BABI NA GOMA

1.5K 111 24
                                    

DEDICATED TO AUNTY SALIHA AA ZARIA

Tashi nayi na shiga wanka, bayan na fito na shirya a cikin atampa super exclusive coffee colour ďinkin plain zani da riga free fitted. Ban yi wata kwalliya ba sai powder dana shafa da lip gloss dana saka a lebunana.

Sosai kayan suka yi mini kyau suka amshi jikina. Ďan karamin hijabi na saka sannan na fita parlour. Ban daďe da zama ba Sakina kanwar Najib tayi sallama ta shigo da kayan breakfast.

Dining table ta wuce ta ajiye basket ďin kayan karin data riko sannan ta dawo muka gaisa tace "su Hajiya sun ce a gaisheki" nace "ina amsawa".

Tashi tayi zata tafi nace "kai haba daga zuwanki, ke kuwa ki zauna mana kya tayani hira" tace "Aunty Maryam Hajiya tace kada na daďe amma ai zamu zo in anjima" nace "to shikenan, ina zuba ido".

Ban ci abincin ba duk da yunwar dake damuna. Sai can Najib ya fito daga ďakin shi a shirye, gaishe shi nayi ya amsa mini da "ya bakunta?" Ban yi magana ba, na dai sanar dashi an kawo abin breakfast daga gidansu.

Har ya fara ci ya kalloni yace "ke kin ci ne?" Girgiza kaina nayi alamun a'a yace "saboda me? Ki zo kici abinci" nace "ka gama tukunna". Bai sake cewa komai ba ya cigaba da cin abincin shi har ya gama, ya tashi yace mini zai je gidansu, nayi mishi adawo lafiya ya fita.

Ina cikin karyawa Mariya ta kirani, gabana ne naji ya faďi. Na ďaga wayar na kara a kunnena nace "ran amaryar Yaya Imran ya daďe, sai yanzu kika tuna dani?"

Tace "babu wani nan, ke da tun jiya nake nemanki wayarki a kashe, to ya kwanan amarci?"

Nayi dariya nace "amarci yana wurinku manya, ina fatan dai komai normal" tace "babu laifi, ina Najib?"

Nace "ya fita" na cigaba da cewa "Mariya duk kewa ta isheni, duk da rashin son mutane na amma shirun gidan nan yayi yawa". Tace "sai hakuri Maryam, auren kenan, a haka zaki saba".

Mun daďe muna hira kafin muka yi sallama. Cikin raina nace Allah Sarki Mariyata, Allah dai yasa ta samu farin cikin da nake mata fata.

Wajen azahar kannen Najib suka zo da abincin da Hajiya ta aiko su da shi. Anan suka yini har dare sannan Najib yace na shirya muje gidan su.

Acan muka yi dinner, duka yayyenshi mata da mazan tare da matayensu da kuma kannenshi na nan. Babansu yayi mana addu'a da nasihar zaman aure, haka nan su Hajiya sunyi mana nasiha bakin gwargwado.

Daga yadda familyn shi suke nuna mini gaskiya bani da matsala, ban sani ba ko a gaba, a yanzu dai kam Alhamdulillah.

Zaman mu babu yabo babu fallasa, ban rasa komai ba. Kowa yana iya bakin kokarinshi wajen ganin ya kyautatawa abokin zama.

Da wuya dai a ganmu tare mun zauna a wuri ďaya muna hira, kamar ma kunyar juna muke ji. Sai dai kullum shi yake kaini school ya kuma ďaukoni yace kafin ya samu time ya koya mini driving.

Ban sake jin ďuriyar Yaya Imran ba, duk lokacin dai da muka yi waya da Mariya ina cewa ta gaishe shi. Akwai ranar da muna waya nace mata ta gaishe shi sai cewa tayi "gashi nan ma bari na bashi ku gaisa".

Da sauri nace "bar shi kawai zan kira shi a wayarshi". Shima ina ji yace ta kyaleni zai kira ni.

