next page

1.3K 64 2
                                    

©Exquisite online writers.
🎯🎯🎯🎯🎯🎯🎯
        🎯🎯🎯🎯🎯
                🎯🎯🎯
                     🎯🎯

  KADDARA KO SAKACI❓

Written by:Hussaina Nasir Ubandiya.

      3⃣6⃣ ➡ 4⃣0⃣

Daddy ne ya shigo a fusace ko amsa sannu da zuwan da mummy keyi bai  ba sai ce mata yake "ina 'yar iskar yarinyar nan take?"
"wacce 'yar iska kuma"
"Nafisa mana"
"tana dakinta"
"kira min ita kar ta batan lokaci kuma"
Toh mummy tace ta nufi dakin Nafisa zuciyarta cike da tunanin ko mai Nafisa tayi wa daddynta yau har ya kirata da 'yar iska? koma dai meye naji idan na kirata. Koda ta shiga dakin ta tarar da Nafisa na waya da Zayyad, ta sanar mata sakon kiran daddy ta ajiye wayar tabi bayan mummy.
   A tsaye suka tarar da daddy Nafisa ta durkusa tana fadin gani daddy yayinda mummy ta kasa zama ganin mijin nata atsaye. Daddy ne ya fara magana cikin bacin rai " ki gaya min gskyar abunda zan tambayeki kar ki kuskura ki min karya dan zancen duniya bata buya, korarki skul a kayi ko a'a?. Mummy da sai yanzu taji dalilin fushin maigidan nata sai da tayi matukar kaduwa dajin wannan maganar.
  Dum gaban Nafisa ya yanke ya fadi ta fara kuka tana fadin "dan Allah daddy kuyi hakuri ba laifina bane KADDARA ce" mummy ta katse ta da fadin "ba kuka aka kira ki kiyi mana ba ki amsa gsky ne ko a'a. Nafisa ta kara volume in kukanta tana gyada kai alamar eh, nan mummy ta yo kanta tana duka ta ko ina, da kyar daddy ya kwace ta  "Amina beating wil nt change anything but wil worsen d situation, nasan dama hakan zata faru tunda ta nuna mana aure take so"
"ai da ka barni na hallaka 'yar banza"
"ki barni da ita bata zabi wannan yaron akan karatunta ba? ya hure mata kunne ta daina karatu tasa soyayya a gaba, ta mayar dani shashasha a ko ina ina alfahari dake ashe watsa min kasa zakiyi, kin cuce kanki zakisa frnds, neighbours nd relatives suyi mana dariya u betrayed d trust i av in u. Nafisa dai bata ce komai ba sai kukan da takeyi kamar za'a cire ranta. Daddy ya cigaba da fadin " tunda aure kike zaba ya zama wajibi ki cewa saurayin naki ya fito, na baki 3 days idan ba haka  ba zaki bar min gidana" har ya kai kofar da zai sada sa da dakinsa ya juyo tare da nuna ta da yatsar sa "kar kiyi zaton zan dau wannan hasarar da kika min,na biya kudin registeration inki tun daga u.g1 har izuwa yanzu da kike u.g3 ga kudin provisions  da pocket money sannan sakamakon koroki zaki bani kiyi expecting zan dau hasara ni daya? Ina bazaiyu ba kudin aurenki kika bata, naira na daya bazai yi ciwon kai ba ban kuma amince ayi taron bikinki a gidana ba sai kije ki sanar da saurayin naki dan ya sani tun wuri. Ya juya zai bar wurin da sauri Nafisa ta riqo rigarsa daddy dan Allah kayi hakuri ka yafe min ya buge hannun nata ya fice,ta rarrafa zuwa wurin mummy tana kuka dan Allah mummy kuyi hakuri "ai Nafisa bamu kika yiwa ba kanki kikama bazaki fahimci hakan ba sai nan gaba zaki gane illar da kika yiwa future ki ko bakomai sunanki ya baci an kore ki daga skul , wai ma gayamin dalilinki na barin karatu har aka koro ki?
"wlh mummy KADDARA ce kawai ta fada min"
"rufe min baki har kinada karfin halin cemin KADDARAne, KADDARA KO SAKACIn kiba, ai shike nan ta faru ta kare in banda sakarci sai da kika kai 300l sannan aka kore ki kin yi hasara wlh, gata muka miki amma kikayi watsi da opportunitynki wasu na son karatun amma basu samu dama ba ke kin samu kin watsar , hmm baki san namiji ba kinyi karatun ya kika kare bare bakiyi ba, ba abunda zance illah duk abunda zai faru nan gaba ki kuka da kanki" ta tafi dakin mijinta ta bar Nafisa dake ta famar kuka.

A dakin kai da komo ta tarar daddy nayi ta karasa wurinsa tare da kamo hannunsa suka zauna a gefen gado "daddynsu da farko zan fara da jajanta mana tare da baka hakuri akan abunda Nafisa ta aikata kuma nayi na'am da dukkan hukuncinka a kanta sai dai batun miji kana ganin baza'a bincika halin yaron ba?" daga mata hannu daddy yayi "dakata Amina bazan bincika komai ba inace ita tace taji kuma ta gani ai shikenan" daga haka suka ci gaba da tattaunawa akan lamari.

Ina labarin Imran?


Sakon gaisuwa ga dukkan readers in KADDARA KO SAKACI❓

  Hussnah~Ubandiya🍭
    Luv u all👏🏼

KADDARA KO SAKACI?حيث تعيش القصص. اكتشف الآن