next page

1.2K 52 1
                                    

©Exquisite Online Writers.
  🎯🎯🎯🎯🎯🎯🎯
        🎯🎯🎯🎯🎯
              🎯🎯🎯
                  🎯🎯

KADDARA KO SAKACI❓

Written by: Hussaina Nasir Ubandiya.

   5⃣1⃣ ➡ 5⃣5⃣

Gidan Imran.

Horn Imran yayi gate man ya bude masa ya shiga yace ma mai gadin kar ya rufe dan yanzu zai sake fita, a daidai kofar da zata sada ka da cikin gidan yayi parking ya ce ma Anisa ta shiga daga ciki yana zuwa ya tada motar ya fice daga gidan Yahuza suya yaje ya sayi kaji da drinks sannan ya nufi gida.
Yana shiga upstairs ya haura ya shiga dakinsa ya ajiye kayan hannunsa ya fada toilet bayan ya fito yayi shafa'i da wutiri ya nufi dakin Anisa da shirinsa na barci "Assalamu'allaiki"
"Wa'allaikassalam sannu da shigowa"
"yauwa amaryar yaya na barki ke daya ko? yanzu kin daina kukan?" rufe fuska tayi da tafin hannun ta tana murmushi ta gyada kai alamar eh "ai yafi miki amma kina ta ma mutane kuka har da wani kara rungume Mami kina fadin ke baki zuwa" ya karashe kamar mai shagwaba, Anisa dai dariya kawai take ciki2 sannan tace "ji yaya kamar yana wurin"
"kika ce me?"
"bance komai ba yaya"
"oya jeki dauro alwalla kizo muyi sallah" nan ta mike tayo alwalla suka gabatar da sallar nafila bayan sun sallame ya dafa kanta tare da yi mata addu'oi daga bisani yayi mata tambayoyi game da addini ta amsa ya jawo ledar da ya shigo da ita ya gabatar musu sukaci suka sha sannan ta bude wardrobe ta dau nightie inta ta je bathroom ta saka tare da kuskure bakinta ta fito shima ya shiga ya wanke bakin nasa, koda ya fito ya tarar har ta kwanta yace "oh matar yaya baki san baida kyau kwanciya immediately after eating ba? atleast ki samu ko da 15mnt a zaune koma kiyi strolling daga nan zuwa parlor kije ki dawo 10tyms dan irin haka shi ke kawo tumbi saboda abunda kikaci bai yi digesting ba kika kwanta sai ya taru a tumbi...... bata bari ya karasa ba ta tashi "ai yaya wlh bana son tumbi kuwa"
"kina tara tumbi nima zan samo yar yarinya mara tumbi na aura" Anisa dai bata ce komai ba sai dariyar da tayi daga haka suka ta strolling na tsawon 20mnt sannan suka kwanta yana rungume da ita a haka har barci mai dadi yayi awon gaba dasu. Amarya da ango asuba ta gari.

  Karfe biyar na asuba Imran ya tashi ya shiga toilet ya dauro alwalla sannan yazo yana tashin Anisa, ta gyara kwanciya tana fadin "Mami  yanzun nan fa na kwanta kikara duba tym lokacin sallah bai yi ba fa" murmushi Imran yayi sannan ya kira sunanta cikin kunnen ta ba shiri ta mike sai lokacin ta tuna ba gidan maminta take ba kunya ya kamata kar yaya yace tanada magagin barci, ta shige dan yin alwalla shi kuma ya tafi masjid bayan ya dawo suka koma barci, karfe 8:00am karar wayarshi ya tashe shi Haydar ne ya sanar dashi yana waje ya sauka ya bude mishi lokacin Anisa ta shiga wanka, Imran ne yace "Haydar wai kai wani irin mutum ne me kazo yi tun da farar safiyar nan bayan kasan ina da amarya inace ni ba haka nayi maka ba" Haydar ya bata rai na wasa yace "maida wukar mallam ba dan Khadija da ta matsa sai na kawo ma amarya abun kari da ka ganni gidanka"(Khadija matar Haydar kenan)
"Allah sarki kace amarya na godia sosai"fadin Imran yana kokarin hawa stairs, Haydar ya jawo shi ya dawo "lallai ango kasha kamshi jiya kawai kaga yanda ka sauya sai wani kyalli goshinka keyi ina ga an kwan biyu" girgiza kai Imran yayi yace "kai dai sai dai muyita nema maka shiriyar ubangiji dan kayi specialising a sharri ni nayi sama inka fita ka rufe mana kofa da kyau" Haydar ya fice yana dariyar shakiyanci yayinda Imran ya dau abincin ya kai dinning,kai tsaye dakinshi ya tafi yayi wanka ya shiga dakin Anisa cikin shirinshi bayan sun gaisa suka sauko zuwa dinning area Anisa tayi serving insu suna ci ne ya mata bayanin Khadija, bayan sun kammala ya dau key ya tafi gidan iyayenshi.

    Shirye shirye ake ta duka bangaren........


Hussnah~Ubandiya🍭
  Luv u all👏🏼

KADDARA KO SAKACI?Where stories live. Discover now