BABI NA BAKWAI

1.3K 105 8
                                    

DEDICATED TO AUNTY SALIHA AA ZARIA

Na sake a cikin 'yanuwan, bani da lokacin kaina kullum muna cikin fita yawo da cousins ďina don haka matsalar da nake ciki bata fiye damuna ba, sai dai idan nazo kwanciya to fa bani da aiki sai tunani.

Sannan kullum wayata a rufe take sai zanyi waya nake buďewa to a lokacin ne zan yi ta ganin messages ďin Yaya Imran da yawa kuma bana karantawa nake gogesu.

Satina biyu a gombe, Alhamdulillah sosai damuwar da nake ciki ta ragu. Mun dawo daga gidan Adda Ma'u na tarar da Yaya Imran da Najib a gidan suna hira da Hajiya. A take gabana ya faďi don ban tsammaci ganin shi a daidai wannan lokacin ba.

"Sannunku da zuwa" nace musu sai dai Yaya Imran ko kallona bai yi ba yaci gaba da hira da Hajiya sai da Najib muka gaisa a raina nace kai ka jiyo.

Sai da Hajiya ta tashi ta bamu wuri sannan Yaya Imran ya kalleni cikin bacin rai yace "kinga abinda kika janyo mana ko?"

"Oh ni Maryam sarkin laifi, me kuma nayi?" nace nima da nawa bacin ran kwatankwacin wanda yake ciki don na fara gajiya da magana guda ďaya. Yaya ba zai barni naji da damuwata ba sai yayi ta kokarin kara mini wata.

Yace "to jiya Babanmu(Baba Ali) ya turawa Alhajinsu Najib sakon cewa su fito ya bashi ke. Kinga kuskuren ki ya janyowa Najib ďin ma tunda yana da wacce yake so. Yanzu dai ai kya hakura na samu Baba nayi mishi bayani".

Sai anan Najib yace "ni abinda yafi damuna yadda Alhaji ya ďauki maganar da girma don nayi duk iya yina domin ya fahimci yadda al'amarin yake amma yaki yarda, yace  shi ba karamin mutum bane an bamu 'ya ya kuma gode.

Yanzu haka zancen da nake yi miki yau naji suna shirin zuwa godiya shi da 'yan uwanshi. Don haka nake so Maryam ki warware mana wannan kullin, sanin kanki ne hakan bai dace ba, ke kaďai zaki iya kawo maslaha a cikin al'amarin nan idan har kin bayyana gaskiya ko kuma ki bari mu bayyana da kanmu".

Tunda ya fara magana ban ce kala ba sai yanzu nace "kana so ne na bijirewa iyayena naki zabin da suka yi mini? Idan har hakan kake nufi to abinda ba zan iya ba kenan, ni banga wani abin damun kai ba anan.

Musulunci bai haramta maka aurena ba kuma tunda ni ban ki ba banga dalilin ka na bijirewa ba, anyways ba laifinka bane tura maka ni akayi amma kasani cewa ni banyi bakin ciki da hakan ba illa ma godiya da nayi wa Allah don a tunani na bazaka taba wulakanta ni ba.

Sai dai zan iya baka shawara guda ďaya, babu dole a cikin al'amarin nan tunda kana ganin kyautar da akayi maka akwai cutarwa kana iya maida musu amma ni babu abinda zan iya yi muku don murna ma nake yi na samu mafita a saukake".

Najib yace "kin san ban isa nayi abinda kika ce ba don su Baba sun fi karfin komai a wurina, ina dai duba abin ne kin san hausawa sun ce ana barin halas ko don kunya, bana so na samu matsala da Imran, ban taba tunanin zan so macen daya nuna sha'awa ba ma bare kuma ke da nine tsanin taka soyayyarku.

Sannan kin sani ina da wacce zan aura, idan kuma don Mariya ne na yarda ni zan aureta na kular miki da ita kamar yadda kike buri, ni dai fatana ki bayyanawa su Baba gaskiyar halin da ake ciki".