Haka rayuwar ta cigaba da tafiya gashi har mun sami watanni biyar da aure. Duk tsawon watannin nan bamu taba haďuwa da Yaya Imran ba, ko a gida ko a gidanshi.

Ko wajena Mariya zata zo baya kawota sai dai ya saka Yaya Abba ko Yaya Mallam wani a cikinsu ya kawota.

Akwai ranar da naje gidanta. Najib ne ya kaini, bayan sun gaisa ne yake tambayarta Yaya Imran tace "bai jima da fita ba an kira shi a asibiti".

Tashi yayi yayi mana sallama ya tafi akan sai bayan la'asar zai zo ya ďaukeni.

Bayan tafiyar shi ne Mariya tace "rayuwarku tana birgeni twin, Najib na sonki".

Nace "babu laifi kam, amma kema ai ina ganin baki da matsala don kowa ya kalleki ya san kina hutawa alamar mijinki na kula dake".

Tace "to ni me zance miki ne ma Maryam, Yaya Imran na kulawa dani iya kulawa, babu wani abu da yake yi mini na musgunawa sai dai ina ganin kamar da akwai wata a zuciyarshi, har yanzu na kasa samun soyayyarshi.

Ina yin komai domin na faranta mishi amma idan tunanin wacce yake so yazo mishi fa baya ko son ganina a kusa dashi, dole nake janye jikina har sai abin ya sake shi".

Tausayinta ne ya kama ni ganin yadda take son maso wani, kenan har yanzu Yaya Imran bai sakawa ranshi hakuri ba? "Sai kiyi ta hakuri ki kuma cigaba da addu'a don babu abinda yafi karfin addu'a, wata rana sai labari sai kiga ya wuce kamar ma ba'a yi ba".

Tace "haka ne, nagode da shawara twin" ta cigaba da cewa "sannan wani abin mamaki, ko kin kula da rashin jituwar dake tsakanin Yaya Imran da Najib kuwa?"

Gabana ne ya faďi jin abinda tace, yaqe nayi nace "ban san komai ba kuma Najib bai taba nuna mini suna da matsala ba. Ina ga dai kawai hasashen ki ne, idan banda haka me zai shiga tsakanin Yaya Imran da Najib bayan yawan shekarun da suka ďauka tare ba'a taba jin kansu ba, wai ma me yasa kika ce haka?"

Tace "tun lokacin biki na kula da raunin mu'amala a tsakanin su, a yadda Yaya Imran da Najib suka taso komai nasu tare suke yi dole ne mutum yayi saurin fahimtar akwai rashin jituwa a tsakaninsu.

Ko kin san Najib bai taba zuwa gidan nan da sunan yazo wurin Yaya Imran a matsayin amininshi ba sai har idan ke ya kawo? Sannan shima Yaya Imran ďin baya yadda ya kaini gidanki sai dai yasa a kaini idan nayi magana sai yace ai suna yawan haďuwa da Najib shi yasa".


Nace "to Allah ya kyauta, amma ni ban san akwai wata matsala a tare dasu ba".

Da yamma Najib yazo ya ďaukeni. A hanyarmu ta komawa gida ne nake faďa mishi yadda muka yi da Mariya.

Tsaki yayi yace "abinda nayi ta gudu kenan Imran ya kasa fahimtata a lokacin, hatta da wasu daga cikin friends ďin mu sun zargi hakan. Abinda yasa bana zuwa gidan shi kuwa don bana so Mariya ta fahimci abinda kenan ne amma ina samun shi a office mu gaisa, Alhamdulillah tunda yanzu na samu ya sauko sosai fiye da da don har shi da kanshi yana kirana a waya sannan kuma yana kai mini ziyara a kasuwa".

Nace "to Allah ya kara haďa kanku, ai gara yayi hakuri don komai muqaddari ne daga Allah, babu wanda ya isa ya canja hukuncin shi, tun farko haka ya tsaro mana don haka dole mu karbi kaddara tunda yarda da ita yana ďaya daga cikin shika-shikan imani".

Daga haka bamu kara wata magana ba har muka isa gida.

UMMASGHAR.

MURADIN ZUCIYAWhere stories live. Discover now