next page

1.5K 48 0
                                    

Exզʊɨsɨtɛ Oռʟɨռɛ Wʀɨtɛrs.
🎯 🎯🎯🎯🎯🎯🎯
🎯🎯🎯🎯🎯
🎯🎯🎯
🎯🎯

KADDARA KO SAKACI❓

Written by: Hussaina Nasir Ubandiya.

Tɦɨs քaɢɛ ɢօɛs tօ ʍʏ aɖօʀaɮʟɛ, sʊքɛʀɨօʀ ʍʊʍ Mʀs Nasɨʀ Uɮaռɖɨʏa 2 ʍɛ ʊ aʀɛ ɖa ɮɛst ʍʊʍ ɛʋɛʀ . Aʟʟaɦ's ҡɦaɨʀ aռɖ ռօ օʀ ɮɛ ʊքօռ ʊ ռօա aռɖ aʟաaʏs.

8⃣1⃣ ➡ 8⃣5⃣

Bayan tafiyar Zayyad daddy ya bukaci ganin mummy da Nafisa, bayan sun zo,daddy ya fara magana "mijinki ya sameni da zancen komawarki kuma a ganina kin samu sauki sosai ko akwai inda ke maki ciwo?" Shiru Nafisa tayi
"Baki ji daddynku na magana bane?" Sai a lokacin tace Dun Allah kuyi hkr amma bazan koma gidan sa b.....
"Dakata hakanan inace zabinki ne kika aura bar kina da bakin cewa bazaki koma gidansa ba? Kinyi kadan aurenku mutu ka raba"
Cikin kuka Nafisa keba daddy hakuri amma KO sauraranta yaki,mummy ne tace" haba daddynsu ai ka bari muji dalilinta ko"
"Ba wani dalilinta da Zan tsaya ji dole tabi mijinta su koma anjima" mummy ta kalli Nafisa tace jeki dakina ki jirani, sannan ta koma kan daddy tana ta lallabashi amma fir ya dage sai ta koma,nan ran mummy ya baci tace "Bari in fada maka indai har dalilin Nafisa na kin son komawa mai karfi ne toh ba inda zata koma"
"Amina ni kike gayama magana akan 'yar banzan yarinyan can?"
"Wlhy ni kam ban haifi 'yar banza kuma ina kan baka na kadaiji na gayamaka" ta wuce fuu daddy ya bita da kallon mamaki dan tunda suke basu taba samun sabanin ra'ayi har haka ba, duk abunda yace toh ya zauna amma yau sai gashi akan nafisa tana nuna mai bai isa ba.

Ko da mommy ta shiga dakin ta tarar da nafisa tana kuka, sai tace"share hawayenki wannan Karon ina tare dake in har zaki gayamin haqiqanin abunda ke faruwa nayi alqawarin magance shi" ta qarashe zancen tare da tallabo kafadar Nafisa, Nafisa ta tsagaita da kukan sannan ta fara sanarda mahaifiyar duk abunda kenan tun daga ranar da ya fara zuwa Mata a buge har izuwa ranar da ta samu miscarriage, Mummy ta numfasa sannan tace"lallai wannan da anyi makiri ga ladabi da fara'a kamar mutumin arziki amma na banza,kinga illar kin bin iyaye kenan da ace kin tsaya kinyi karatu fisabilillahi kin kammala na tabbata baza ayi miki aure ba tare da an bincike mijin ba, gashi yanzu wa gari ya waya ace aure wata uku da satittika za'a raba shi mu gode ma Allah da yasa cikin ya zube da mum had a iri da mashayi ba fata ba da yazo yayi gado" Nafisa bata Kara cewa komai ba sai kukan da take rizga "yi shiru ki daina kuka ada ina daukar abun amatsayin SAKACInki yaja miki yanzu nayi realizing KADDARAce wadda tana kan ko wani dan adam,yanzu abunyi shine bara naje wurin mamar Aisha muyi shawarar yadda zamu bullo ma lamarin tunda daddynku bazai sa muna Kai ba amma lamarin na maza ne" ta tashi ta dau mayafinta ta fito zuwa parlorn daddy dan nemar izini "Zan shiga gidan Maman Aisha"
"Amina zo ki zauna" ba musu ta samu wuri ta zauna sannan ya Fara magana "nayi nazari bayan tafiyarki ciki na gane ban kyauta ba ina Neman gafararki tunda nike da ke baki taba min gardama ba, wannan ma nasan kin hango abunda zai cutar da yar mu ne shiyasa kika dage"
"Komai ya wuce daddynsu nima ka yafe min"
"Toh ngd yar aljanna ta gaya miki dalilin Nata?""eh ta fada min" nan shima ta fada mishi, "ikon Allah a gsky munyi kuskure Amina ko Fushi da rashin sanya ma Nafisa albarka da mukayi na iya haddasa Mata rashin jin dadin aure, yanzu abunyi anan zamu je gidan iyayensa anjima dukanmu in yaso gashi gata sai asan abunyi aure kam an gamashi Inshaa Allahu" daganan suka cigaba da jimamin al'amarin bayan sun Kira Nafisa sun sanar Mata duk sun yafe Mata.