Dariyar takaici nayi nace "fito fili kace Maryam bana son ki bazan iya auren ki ba amma ba ka tsaya kwane-kwane ba, to an faďa maka dama zan yi aurene don soyayya? Zan yi aurene don Allah da raya sunnar Manzonmu (SAW) sai kuma don farin cikin iyayena don nasan zamana a haka ba daďi zai yi musu ba. Idan kaso ka sake ni a ranar da aka kai ni gidanka Imran ne dai ba zan aura ba idan yaso yayi biyu babu ukun lala".

Cikin matukar fushi Yaya Imran yace "ba taimakon Mariya kike son yi ba cutar da ita zaki yi don na faďa na sake faďa ke kaďai na tanadarwa zuciyata da ma komai nawa, duk bacin ran da Mariya zata yi a gidana ke kika janyo mata don bazan taba bata farin cikin da kike son na bata ba".

Nima cikin nawa fushin nace "ni kuma ka rike a ranka duk abinda ya samu Mariya bazan taba yafe maka ba, zan iya yin komai dominta kamar yadda nasan idan itace a matsayina hakan zata yi.

Aurenka ne nace bana yi ko dole ne, kada ka sake zuwa mini da maganar soyayya, idan dai zamu yi zumunci muyi idan kuma bazaka yi dani ba duk ďaya". Na tashi na shige ďaki na barsu a wurin.

Don takaicina a ranar suka juya Kano basu bari sun kwana ba kamar yadda suka yi niyya, babu yadda Hajiya bata yi ba su hakura sai da safe sun tafi don dare yayi amma suka ki.

Ba karamin tashin hankali na shiga ba bayan tafiyarsu, yanzu kuma haka rayuwata zata yi ta walagigi na kare da auren Najib. Duk da bana son shi yana da mutunci a idona bai cancanci abinda nayi mishi ba, to shi kuma Yaya Imran fa? Duk sadda na bata mishi rai na bar samun farin ciki kenan don kwana nake yi kuka har sai na bashi hakuri mun daidaita. Oh Allah ka kawo mini ďauki don abin nema yake yi yafi karfina.

Mun yi waya da Mariya take sanar mini Yaya Imran ya samu aiki a AKTH kuma ya sayi mota. Nace "lallai, kice ina yi mishi murna, abin yayi kyau ga amarya mai kafa huďu kafin me kafa biyu ta zo".

Dariya tayi tace "wai yaushe zaki dawo ne? Kun fa fara lectures". Nace "In Sha Allahu jibi zan taho. Tsohuwar nan ce ta hanani tahowa, ita a son ranta ma nayi aure anan kin san so suka yi na amincewa Farouq".

Tace "kai ai Hajiya da rigima take, to kiyi yaya da Najib ďin?" Nace "ai ban yarda ba, kin san ni duk kwalisar shi da ake faďa ba burge ni yake yi ba don kuwa he's not my type, ya fiye rawar kai da yawa ga shegen kallon matan tsiya".

Kyalkyalewa tayi da dariya jin abinda nace tace "Maryam kenan, ni dai sai kin dawo, don Allah ki dawo jibin fa wallahi bana jin daďin gidan nan babu ke a ciki". Nace mata "In Sha Allahu ina nan tahowa" daga haka muka yi sallama.

Na turawa Yaya Imran message, abinda kawai na rubuta shine "congrats, naji abin arziki, Allah ya sanya alkhairi". Ina tura mishi na koma na kwanta, babu jimawa reply ďin shi ya shigo inda yake cewa "hmm Fakra kenan, ba abinda nake son ji kenan ba daga gareki. Komai zan samu is nothing idan har ban same ki ba".

Lumshe idanuna nayi ina tuno irin son da muke yiwa juna, tausayinmu ne ya kamani. Yaya Imran bai cancanci abubuwan da nake yi mishi ba. Ji nake yi kamar na fasa hakurin na barwa Mariya. Nayi sauri na kori shaiďan don nasan idan na biyewa zuciyata bazan iya yin abinda nayi niyya ba.

UMMASGHAR.

MURADIN ZUCIYAحيث تعيش القصص. اكتشف الآن