BABI NA HUĎU

1.4K 111 15
                                    

DEDICATED TO AUNTY SALIHA AA ZARIA

Sati ďaya Yaya Imran yayi ya koma. Admission ďinmu ya fito ni da Ruqaiya a BUK don dama Mariya ta fara karatunta tuni a school of nursing. Ni Mass communication na samu ita kuma Ruqaiya Micro biology.

Yaya Imran ya gama housemanship ďinshi har ya tafi NYSC a jihar Edo. Muma karatunmu ya fara miqawa don gashi har mun gama 100 level muna hutu, a lokacin Yaya Imran ya kusa dawowa daga bautar kasa a inda yace mini yana isowa zai gabatar da maganar mu a wurinsu Baba na kuma amince.

A wani dare ne muna kwance a ďakinmu don har na fara bacci sai naji kamar Mariya tana kuka. Tashi nayi zaune na ganta ta kifa kanta a gwiwa tana kuka a hankali.

Dafata nayi nace "Mariya lafiya? Me ya sameki cikin daren nan kike kuka?" Saurin ďagowa tayi tace "kuka kuma? Ba kuka nake yi ba".

Hannu nasa na shafo hawayen dake kumatun ta nace "miye wannan to? Ina ce hawayenki ne ke zuba". Gogewa tayi tace "ban san kuka nake yi ba, oh tunani fa kawai nake yi ashe harda kuka".

Na jima ina kallonta sannan nace "me ke damunki twin? Ina lura dake cikim kwanakin nan kina yawaita kaďaicewa kiyi tunani, kamar kina cikin matsala. Ki taimakeni ki sanar dani damuwarki, watakila akwai taimakon da zan iya yi miki".

Hawaye ne ya kara zubo mata tace "Maryam ina cikin masifa, zuciyata bata yi mini adalci ba, wai ta rasa wanda zata kamu da ciwon so sai mutumin da bai san tana yi ba, bama na tunanin zai taba sona. Tun ina gargaďinta da cewar abinda take son yafi karfinta bazata same shi ba har na hakura tunda kullum son nasa karuwa yake yi, yanzu abin nema yake yafi karfina don ji nake yi idan har ban same shi ba zan iya rasa raina akan son da nake yi mishi".

Nace" Ikon Allah, Mariya ta soyayya. To waye wannan, wane ďan gata ne yayi nasarar sace zuciyar twin ďita haka da sauri?" Tace "zan faďa miki ko wanene amma ba yanzu ba, ke dai ki tayani da addu'a Allah yasa ya soni ya kawo kanshi gareni don nasan duk irin son da nake yi mishi bazan taba iya furta mishi ina son shi ba koda kuwa son zai zama silar ajalina".

Hannu nasa na rufe bakinta nace "In Sha Allahu zan fara yi miki addu'a daga yau, idan Allah yaso da kanshi zai zo ya furta miki kalmomin soyayya, sai dai don Allah ina so ki rage yawan damuwa, kin san sarai yanayin da lafiyarki take ciki, da wannan damuwar gara ki tashi ki faďawa Allah shi yasan daidai sai ya zaba mana abinda yafi alkhairi".

Tace "In Sha Allahu zanyi yadda kika ce, nagode Allah da ya bani ke a matsayin 'yaruwa kuma abokiyar shawara".

Ranar lahadi su Baba a gida suka yini, Goggo Zulai ma tazo don haka suka tattaru a ďakin Inna suna ta hira. Can da yamma 'yar autar Mama wato Nana tazo tace "Yaya Mariya wai ki zo inji su Baba".

Dafa kirji Mariya tayi tace "na shiga uku, me kuma nayi? Ni fa bana son ayi taron dangin nan sannan a kirani". Goggo tace "ke bana son sakarci, ko meye ma kije mana kiji". Tashi tayi ta tafi ina yi mata dariya.

