next page

1.3K 42 2
                                    

©Exզʊɨsɨtɛ Oռʟɨռɛ Wʀɨtɛʀs.
🎯🎯🎯🎯🎯🎯🎯
       🎯🎯🎯🎯🎯
             🎯🎯🎯
                 🎯🎯

KADDARA KO SAKACI❓

Wʀɨttɛռ ɮʏ: Hʊssaɨռa Nasɨʀ Uɮaռɖɨʏa.

Tɦɨs քaɢɛ ɢօɛs tօ: Zaɨռaɮ(Rɛɖ ɮʊttɛʀʄʟʏ) & ċաt sɨs Fatɨʍa Nasɨʀ Uɮaռɖɨʏa, աɨsɦ ʊ ɮօtɦ tɦɛ ɮɛst ɨռ ʟɨʄɛ.

Second 2 d last page

   8⃣6⃣ ➡ 9⃣0⃣

       Wasɦɛɢaʀɨ, daddy na tashi daga office gidan yayanshi Alh.Ridwan ya zarce ya sanar dashi abin da kenan,nan ya hau sababi "ba dai sun zabi aje kotun ba ai shikenan za'a gani mu dasu wazai ji kunya, yanzu bari na kira wani dan abokina barr.Imran sunanshi, muji procedures inda ya kamata mubi nan ya ciro waya ya kira Imran ya fara masa bayani Imran yace yana kusa da gidan bari yazo dan maganar tafi karfin waya.

Cikin minti goma sai ga barr. ya karaso suka gaisa sannan akayi masa bayanin komai ,ya sauke ajiyar zuciya yace"a gsky wannan maganar ba karama bace kuma baxan so ku kaita kotu ba  suma sunyi kuskuren kin binku a hankali amma bakomai ku bani address in gidan mahaifin Zayyad in idan na basu shawara suka dauka toh ba zanccn shiga kotu in sunyi taurin kai sunki bayarwa toh sai a shigar da kara" daddy da Alh .Imran sunyi na'am da shawarar barr.Imran  dun haka suka bar komai a hannunsa,yayi musu sallama ya tafi.

       Bayan yaje gida yayi wanka yaci abinci ya huta sai ya nufi gidansu Zayyad,cikin sa'a ya tarar da Abban Zayyad dashi Zayyad in sai dai Ammi da Nabila basa gida,bayan sun gaisa ya gabatar musu da kanshi da kuma abunda ke tafe dashi sam Abba yace sai an shiga kotun amma baza'a bada saki ba tunda mijin nason matarsa, shi kam Zayyad yasan bashi da gsky dan haka yace ma Abba gara kawai ya saketa ai ba ita kadai ce mace ba, anan ya rubuta saki  uku yaba barr.Imran shi kuma ya kaima daddy.

       Tun ranar da Nafisa ta daura ido aka barr.Imran Allah ya jarrabeta da sonsa haka shima a nasa bangaren jira kawai yake ta gama iddar ta ya gabatar mata da bukatarshi.

          Bayan wata uku da sati daya.

         Kasa daurewa tayi a yau ta kudiri niyar karbar number barr.wurin daddynta dan haka ta nufi parlor daddy ta shiga da sallamarta daddyn ya amsa yana zaune hannunsa rike da newspaper yana Karantawa, gaishesa da tayi yasa ya dago yana dubanta ya amsa sannan "ya akayi Nafisan daddy kinada matsala ne?"
"Eh daddy aron wayarka zaka ban in kira frnd ina babu kudi a nawa"
"Toh ai gara in baki kudi kiyi recharging zai fi"
"Eh amma ka fara bani wayar daddy i want 2 speak 2 her urgently" ya ciro kudi da wayar ya mika mata,cikin zumudi ta karba ta masa godia ta nufi dakinta ta kira barr da wayar daddy yana picking yace"Assalamu'allaikum Alh. an wuni lfy?" Nafisa ta amsa "wa'allaikassalam" sai kuma tayi shiru, jin tayi shiru sai ya dauka bataji sai yace "hello kina jina" sai da ya maimaita wurin sau uku sannan tace "eh Nafisa ce nace bara na kira mu gaisa"
"Toh ngd da zumunci dan Allah ko zaki kirani da numbernki dan nima na riqa kira muna gaisawa"
"Toh zan kira"
"Yanzu fa nake nufi, ngd ina jiran kiran" ya katse kiran. Kwashe number tayi zuwa wayarta tayi saving sannan ta maida ma daddy wayarshi bayan tayi deleting sunan barr. daga call log,sannan ta kira barr kamar yadda ya bukata.

  Tun daga ranar suka hau soyayya ba kama hannu yaro ko dayaushe suna kan waya indai yana office sai dai in yana da case ne basa yi, kullum dare bayan Anisa tayi bacci Nafisa kan kira sai ya lallaba ya koma dakinshi suyita waya gashi lokacin cikin Anisa ya shiga wata takwas,yau da gobe sai Allah tun bata san yana haka ba har ta gane a kan idonta ya kan fita zuwa waya duk daukarshi bacci take, ita dai bata nuna masa tasan abunda yake duk da abun yana matukar bakanta mata rai rokon Allah take ranar da Nafisa zata kira bayanan ta dauka. Allah ko ya amsa roqonta yau Imran na toilet Nafisa ta kira akayi sa'a Anisa ta farka ta hango wayar na haske(a silent take) da hanzari ta dauko wayar ta nufi parlor lkcn har kiran ya kusa katsewa tayi picking, Nafisa tace "hello hubby"................

  Sai mun hadu a next page kuma last page ISA.

Hussnah~ubandiya🍭
     Luv u all👏🏼

KADDARA KO SAKACI?حيث تعيش القصص. اكتشف الآن