BABI NA ĎAYA

6.2K 292 15
                                    

DEDICATED TO AUNTY SALIHA AA ZARIA

Gidan mata uku shine sunan da ake kiran gidanmu a unguwar Ďandago dake cikin birnin Kano. Gidanmu na nan a bayan makarantar Ďandago special primary school. Gida ne da ya kunshi sassa uku.

Sashen Baba Ali, sashen Baba Sule sai sashenmu wato sashen Baba Kabiru. Akwai albarkar 'ya'ya a gidanmu don kowanne sashe na ďauke da yara maza da mata. Baba Ali da matarsa Sa'adatu wacce muke kira da Mama suna da yara bakwai. Sai Baba Sule da Matarsa Aisha(Umma) da 'ya'yansu huďu.

Sai sashenmu, mu uku Goggonmu mai suna Habiba ta haifa. Mariya da ni Maryam 'yan biyu ne sai kaninmu Sagir wanda tazarar shekara takwas ne a tsakaninmu.

Asalin mahaifinsu Baba Mallam Lawan mai almajirai yawon almajiranci ya fito dashi daga garinsu Numan ďin jihar Adamawa yazo Kano, anan yayi karatu har Allah yasa shima ya zama malami.

Mallam Lawan mutum ne mai dattako sai dai yana da zafi sosai, baya ďaukar raini, almajiranshi na shakkarshi sosai. Matarshi ďaya Inna Abu. Auren zumunci sukayi tun auren saurayi da budurwa. Inna Abu macece mai tsananin hakuri da sanyin hali hakan ne yasa suka yi zaman lafiya da Mallam har mai rabawa ta rabasu wato mutuwa.

Yanzu haka tana nan a cikin gidanmu. 'Ya'yansu huďu da Mallam. Babbar macece wato Goggo Zulai, sai Baba Ali, Baba Sule sannan Babanmu Kabiru.

Mallam ya rasu tun muna da shekaru uku da haihuwa. Goggo Zulai tana auren wani ďan kasuwa a yakasai da 'ya'yanta shida. Baba Ali da Baba Sule a singa suke kasuwanci, Babanmu kuwa malamin makarnta ne, da a nan Ďandago yake headmaster daga baya aka maida shi Aminu Kano Commercial College a matsayin principal.

Duk da yanzu babu almajirai amma ana karantarwar dare a kofar gida haka nan akwai wasu almajiran da suke zaune a gidan suna karatunsu na boko, wasu kuma suna kasuwanci sun kuma zama 'yan gida don idan ba an faďa ba babu mai gane cewa ba 'yan gidan bane.

Yaran gidanmu nada kyakkyawar tarbiyya don yadda muke faďawa yayyenmu Yaya haka suma muke kiransu, haka nan kan iyayenmu mata a haďe yake babu gulmace-gulmace da ake yi a yawancin gidajen yawa.

Da wuya yaro ya gama karatunshi na secondary a gidanmu ba tare da ya sauke AlQur'ani ba, akwai kwakwalwa a wurin yaran gidanmu don haka mutane ke cewa wai akwai abinda Mallam yayi wa zuri'arshi da suka fita zakka a cikin sauran yara wanda ba haka bane Allah ne dai yayi mana baiwar kokari.

Duk cikin 'ya'yan gidanmu babu da wanda tamu tazo ďaya irin Yaya Imran, shi ne yasan halina yake kuma biye mini, koda yake Inna tace wai sai hali yazo ďaya ake abota don kamar yadda nake miskila shima haka yake miskili.

Miskila ce ni ta ajin karshe don zan iya yini ban yi magana ba. Abokan maganata biyu ne daga Mariya sai Yaya Imran. Idan har aka jini ina doguwar hira to dasu ne.

Ko baki akayi a gidan sai Goggo tayi ta faman faďa kafin na sake na gaishesu. Haka nan kuma bana ďaukar raini don kuwa komai girman mutum idan naga yana neman takani yanzu ne zan yagashi.

Sai dai kuma ina da walwala da sakin jiki da duk wanda na saba dashi ya kuma fahimci halayena, saboda haka nema yasa bani da waau kawaye don kawayena biyu ne daga Husna Imam sai Zubaida Umar, su kam jinina ya haďu dasu sosai.

Idan naso ina da tsokana amma tsokanata tafi a Mariya wacce halinmu yasha bambam. Ita kam tana da son mutane da haba-haba dasu gata da saurin sabo, sai dai tana da faďa, tana da saurin fushi amma idan tayi faďanta ya wuce don bata da riko ko kaďan.

