinshi.

Mun sami Alhaji dasu Hajiya tare da 'yan uwanshi duk a wajen, sai da muka gaisa dasu tare da jajantawa juna sannan muka matsa muka yi mishi sannu.

Sai karfe goma Alhaji yace duk mu tashi mu tafi gida Murtala kaninshi zai zauna a wajen shi.

Washegari aka yi mishi gyaran kafar ya cigaba da karbar magani, a asibiti muke yini kullum don ni wani lokacin ma daga school nake wucewa can sai dare yayi sannan na maida mu gida.

'Yan uwana duk sun je sun duba shi, Yaya Imran kuwa da ya samu sararin aiki zai zo ya dubashi, abotarsu dai ta dawo sosai. Kusan duk dare wurin shi muke hira har Mariya mai tsohon ciki.

Najib ya fara samun sauki don har ya fara takawa don ciwukan jikinshi tuni suka warke.

Yau asabar ba zamu asibitin da wuri ba, na dai yi breakfast Sabi'u yazo ya ďaukar mishi, komawa nayi na kwanta barci.

Cikin barcin ne naji wayata ta dameni da kara, da kyar na buďe ido na janyo wayar. Sunan Goggo na gani akan allon wayar yana yawo.

Da sallama na amsa sannan na gaisheta, sai da muka gama gaisawa sannan take sanar mini wai Mariya ce a asibiti suma suna can.

Ai a take na watsake nace "ba dai haihuwa bace ko don kwanannan ta shiga wata bakwai?"

Goggo tace "to gamu nan dai Maryam amma 'yar uwarki tana cikin mawuyacin hali, ciwonta ne ya tashi da nakudar baki ďaya".

Ai ban ma gama sauraren Goggo ba na kashe wayar na duro daga kan gado, cikin sauri na shirya sannan na kira Najib na sanar mishi.

Ďakin Ummie na shiga itama na faďa mata. "Allah ya bata lafiya, nima zan zo in anjima".

Ina shiga AKTH labour ward na wuce, anan na tarar dasu Goggo sunyi jigum-jigum don Umma Aisha ma gani nayi kamar kuka take yi.

A tsaitsaye muka gaisa nace "Goggo ya ake ciki?" tace "to mu dai tunda muka zo bamu ganta ba". Na sake tambaya "ina Yaya Imran fa?" Umma Aisha ce tace "yana ciki, ya dai fito ya shaida mana haihuwa zata yi sai dai bakwaini ne".

Nabi layin su Goggo na zauna ina karanto duk addu'ar da tazo bakina.

Har kusan sallar la'asar kafin Yaya Imran ya fito. Mama ce ta fara tambayarshi "yaya ake ciki?"

Yace "ta haihu namiji sai dai bakwaini ne amma ita kam bata san inda kanta yake ba".

Tuni na fara kuka ina cewa "meya sameta? Tana ina yanzu? Ka taimakeni ka haďani da ita don Allah".

Shi kanshi abin a tausaya mishi ne don kuwa yayi zuru-zuru kamar dai ba likita ba. "Kiyi hakuri Maryam" yace mini. "Ba zasu barki ki shiga ba, ke dai kiyi tayi mata addu'ar Allah ya bata lafiya don abinda tafi bukata daga gareki kenan a yanzu".

Najib ya kirani yana tambayar yaya ta haihu? Fashewa kawai nayi da kuka, cikin tashin hankali yake tambayata lafiya?

Da kyar na iya yi mishi bayanin halin da take ciki, lallashina yayi tayi yace "kiyi mata addu'a Maryam, ki zama jaruma, idan kina kuka yaya kike so Goggo tayi? Ki daure zuciyarki kinji? Zan sake kira naji halin da ake ciki".

UMMASGHAR.

MURADIN ZUCIYAWhere stories live. Discover now