Ta ďan daďe kafin ta shigo gidan da murnarta ta kama hannuna ta jani ďakinmu. Muna shiga ta rungumeni tace "Maryam Allah ya amshi addu'ar mu, wai su Baba zasu haďani aure da Yaya Imran".

Daskarewa nayi a tsaye nama rasa a wacce duniyar nake tsabar ruďani. Taci gaba da cewa "i've been in love with Yaya Imran for sooo long Maryam, he's my secret admirer, shine wanda zuciyata ta daďe tana MURADI. Ina yi mishi wani irin so da bakina bai isa ya iya bayyanawa ba".

Jin nayi shiru ne yasa ta sake ni tace "menene Maryam? Ba kya farin ciki ne? Ba zai so ni ba ko?" duka ta jero mini tambayoyin.

Kakalo murmushin yake nayi nace "of course i'm happy for you. Mamaki ne ya ishe ni ganin yadda kuke yiwa juna, ban taba tunanin zaki iya son Yaya Imran ba saboda ganin ba ra'ayinku ďaya ba. Sai dai na manta shi so babu ruwan shi da wannan. Amma nayi farin ciki, kun dace kuma nasan shima zai soki. Allah yasa alkhairi za'a kulla".

Dariya tayi tace "dama rashin shirinmu dashi duk kishi ne ya haddasa, ada nayi tunanin son juna kuke yi, sosai nayi bincike daga baya na gane shakuwace da kauna irinta zumunci a tsakaninku".

Nisawa tayi ta cigaba da cewa "yanzu miye shawara don ina tsoro gani nake yi kamar ba zai soni ba".

Karfin hali kawai nayi nake zaune ina sauraren Mariya tana fayyace mini irin son da take yiwa Yaya Imran. Sai da na saisaita muryata sannan nace "me zai hana shi sonki? A tunani na baya da wacce yake so bare ya qi ki, sannan kuma umurni ne kawai za'a bashi kuma dole ne yabi.

Sama ace baya sonki, hakkin kine ki nemawa kanki soyayya a zuciyarshi da kyawawan halayenki da kuma kissa irinta 'ya mace bare ma zanyi duk yadda zanyi sai kin kafu a zuciyarshi.

Kin san mutumina ne, ke dai ki kwantar da hankalinki In Sha Allahu everything will be alright. Yaya Imran zai soki, sai kin yi mamaki da irin son da zai nuna miki" tace "Allah yasa 'yaruwata".

Idanuna fal da hawaye na fita daga ďakin. Sashen Umma Aisha na wuce, suna zaune a parlour na shige kuryar ďakinta  na sha kukana.

Sai da na gaji don kaina na bawa kaina hakuri na tashi na koma wajenmu. Ďakin Goggo na shiga na haye kan gadonta na kwanta ina cigaba da kuka.

Oh! Ni Maryam na cutar da kaina don kuwa ya zamar mini dole na hakura da Yaya Imran na barwa 'yaruwata. Sai dai kuma idan na hakura yaya zan yi da ďumbin son da nake yi mishi? Na sani zan mutu ne da so da kaunarshi. Sai dai zan yi kokarin fahimtar dashi ko don na ceto rayuwar 'yaruwata.

Kafin dare yayi matsanancin zazzabi da ciwon kai sun rufeni. Duk da na sha magani har gari ya waye zazzabin bai sauka ba. Cikin kwana ďaya na rame na jeme na fita daga hayyacina.

Kwana biyu ina fama da zazzafan zazzabi da ciwon kai mai azaba, takurani Goggo tayi akan sai naje asibiti don haka na shirya ba don ina so ba Yaya Abba ya rakani.

Naga likita ya rubuta mini magungunan da zamu saya sannan ya faďawa Yaya Abba cewa damuwa ce tayi mini yawa, na rage yawan tunani don kuwa jinina yana gab da fara hawa.

UMMASGHAR.

MURADIN ZUCIYAWhere stories live. Discover now