next page

1.4K 65 0
                                    

Exզʊɨsɨtɛ Oռʟɨռɛ Wʀɨtɛʀs.
🎯🎯🎯🎯🎯🎯🎯
      🎯🎯🎯🎯🎯
           🎯🎯🎯
               🎯🎯

KADDARA KO SAKACI❓

Wʀɨttɛռ ɮʏ: Hʊssaɨռa Nasɨʀ  Uɮaռɖɨʏa.

    Oh Allah send ur mercy upon all my known & uknown ċօʍʍɛռtatօʀ s,ʄaċɨʟɨtatօʀs& ʄaռs of dis novel.
   Of paramount important 2 me is Haʝɨa  Raҡɨʏa  Aɮɖʊʟҡaʀɨʍ Laʄɛռɛ , pls readers allow me 2 introduce d sun dat let me see 2ru its lights, she was a shining bright object in my heart dat always push me 2 continue writting. At dis juncture i've a package of so many sweet quantity of tnk u Haʝɨa , u av been so much for words 2 explain. Please Hajia accept this as a mini honour 4rum me.
HAT OFF 4 ALL MY FANS 
HAT OFF 4 ALL MY FAMILY
HAT OFF FOR SPECIAL U
Once again,HATS OFF 4 HAJIYA RAKIYA.

  6⃣6⃣ ➡ 7⃣0⃣

A gurguje.

Bayan wata uku.

Imran ne da Anisa suka fito cikin shiri zasu je gidansu Imran, yau Anisa zata fara fita sai murna take bakinnan yaki rufuwa, imran ne yace "matar yaya wannan murna haka kamar wadda zata fita daga prison?"
"wlh yaya ba haka bane ban taba yɨռ three months ban fita ba gashi in ka fita ba abokn hira sai tv, so dayawa nikan gaji da kallo gashi ka hanani chatting"
"in banda abinki bakiyi kina buduwar ba sai da kikayi aure? ai mami ta burgeni da ta hanaki"
"nadai ji koma meye mu tafi lokaci na tafiya" daga haka suka karisa suka shiga mota suka tafi.
  Suna shiga suka tarar da Haj. tana kallo hajiia ta fara fadin "wa nake gani kamar 'yata lalle marhabin da gudu Anisa taje ta rungume haj. Imran kuwa gaisheta yayi ya samu gu ya zauna yace "ai kin dagata haka ku gaisa ko" sai a lokacin Anisa ta zame kasa ta gaida haj. Haj. takara janyota ta aza kanta bisa kafadanta, Imran ne yace "haj. Abba ko na gida?"
"bayanan da safen nan ya tafi kontagora"
"Allah dawo dashi lfy" haj. da Anisa suka amsa da ameen" daga nan suka cigaba da hira har haj. ke cema Imran yakamata Anisa taje Kd wurin mami, Imran  yace "na dauka ko sai tayi 6month" caraf Anisa ta amshe mgnr "a'a yaya ina laifin kace jibi ko haj.?
Haj. tace bazaki jibi ba kibari koda next week lokacin kin shirya da kyau"
"toh shikenan hajiata Allah ya kaimu,nan suka cigaba da hira kiran sallar la'asar ne yasa Imran tashi ya tafi masjid bai dawo ba sai bayan magrib ,sukayi sallama da haj. suka nufi gidan Haydar.
Kiran Haydar yayi yace "gamu a waje" sai ya katse wayar ba'ayi minti biyu ba Haydar ya bude suka shiga, Haydar ne ya fara kiran Khadija "wifey2 zoga amarya fa" sai ga Khadija ta fito daga kitchen tana goge hannu"ah an gama muna rowar amaryan ne barrister? Imran bai ce komai ba sai murmushin da yake,baya sun gaggaisa Khadija ta koma kitchen ta fara fito da abinci tana jerawa a dinning Haydar ya dakatar da ita "wifey ki kawo nan zaifi" toh kawai tace ta fara kwaso warmers ɨռ   da duk wani abu da zasu bukata sanan tace dasu bismillah duk suka sauko Khadija ta dau plate ta zuba Nata da Haydar tasa spoons biyu,a day an plate in tasa pepper soup na kayan ciki,ta tura ma Anisa saura nan itama tayi serving Imran a plate daban Nata daban sabanin su Khadija dake ci a plate daya, su Khadija naci suna feeding junansu Imran na satar kallonsu bai San lokacin da ya Kai ma Anisa spoon a baki ba, kauda Kai tayi taki amsa tace "yaya meye haka KO kunya baka ji a gidan mutane muke fa"
"Wai bakiga yanda masu gidan keyI bane? dun Allah basu burge kiba?" duk magannan nan a hankali suke yinshi sai dai basu San su Haydar na jinsu ba sai dariyansu kawai suka ji, Khadija tace "barrister akwai son soyewa amma baka Bari matar taka ta koyo" dariya kawai sukeyi har ita Anisan, Imran ya tsagaita DA dariyar yace "Khadija Ina zata koyo?" Khadija tace kasan bakomai iyaye ke koya ma 'ya'yansu a dangane da zamantakewar aure ba dan acewarsu kan yaran yanzu a waye yake, toh abun dubawa anan tayaya kan zai waye? Kaga na daya interaction da frnds most especially wa'inda ke social media zakaga idan sun zauna in one way or d other zasu sako topic in aure a hirarsu kowaccensu zata fadi yadda zatayima mijinta kaga kuwa zasu karu da juna, sannan karatun novels yana taimakawa sosai amma wasu mutane sukan mishi mummunar fahimta sukan ce yana bata tarbiyan yara Wanda kwata2 ba hakan bane, so dayawa zakaga yariyan dabata taba karanta novel ta lalace while mai karantawa Tana a natse,sbd me ? SBD a novels akwai moral lessons na 1) a koda yaushe akan Nuna illar shirka wato zuwa wurin boka.
2)muhimmancin Kai martabarki gidan miji.
3)muhimmancin hakuri a rayuwar yauDA kulum.
4)biyayya ga iyaye, e.t.c idan nace in tsaya zayyane maka duka zamu kwana bamu gama ba barrister" Imran ya numfasa sannan yace "duk magananki gsky ne sai dai Ina mamakin yanda kikasan duk wainnan abubuwa" Haydar yace "ba abun mamaki bane idan kayi la'akari DA kasancewarta ma'abuciyar karatun littafi DA kuma na waya, ai ni ba abunda zance DA novels writers sai  fatan alheri" Anisa tace "toh yaya baza kabari Anty Khadija ta tura min WhatsApp in ba?"
"Kajiki DA wata irin tambaya ai ba watsapp kadai zata tura miki ba har groups insu nake so ta bada numberki ayi adding" nan Anisa taba Khadija wayar ta tura Mata ta Xender bayan anyi duk abubuwan DA suka dace tayi adding inta a group in wata namesake inta dayake itama admin ce a  Nօʋɛʟs aռɖ ċօօҡɨռɢ ʍɛtɦօɖs, saռռaռ ta ɮaɖa ռʊʍɮɛʀ ta aҡaʏɨ aɖɖɨռɢ a Uʍʍɛɛ Jaʄaʀ ռօʋɛʟs ɖa Dɨʍքʟɛs ɖa ҡʊʍa Mʍռ Sɦʊҡʀa aռɖ Haʝaʀ ռօʋɛʟs . naռ Iʍʀaռ DA Anisa suka yita zuba Mata godia sannan suka tafi.

