next page

1.2K 60 3
                                    

🎯🎯🎯🎯🎯🎯🎯
       🎯🎯🎯🎯🎯
               🎯🎯🎯
                    🎯🎯

    KADDARA KO SAKACI❓

Written by:Hussaina Nasir Ubandiya.

        3⃣1⃣ ➡ 3⃣5⃣

  A yau result insu Nafisa ya fito na second semester u.g 3, anyi withdrawing Nafisa daga university innalillahi wa'inna illaihir raji'un hauka ne kawai batayi ba amma kuka dai ihu ba irin da batayi ba, tunaninta taya xata fara fada ma iyayenta wannan mummunar labari bayan tasan irin burin dasuka ci akanta sai a lokacin ta kara nadama da tsanar kanta ( darasi gare mu mata, mu sani bawa lecturers kanmu bashi ne abun yi ba mu kare mutuncinmu tare da na addininmu, ba duka lecturers suka taru suka zama daya ba in wani ya neme ki yabaki free marks wani ko kallonki bazayyi ba daga lkcn da kika fara bin lecturers zaki kasance bakya iya karatu  sai dogara da wani sannan kin maida kanki karuwa akan karatun da bazaki je lahira dashi ba kin take fadin Allah baki tsoron haduwarki dashi, dun Allah mu kula, sannan Allah ka kare dukkan musulmi daga aikata zina masuyi Allah ya shirye su dan alfarmar Annabi Muhammad (s.a.w).
   Sati daya da faruwan haka amma har lokacin Nafisa na skul ta kasa komawa gida, bata da aikin da yawuce kuka,tunani haka dai frnds inta ke sata gaba da lallashi ta zama topic of discussion abunda ma yafi daga hankalinta shine cewar da wasu keyi wai zubar da cikinta uku a skul, a dalilin haka ta yanke shawarar komawa gida.

    Ta iso garin minna da misalin karfe shida na yamma,ta tafi gida cike da tunani iri iri. Kowa yayi mamakin dawowarta dan basufi two weeks da resuming ba, ko da iyayen suka tambayi dalilin zuwan nata tace bata da lfy . Washegari daddy yace ta shirya ya kaita hospital kafin yaje office amma taqi, ta bukaci ya bata kudin zataje zuwa anjima haka kuwa akayi ya bata, da fitanta ta nufi chemist ta hado maganin typhoid nd maleria ta koma gida, a haka har ta kai three weeks a gida.

   Hausawa dai sukace komai nisan dare gari zai waye toh bari dai mugani. Fitowar daddy daga masjid bayan sallar magrib wani makwabcinsu ya tare shi da magana "Alh.Faruk barka dai"
"Ah Alh.Illiyas an yini lfy?ya iyali?"
"lfy lau iyali kam duk suna lfy,ashe kuma abunda ya faru kenan wlh banda labari sai jiya da Hafiz ya dawo yake sanar mini gashi muna ta haduwa ban jajanta maka ba" (Hafiz  a ABU yake shima)
" ban tari numfashin kaba Alh.Illiyas amma ko kadan ban fahimci inda zancen ka ya nufa ba"
"batun koro Nafisa daga makaranta nake nufi"
"wata Nafisan?"
"yar wajenka mana"
"aka kora daga skul? Ba dai tawa Nafisan ba dan ita jiya satin ta uku a gida ba lfy"
"subhanAllah Allah ya bata sauki, dun Allah kayi hkr Alh. Ina ganin nine banji da kyau ba amma bari in kira shi Hafiz in inji" ya ciro wayar tare da dialling number dansa yasa a handsfree " Assalamu'allaikum Abba"
"Wa'allaikassalam, Hafiz me kace dani game da Nafisan Alh.Faruk?"
"nace anyi withdrawing inta daga skul wani abunne ya faru abba?"
"a'a sai dai na shigo gidan" suka aje wayan. Alh Illiyas ne yace "Alh. mai zai hana kaje ka tuntube ita yarinyar dan she might be fooling u"
"hakane ngd" sukayi musabaha kowa ya kama hanyar gidansa, ran daddy a bace duk da bai ji daga bakin Nafisar ba.

Daddy ne ya shigo a fusace,ko amsa sannu da zuwan da mummy keyi mai bai yiba sai ma ce mata yake ina..................

  Toh sai ku cigaba da kasancewa tare dani dan yanzu za'a fara KADDARA KO SAKACI❓.

Kuyi hkr da wannan ba yawa,amma gobe zanyi mai yawa ISA.



Hussnah~Ubandiya🍭
   Luv u all👏🏼

KADDARA KO SAKACI?Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang