next page

1.8K 85 1
                                    

🎯🎯🎯🎯🎯🎯🎯
        🎯🎯🎯🎯🎯
                🎯🎯🎯
                      🎯🎯

KADDARA KO SAKACI❓

Written by:Hussaina Nasir Ubandiya

      1⃣6⃣ ➡ 2⃣0⃣

  3 days later

   Nafisa ce ta fito cikin shirinta tsaf ta nufi parlorn daddynsu inda tafi tsammanin ganin mummy. Da sallamarta ta shiga cikin sa'a ta tarar dasu a tare suna kallon T.V.C news sallamarta suka amsa tare da maida hankalinsu gun da take ta durkusa ta sanar dasu zata gidan Aisha, daddy ne ya dubeta cikin sigar wasa yace "a haka za'a tafi ganin dan hannu rabbana? Ba dan leda" murmushi tayi "toh ai daddy ba kudi a hannuna ne"
"a'a kice kin kasa baki isa haihuwar ba kenan ga wannan kya biya boutique kisamar ma baby kaya" nan tayi godia ta fice.

Kai tsaye monday up town boutique ta nufa ta siya kayan baby masu kyau guda uku sannan ta fito jiran abun hawa, ta fi 20mnt bata samu ba, a hankali naga yayo reverse zuwa inda Nafisa take cikin motar shi kirar combatable pontiac yana ta horn tayi kamar bata san da ita yake ba, karshe ma bar masa gun tayi shi kuwa saurayin ganin haka yasa ya fito da zummar zuwa wurinta.
  
Saurayi ne dan kimanin shekaru ashirin da bakwai,fari dogo mara kauri yanada kyau dai2 gwargwado yana sanye da bakin jeans trouser da farin polo shirt kafarsa sanye da prada, Zayyad kenan dan Alh.Ahmad chief of staff na Niger state su biyu iyayensu suka haifa dashi da kanwarsa Nabila suna zaune a go'vt house a nan minna currently a banker in guarantee trust bank(G.T.B) bansan ya zan misalta muku halin Zayyad ba dan fir'auna a zuci Musa a fili dan kuwa Zayyad na shaye2 sai dai banda abokan yinnasa ba wanda ya san da haka inda Zayyad ya burgeni baya harkan mata hasalima tun bayan soyayyar da yayi a sec skul bai kara tun karar wata 'ya mace da sunan so ba sai yau da Allah ya hadashi da Nafisa.

Kai tsaye wurin Nafisa ya nufa "Assalamu'alaiki" kamar ba zata amsa ba tuna muhimmancin sallamar yasa ta amsa "wa'allaikassalam"
"mun yini lfy"
"lfy" ta amsa masa "da farko ina mai baki hkr aka tsaida ki danayi a titi duk da nasan ba mutunci bane, bakomai nake bukata a gun ki ba illah digits inki in yaso mayi magana a waya ina ganin zaifi"
"eyyah sai ya kasance kuma ba nida wayar ya za'ayi kenan"
"ai ba danni zaki bada number ba sai dan darajar Allah da manzon tsira (s.a.w)" sanin darajar wa'inda ya hadata dasu yasa ta bashi, sai ga napep ta tare ta shige yayinda Zayyad ke kokarin tambayar adress in ta.

Ta shiga gidan Aisha parlor ta shiga da sallamarta, Aisha ce zaune a kujera 3 seaters tana breastfeeding babynta yayinda Sadeeq yayi crossing hannun a shouldern Aisha, sunyi matukar burgeta taji ina ma ace itace tunawa da  burin mahaifanta yasa tayi saurin kauda wannan tunanin. Bayan sun gaisa da Sadeeq ya fita ya basu wuri, nan suka hau hira inda Nafisa kema Aisha korafin kin sanar mata ta haihu da tayi, Aisha ta bata hkr tare da fada mata dalilinta nayin hakan daga nan suka cigaba da hira sai bayan la'asar ta bar gidan.

🎯🎯🎯🎯🎯🎯🎯🎯🎯

Fitowar Imran daga court kenan kasancewar yana da case agabansa da aka fara saurara a yau, wayarsa dake a cikin aljihu ta fara ringing cirota yayi tare da picking ya kara a kunnen sa ,Haj.Rabi ce ta sanar dashi cewar tana nemarsa da hanzari ya nufi motarsa ya tayar dan hankalinshi yayi matukar tashi dalili kuwa shine Haj.Rabi bata kiransa idan ya tafi aiki sannan bai san dalilin kiran ba.
  Cikin mintunan da baxa su wuce 20 ba ya isa gida,part in Hajiyar tasa ya nufa ya tarar da ita a parlor ya karasa inda take da sallamar sa ya zauna   "haj. sannu da gida "
"sannu dan albarka ya aikin?"
"Alhamdulillah"
Duk sukayi shiru ba wanda ya kara mgn na wasu lkc, Imran ne ya katse shirun da fadin "
Haj. kina nema na"
"dama ba wani abu bane yasa na kiraka sai dan in maka albishir mai dadi" Imran kuwa cikin zakuwa yace "ina jinki"
"Zaka iya tuna Anisa?"
"Anisa yar marigayi kawu Abubakar?
"yauwa dan albarka ka ganeta"
"wani abun ne yasa meta haj.?" ta gyra zamanta "ba abunda ya same ta sai alheri na hanga na hango naga ba wacce ta dace da kai sai ita ma'ana ina son ka auri Anisa" ya dago cikin kaduwa yana kallon mahaifiyar tasa sannan yace "Haj. ce miki akayi ina sonta ko ita tana sona bama wannan ba tun rasuwar kawu da Mami (mahaifiyar Anisa) ta tafi da ita kaduna ban kara sanya ta a ido ba shekaru biyar kenan Haj.
"nasan da haka Imran amma nace ka aure ta ko kana son nuna min bansan abunda nake bane?"
"a'a Haj. ai bai kai can ba indai dan aure ne na amince Allah ya tabbatar mana da alherinsa"
"Ameen dan albarka Allah ya kare ka daga sharrin abun qi ya baku zuri'a dayyaba, yanzu kaga sai in kira Mamin naku in sanar mata in yaso sai ta sanar da Anisan daga bisani iyayenku maxa su shiga.
"toh Haj. bara na shiga ciki.  Ta amsa da toh tana kara sa masa albarka.



Hussnah~Ubandiya🍭
   Luv u all👏🏼

KADDARA KO SAKACI?Where stories live. Discover now