next page

1.4K 73 3
                                    

🎯🎯🎯🎯🎯🎯🎯
        🎯🎯🎯🎯🎯
                🎯🎯🎯
                     🎯🎯

KADDRA KO SAKACI❓

Written by:Hussaina Nasir Ubandiya

         2⃣6⃣ ➡ 3⃣ 0⃣


  A haka su Nafisa suka samu hutun mid-semester suka tattara suka tafi gida. Daren ranar kasa barci Nafisa tayi sbd fargabar yadda zata sanar da iyayenta batun Zayyad, ba dan tana sonshi ba da kuma alkawarin auren da ta mishi ba da ta fasa ta jira har ta gama makarantan. Kwana tayi tana practising yadda zata yi magana idan taje wurin iyayen nata.  Sai gabanin 4:am barci ya dauke ta ba tare da saninta ba, ba ita ta tashi ba sai past 7 da sauri ta fada toilet ta dauro alwalla, bayan ta idar da sallah ta koma toilet tayo wanka ta nufi kitchine dan taya mummy hada break sabanin da da in ta dawo bata fitowa sai 11:00am. Bayan sun kammala cin abinci ne take sanar da iyayenta akwai muhimmiyar maganar da take son sanar musu, nan mummy ta kore duka kannin Nafisa, daddy ne yace " muna jinki Nafisar daddy"
"dan Allah kar ku fassara maganar da zan muku da cewa ina son bijire muku ko baku kunya a'a sai dai bukatar abun ne ya taso..... Daddy ne ya katseta da fadin "ban fahimce zancen ki ba go straight 2 d point dear"
"um3 dama2" dama me? Mummy ta tambaya.
"dama akwai wani dake sona shine yake nemar izinin turo iyayensa.....
"will u shut up ur dirty mouth kin san abunda kike fada kuwa? da bakinki aure a yanzu kina 300level?" fadin dady kenan.
"daddy wlh auren nake so a yanzu besides ma ai zan cigaba koda nayi auren"
"rufe mana baki shashashar banza wadda bata san ciwon kanta ba kin zauna yana ta rudarki da kalamun yaudara har ki iya ce mana aure kike so" fadin mummy cikin bacin rai.
"ki barni da ita Amina, tace ya turo iyayen nasa and get out of my sight.da sauri ta tashi ta bar parlon.
"daddynsu kana nufin auren zaka mata?"
"hauka nayi? Allah dai ya kawo iyayen yaron lfy. Nan mummy keta kara zuga shi

Tana shiga daki ta dau waya ta kira Zayyad.
  "hello angel"
"hi dear guess what"
"common babe tell me, u knw am nt gud at guessing"
"ok dady yace ka turo iyayenka"
"really angel? gaskiya nafi kowa farin ciki a yau, bari in sanar dasu Abba, ya katse kiran.

Da sallamarsa ya shiga parlorn Abba da Ammi da Nabila ne zaune suna hira ya samu gefen daddynshi ya zauna da ka dube shi zaka gane yana cikin farin ciki, Abba ne yace "Zayyad da alama kana cikin farin ciki  a gaya mana muma mu taya ka farin cikin" Zayyad ya fara sosa kai yana inda2 alamar jin kunya "dama iyayen wacce nake so suka ce in turo magabata na"
"brother Aunty Nafisa? (ta san ta har sun taba gaisawa a waya)
"ke yima mutane shiru manya na magana kina interfering kamar ban hanaki ba" daga nan Nabila bata kara mgn ba.
" 'yar gidan waye?"
Abba ya tambaya
"sunan mahaifinta Alh.Umar Faruk Idris suna zaune a nan tudun fulani ne"
"ok zan sa Sani P.A ya bincika min gidan sai inyi ma uncles inka magana"
"toh ngd Abba"
"Ammin yara baki ce komai ba"
" toh me zan ce bayan Allah ya sanya alheri"  su duka suka amsa Ameen.

Bayan kwana uku,

Iyayen Zayyad suka nufi gidansu Nafisa. Bayan an gaisa an kawo musu drinks sun sha, Daddy ne ya fara magana " ku ne iyayen yaron dake son 'yata ko?" suka amsa "Eh"
"toh madalla, mgn ta gskya ba nace ya turo ku dan ku nema masa aure bane a'a, sai dan in fada muku ku ja kunnen danku ya rabu da 'yata ban tashi aurar da ita a yanzu ba sai ta gama skul idan yaga yana iya jira fallillahil hamdu idan bazai iya jira ba fyn akwai mata dayawa a gari, nasan duk dan halal yana jin maganar iyayensa shiyasa na bi ta wurinku, iya  abunda zan fada kenan da fatan ban bata muku rai ba" Alh. Musa ne yayi karfin halin amsa shi " baka bata muna rai ba 'yar kace sai yanda kayi da ita, ko ranmu ya baci ai danmu yaja mana"
"yauwa ngd da kuka fahimce ni a gaida gida"

Bayan sun koma suka sanar ma Alh. Ahmad komai nan ranshi yayi mugun baci ya bawa 'yan uwan nasa hkr, sannan ya nufi shashen Ammi ya tarar tana waya bayan ta gamane tace "Abban Nabila lfy na ganka haka?" nan ya zayyana mata komai, itama ranta ya bace "ai Zayyad in zai zo ya same mu, ba jiran daxaiyi ko ita kaidai ta rage mace bazai aure ta ba"
" idan ya dawo ki fada masa cikin lumana karki tashi hankakinsa"
"au gudun bacin ransa kake bayan ko ma meye shi yaja ma kansa"
"na gama mgn karki tashi hankalin yaron nan da me kike so yaji?   Ya rasa masoyiyar sa" daga haka ya fice daga  dakin ya bar Ammi tana ta sababi ita daya.
Koda Zayyad ya dawo Ammi ta sanar masa ya nuna mata indai Nafisa ce ya barta amma yana fita ya kirata ya labarta mata abunda kenan, ta razana da jin abunda daddynta yayi nan taba Zayyad hkr shi kuma ya tabbatar mata zai jira har ta gama.


Hussnah~Ubandiya🍭
    Luv u all👏🏼

KADDARA KO SAKACI?Where stories live. Discover now