Baʀɨ ʍʊ ʟɛҡօ ɢɨɖaռsʊ Zaʏʏaɖ ɖa Naʄɨsa .

A ċɨҡɨռ wata ukun da Nafisa tayi a gidan Zayyad sunyi shine cikin so da kyautatawa juna, har lokacin Nafisa bata da masaniyar Zayyad na shaye2 sbd kullum dare bayan sun biya ma juna bukata yakan koma dakinsa yasha dan tun suna sabon aure ya sanar da ita akwai aikin da yakanyi in dare yayi,bata kawo komai a ranta ba Dan tasan shi banker ne. Sai dai hausawa kance a jure zuwa rafi wataran an fasa tulun , karfe 7:30pm Zayyad kan dawo gida sai dai gashi yau har 11:45 bai dawo ba, hankalin Nafisa ya Kai matuka wurin tashi Tana ta kiran wayarsa amma hat ta tsinke ba'a dagawa,karshe nan parlor ta kwanta Tana tunani har barci ya saceta.
A bangaren Zayyad kuwa tun a office sukayi gardama da wani colleague inshi mai suna Andrew, inda Andrew yace ma Zayyad in yasha wani hadi bazai iya tashi ba,shikuma Zayyad yace ba abunda zai fi karfin kanshi nan dai Andrew ya ce aje gidanshi ya hada ma Zayyad, koda suka je ya hada yabashi tunda yasha ya kasa ko daga kafa bacci ya kwasheshi da sai 11:00pm Andrew ya tashe shi amma still baya iya komai sai sambatu da layi, bazai ma iya driving ba ga Andrew bai San gidanshi ba can dubara yazo mishi ya bude brief case inshi ko zai ga complementary card in Zayyad cikin sa'a kuwa ya gani nan yakamashi ya kaishi mota da taimakon address inda ke a complementary card in ya kaishi gida ya fito yayi knocking a gate baba ya tambaya "waye?" Cikin hausar da bata Nuna ba Andrew yace "mai gida naki na kawo" baba ya maimata Kalmar mai gida kuma KO mai ya sameshi da tunani ya karasa ya bude nan Andrew ya mika ma baba mai gadi Zayyad yace zai tafi da motar sbd bazai samu abun hawa ba yanzu, Baba ya kamashi har zuwa kofar da zata sada ka da parlor cikin muryar maye Zayyad yace baba barni a nan na gode, baba ya koma gate Zayyad kuwa knocking ya Fara kamar hauka,cikin baccinta taji Ana knocking a tsorace ta tashi ta Kai duba zuwa ga wall clock inda ke a parlor 12:05 ta gani ta karasa zuwa bakin kofar tace "waye?" Cikin muryar maye yace UBANKI ne zaki bude ko kuwa ?ga Rana na dukan mutum (kunji Dan Maye dare yake Kira Rana 😳). A sanyaye taje ta bude kofar bai bari ta gama ba ya turo da karfi ji kake Bam ya buge ta a goshI,wani razanannen ihu ta sake shi kuwa saman rug ya zube ya cigaba da bacci ba sallar magrib balle isha'i, tashi tayi hannunta dafe da gosh I ta wuce daki ta fada gado Tana ta kuka a takaice ranar dai batayi barci ba.

  Washegari.........

 

Hʊssaiռaɦ~Uɮaռɖɨʏa🍭
    Lʊʋ ʊ aʟʟ👏🏼

KADDARA KO SAKACI?Where stories live. Discover now