BABI NA BIYAR

1.5K 112 2
                                    

DEDICATED TO AUNTY SALIHA AA ZARIA

Tun a hanya Yaya Abba yake tambayar abinda ke damuna da har yake barazanar sanya mini hawan jini. Nace "ni fa Yaya Abba babu komai, sai dai ko zazzabin ne yasa hakan".

A gida yayi wa Goggo bayanin abinda likita yace. Itama hankalinta ya tashi tayi ta tambayata abinda ke damuna, amsa ďaya nake bata cewa babu komai.

Sosai ranta ya baci har tana faďa tana cewa idan ban faďa mata damuwata ba wa gareni da ya fita da zan faďa mishi. Kuka na saka mata, sai kuma ta koma lallashi tace "haba Maryam, idan baki faďa mini damuwarki ba wa zaki faďawa? Ki faďa mini watakila ba zan rasa abinyi ba akai".

Cikin kukan nace "babu abinda zaki iya yi mini da ya wuce addu'a Goggo, na riga nayi wa kaina, sai dai na bar hakan a matsayin kaddara bani da abin yi sai hakuri".

A hassale tace "ke ni kiyi mini bayani yadda zan fahimta ba wai ki tsaya yi mini dogon turanci ba".

A nan na zayyane mata alakarmu da Yaya Imran har zuwa yanzu da yadda muka yi da Mariya tun ma kafin nasan waye take so har zuwa haďin da aka ce za'a yi musu da goyon bayan dana bawa ita Mariyar.

Goggo tayi salati tana tafa hannayenta tace "amma dai Maryam zurfin cikin ki yayi yawa. Don me baki shaidawa 'yaruwarki ba? Ko ni ban taba tunanin soyayya kuke yi da Imran ba, mu duk a tunanin mu Najib ke son ki, wannan wauta da me tayi kama?

Amma tunda haka ne yau zan sanar da Baban ku idan yaso sai a fasa da Mariya tunda Allah ya taimaka ba'a kai ga ďaura auren ba na sani".

Sauri nayi na rike hannunta ina kuka nace "don Allah kada ki faďawa Baba, idan aka aura mini Yaya Imran yaya Mariya zata yi? Kin san tana yi wa Yaya Imran wani irin so da idan har ta rasa shi komai yana iya faruwa da ita, kuma kada ku manta da yanayin ciwon ta.

Ni na hakura, dana rasa 'yaruwata gara ace na rasa auren Yaya Imran. Kada ki damu Goggo, wannan halin da nake ciki na ďan lokaci ne, zan cigaba da rayuwata mai daďi. Ni dai burina Mariya ta kasance cikin farin ciki ta cimma burinta.

Kiyi mini addu'a Goggo, Allah ya bani wanda zai mantar dani Yaya Imran ya kuma so ni fiye da yadda yake sona duk da nasan mawuyacin abu ne son shi ya rabu da zuciyata".

Goggo ta goge kwallar da ta zubo mata  tace "ni na ma rasa abin cewa. Itama Mariyar idan tasan tsakaninku da Imran hakan zata yi" nace "don Allah Goggo kada ki bari Mariya taji zancen nan, shi kuwa Yaya Imran nasan ta yadda zan bullo mishi".

Goggo tace "Allah yayi muku albarka ya kuma zaba abinda yafi alkhairi a gareku baki ďaya".

Tun daga wannan ranar na daina kiran Yaya Imran a waya sai dai bana kin ďauka a duk lokacin da ya kirani mu sha hirarmu, sai dai bana sakin jiki kamar da shi kuma yayi ta mita kenan, bana dai ce mishi komai.

A kullum tunani na yadda zan fidda soyayyata daga zuciyarshi ne na cusa na 'yaruwata, sai dai nasan sai na sha fama dashi akan ya hakura ya amince da aurenta ba tare da tasan tsakaninmu ba.

A ranar da Yaya Imran zai dawo ban yini a gida ba. Gidan su Zubaida naje don dama tayi mini waya tace Mamanta bata da lafiya. Sai daf da magriba na dawo.

Tun daga kofar gida yaran gidan mu ke shaida mini dawowar shi. Gaba na ne naji yana faďuwa, a haka na daure na shiga gida. Itama Mariya dawowar tashi take faďa mini.

Tace "Maryam baki ga yadda ya kara kyau da kwarjini ba, ni duk na sare gani nake yi kamar yafi karfin ajina". Nace "ai kin ji ki, ta ina yafi karfin naki? Kawai ki fara tunanin ta yadda rayuwar aurenku zata kasance ba ki tsaya tunanin shirme ba. Bari nayi sallah na kai gaisuwa tun kafin yazo yayi mini tijara".

MURADIN ZUCIYAWo Geschichten leben. Entdecke jetzt