Bayan sallar isha'i daddy ya kira Zayyad a waya cewa kar yazo su zasu kawo ta sannan ya tambayeshi ko abbansa na gari yace eh, suka dunguma zuwa gidan.

Bayan an gaisa an kawo musu drinks daddyn Nafisa ya Fara magana "nasan zakuji mamakin ganinmu alhalin dazu nace Zayyad yaje ya tafi da matarsa,sai dai bayan tafiyarsa na tuntunbi ita yarinyar ta kuma nuna batada ra'ayin komawa gidan Zayyad bi-ma'ana raba auren take so ayi"
"Ban fahimci a raba auren ba Alh. Faruk wani abunne ya faru" Abban Zayyad ya tambaya
"Eh kaji2 abunda ya faru nan ya zayyane musu komai kafin ya dire Abban Zayyad ya dakatar dashi cikin bacin rai "wani irin magana kake Alh.Faruk shekararmu 27 da Zayyad bai taba shaye2 sai yau zaku zo muna da wani zance haka in raba auren kuke so ba sai kun masa sharri ba"
"Da girmana kake tsammanin zanma Zayyad sharri? in kashe auren 'yata haka kawai in samu ribar me? Fadin daddyn Nafisa, Abban Zayyad yace "inda ba kasa nan ake gardaman kokawa Zayyad abunda sukace gskya ne?" Ba tsoron Allah Zayyad yace karya Nafisa tai mishi sannan ya kara da fadin ina son matata bazan saket...... Ammin shine ta katseshi"yazama dole ka Saki yarinyan can tunda basu San mutunci ba tun farko na fada ba mutanen arziki bane"
"Dakata haj.Sadiya wannan magana ta maza ne ki daina sa baki bazai yiyu kiyita aibantamu agabanmu dan cin fuska ba" fadin mummy kenan,"tunda Wanda ikon saakin ke hannunsa yace yana son matarsa toh baza'a bada takardar ba danni duk abunda dana keso nike masa"inji daddyn Zayyad, "haka kace Alh.Ahmad? idan bai bada cikin sauki ba kotu zata tursasashi sannan kowa yasan halin da yake ciki"
"Daga nan har kotun qoli ku Kaimu"
Daddy da mummy da Nafisa suka tashi sannan daddy yace"haka kace toh mu zuba" daga haka suka fice zuwa motarsu, acikin motar ne Nafisa ke basu hkr"daddy mummy dan Allah kuyi hkr duk nina janyo muku wanan wulakancin" suka amsa da bakomai Nafisa komai mukaddari ne daga Allah.......

Hussnah~ubandiya🍭
Luv u all👏🏼

KADDARA KO SAKACI?Onde histórias criam vida. Descubra agora