next page

1.3K 65 2
                                    

©Exquisite online writers
🎯🎯🎯🎯🎯🎯🎯
       🎯🎯🎯🎯🎯
               🎯🎯🎯
                   🎯🎯

  KADDARA KO SAKACI❓

Written by: Hussaina Nasir Ubandiya.

      4⃣1⃣ ➡ 4⃣5⃣

  Abban Imran ne da mahaifiyarsa zaune a parlor suna hira, haj. Rabi ta numfasa sannan tace " Abban Imran nace ba mai zai hana ka nemawa Imran auren Anisa"
"shi Imran inne yace yana son Anisan?"
"A'a dacewar hakan kawai na gani kuma har mun zanta da ita Mamin Anisan ta nuna jin dadinta game da lamarin"
"hakan yayi sai dai kinyi gaugawar sanar da ita, kafin nan ya kamata ki tuntubi shi Imran in ko akwai wacce yake so"
" in dai dan Imran ne mun riga mun gama maganar har ya amince, wato ta danka kawai kake baka tambaya ko ita Anisan nada wanda take so ba" murmushi yayi tare da kallon hajiyar cikin sigar wasa "kinsan indai da Imran a magana bana bin ta kowa sai na gama da nashi"
"ai gara ka canza hali domin kara na da dadi"
"hakane kuma, kira min Imran a waya dan in kara jaddada masa batun da kaina" Haj. Rabi na shirin kiransa sai gashi ya shigo da sallamarsa ya gaida iyayen nasa duk suka amsa, Abba ne yace " dan halak kaqi ambato yanzu nake cewa mahaifiyarka ta kira min kai sai gaka"
"shigowata kenan nace bara na fara gaidaku ina fatan dai lfy Abba"
"ah lfy lau batun yar uwarka da kukayi da mahaifiyarka,ina son kasan da sanin nan da 3 weeks za'a daura aure tare da biki da kuma tarewa" Imran ne ya dago yana kallon Abban nasa in shock "3 weeks fa kace abba hanzarin me akeyi haka?" Haj. tace "toh me za'a tsaya jira kanada muhalli batun yau ba ga aiki kanayi, yanzu dai zaka bada kudin lefe da sauran abubuwan al'ada da ake gudanarwa kafin aure"
"a'a basai ya bada komai ba sadaki kawai nake bukata daga wurinsa, in banda abinki auren tsoka daya a miya kike masa batun kawo kudi? toh dun wa nake neman? ki zauna kiyi calculating kudin duk da ake bukata sai ki bani bill"
"nagode Abba Allah ya kara girma" Haj. ta amsa da Ameen Allah ya maka Albarka.

          *⃣*⃣

   Tana shiga daki ta fada gado ta ci gaba da rera kuka gwanin tausayi, sai da ta gaji dan kanta tayi shiru kasancewar ba mai lallashi a karshe ta janyo wayarta ta kira kawarta Hajara ringing uku ta dauka "hello Naffy ya kike?" cikin sheshekar kuka Nafisa tace "Hajara ba lfy"
"subhanAllah mai ya faru?"
"su daddy sun samu lbrn an koreni daga skul Hajara suna fushi dani sosai" cike da mamaki Hajara tace "daman baki fada ba duk zamanki a gida? haba kamar ba yar zamani ba kamata yayi daga komawarki ki fada musu ki tsara musu magana yanda zasu ga sam baki da laifi su dauka KADDARAce ta fada miki amma yanzu zasu dauka SAKACInki ne kawai , yanzu ya ake ciki?
" wlh na rasa mafita kinsan lkcn da iyayen Zayyad suka zo daddy ya ci musu mutunci gashi yace in fidda miji ya bani 3days in ba haka ba zan bar mishi gida, tunani na taya Zayyad zai tunkari iyayensa da batun su dawo gidanmu nema masa aurena a yanzu kuma bana sauraran kowa bayan Zayyad" ta karashe cikin matsanancin kukan da yafi na da.
"Allah sarki kiyi hakuri ki kuma mika ma Allah dukkan lamarinki tare da nemar zabin mafi alheri sannan da safe ki tabbatar kin basu hakuri"
"nagode sosai Hajara Allah ya bar zumunci sai da safe.

        Washegari Nafisa taje gaida iyayenta duk sun amsa mata sai dai ba wanda ya kalle inda take a cikinsu koda ta fara basu hkr dakatar da ita daddy yayi yace "bama bukatar hkrn da zaki bamu sai dai ina miki  tuni da batun turo magabatan shi yaron da kike so, na kara miki sati akan kwana ukun da nace a baya duk ranar da suka yanke hukuncin zuwa ki sanar dani dan in sanar ma yan uwa" ta amsa da toh daddy bata bar wurin ba har sai da mummynta ta bukaci ta wuce ta dada basu hkr daga bisani ta tafi dakinta. Ta yanke shawarar kiran Zayyad, koda ta kira ya dauka ta sanar mishi duk abunda kenan tana kuka, ya lallashe ta tare da assuring nata zai turo iyayensa kafin lokacin da daddy ya dibar mata.

  Toh ko ya Zayyad zai kare da iyayensa idan suka ji zancen komawa gidansu Nafisa nemawa dannasu aurenta?

Godiya ta musamman ga yan group ina na gode da addu'arku Alhamdulillah naji sauki sosai, Allah ya bar zumunci, baxan gaji da mika dumbin godiyata a gareki ba Anty Ummiee Jaafar da duka members in Exquisite online writers Allah kara mana basira mai amfani. Da kuma dimples novels sannan Mmn Shukra&Hajar novels.

  Hussnah~Ubandiya🍭
        Luv u all👏🏼

KADDARA KO SAKACI?Where stories live. Discover now