Duk faďan nan nata da wuya kaji tayi mini har sai idan na kureta. Tana sona sosai hakan ne ma yasa Goggo ke cewa ina cutar da ita saboda son da take mini. Nima kuma ina sonta sosai don ko da wasa bana son bacin ranta.

Umma Aisha na yawan cewa bata taba ganin 'yanbiyu dake son junansu kamar mu ba don ko ciwo nake yi Mariya ta bar yin sukuni kenan har sai taga na warke nima kuma haka nake yi duk sanda ta kwanta rashin lafiya.

Kamar mu ďaya da Mariya sai dai ita fara ce tas kalar Babanmu ni kuma bani da haske don na ďebo kalar fatar Goggo ne wato chocolate colour.

Yaya Imran ne babban ďa a duk gidanmu. Ďan Baba Ali ne da Mama Sa'a. Yana karatun medicine a BUK. Allah ne kaďai yasan tsakaninmu don duk wata shawara tashi ko tawa tare muke yi, ko budurwa yayi sai ya faďa mini idan naga sun dace na bada goyon baya idan naga basu dace ba nace kawai shareta.

Kamar yadda Inna tace ne, shima kusan halinmu ďaya sai dai shi yana da hakuri bar shi dai da miskilanci. Ko kaďan Mariya bata shiri da Yaya Imran, kullum cikin yi mini mita take akan shi wai nafi son shi da ita.

Sai dai nayi dariya nace "twin kenan sarkin kishi, ke fa tare muka yi rayuwa tun a ciki aka haifemu tare. A ganinki akwai wani mahaluki da zan so fiye da son da nake yi miki? Kawai dai Yaya Imran is special to me, duk cikin 'yanuwana kinga yafi kowa kulawa dani da kuma sanin halina".

A gaskiya mun daďe muna muku-mukun son juna ni da Yaya Imran sai dai kowa yana ji da miskilanci don haka muka bar abin a cikin zukatanmu.

Bana mantawa muna ss2 shi kuma a lokacin zai tafi housemanship Maiduguri, mun dawo daga islamiyya tare da kannenmu muka ganshi a kofar gida shi da abokinshi Munir.

Gaishesu muka yi muka wuce, har mun kusa shiga gida Munir ya kirani na dawo. Kallon fuskar Yaya Imran nayi naga ya bata rai sai naji banji daďi ba don ban saba ganin hakan a tare dashi ba. "Gani Yaya Munir".

Yace "Imran ya taba baki sakona?" na kalli Yaya Imran ďin naga ya sake haďe rai ya ďauke kanshi. Girgiza kai nayi alamar a'a. Yace "Maryam sonki nake yi, ina kuma fatan zaki bani haďin kai don da gaske nake yi zan tura wurin su Baba don su san da zamana idan yaso idan kika gama secondary school sai ayi bikin. Ni dai fatana asan dani.

To amma Imran yace wai karatu zakuyi baya so ku haďa karatu da soyayya ni kuma tsoro nake ji kada wani yayi mini shigar sauri, idan don karatu ne i promise you zan barki kiyi karatunki a gidana har sai kin ce ya isheki".

Kallon Yaya Imran na sake yi don son samun amsar da zan bawa Munir ďin. "Wai babu sauki" na faďa a cikin zuciyata. "Don Allah kayi hakuri Yaya Munir, tuni na sallamawa wani zuciyata, nagode sosai da kaunarka a gareni" nace ina mai sunkuyar da kaina don sai naji kunyar haďa ido dashi.

Yace "ayya, babu komai Maryam, nima nagode da saurarona da kika yi. Ina taya wannan ďan gatan saurayin naki murna, he is a very lucky Man to have found you. Ina son kiyi mini addu'ar Allah ya bani wadda zata maye mini gurbinki a zuciyata" nace "In Sha Allahu zan yi maka, nagode". Daga haka na shige gida na barsu a wurin.

Fushi sosai na lura Yaya Imran keyi dani. Nayi iya tunanin laifin da nayi mishi amma na kasa ganowa. Nayi tunanin ko don naki Munir ne? Kai a'a don kuwa da ya soni da Munir da ya faďa mini tuni.

Ko wajenmu ya shigo sai dai ya sha hirarshi da Goggo tunda Mariya ma ba wani shiri suke yi ba. Ko a ďakin Inna muka haďu ana hira baya kulani, dana ga haka sai nima kawai na shareshi. Har ni zai nunawa miskilanci?

UMMASGHAR.

MURADIN ZUCIYAWhere stories live. Discover now