chapter 17

1 0 0
                                    

Washe gari Adyan na company Afnan ta sami shi. Yana amfanin da system ya dauka Isabel ce ta shigo ya ce "Isabel inform the chief accountant I want to see him now. "

Afnan ta ce is not Isabel is Afnan." Ta karaso wurin shi.

Da jin muyar ta yai saurin dago kansa dan tabbatar abinda kunnen sa su ka ji.

Ta sakan mai murmishi, ta zauna.
Ya daure fuska ya tambaye ta wa ya ba ki izinin shigo min office.
Kyawatatcen murmishi ta ma shi sannan ta ce "Morning my love."

"Out! Ya furta cikin bacin rai.

Ta ce "Haba mana is too early ranka ya fara bace wa. Daman na zo in ma jajen abinda ya faru da matar ka sannan..."

"Tashi ki fita kafin in sa security su fitar da ke." Ya katse ta

Afnan ta yi murmshi sannan ta ce"Haba mana ko ba komi ka tsaya ka saurare ni please."

Ya ce "Ba Abinda zan ji ki tashi ki fita."

Ta ce "Mi love ka san ina son ka I love you with all my heart, duk tsawon lokutan da muka ka bata za ka bar one mistake di na ya ruguza soyayar mu, dan Allah kayi hakuri na daina na ma alkwarin haka dan Allah,  an aura ma ita ba tare da ka san ko wacece ba amma ji abinda ta ma, na ji ina da a lot of boyfrends but you're the only person that my heart love, want and wish, also duk rishin ji na I will never give my pride and identity to someone excpect my husband.

Rai ba ce ya ce:"Daman haka duka mata ku ke, Afnan ba na son ki kuma ba zan so ki ba."

Afnan da jin haka nan ta ke kwala suka cika mata ido, zuciyar ta ta karye Baki daya ta na kallen shi shi kuma ya ki bari su hada idon dan ta san raunin sa hawayen ta.

Ya tuna da maganar Iman hakan yakara bata masa rai akan Afnan ya jawo telephone ya kira security ba tare da ya bari idon sa sun kalle ta ba.
Cikin murya kuka ta ce "Ad kar ma zuciyata haka, zuciyata kai kadai ta ke bida dan Allah ka so ni ka ba zuciyata abinda ta ke bida."

Jin an budai kofa ta goge hawayen fuskarta duk da sun ki tsayawa.

Yayi commanding din su da su fitar da ita.

She gazed at him with dismayed itace Ad zai kora. Bakin ta ya rufe ta kasa cewa uhfan sai dai kallon shi da ta ke yi shi kuma ya maida kan shi ga desktop. Da baya da baya ta ke taku har ta isa wurin kofa security ya  budai mata kofa. Ta tsaya ta rasa mi za ta ce mashi zuciyarta cike ta ke da ciwo bakin ciki da takaici.

security ya ce Hajiya ki fita.
Afnan ta juya da sauri ta fita.  Bata tsaya ba har sai da ta zo wurin motar ta ta shiga ciki ta ja motar da karfi ta bar compny, ba ta tsaya ko ina ba sai gidan su. Ta na shiga direct dakin Mummy ta nufa.

Mummy kuma na zaune bisa sofa ta na reserch da wayar ta Afnan ta shigo ciki tare da fadawa saman ta.
Mummy ta ce "Subahannallahi lafiya? Ta karsa Magana tare da aje wayar ta cire glass din ta aje sannan ta ce lafiya Afnan miyafaru?

Afnan cikin kuka ta ce "Mummy Ad ne."

Mummy tayi tsakin takaici ta ce ba na ce ki rabu dashi ba, shi kadai ne namiji da zaki ta faman binsa." Ta karasa maganar tare da cire ta daga jikin ta.

Ta cigaba; "Ba yayi aure ba, tin da yace bai san ki ki kyale shi ba na, ay bashi ka dai ba ne namiji a duniya kuma bashi ne autan maza ba.

Afnan cikin kuka ta ce "Mummy zuciyta zata fashe in ban aure shi ba, dan Allah Mummy."

Ta ce bai son ki ba sai ki kyale shi ba, ki na mace ke za ki bi shi ki na rokan sa, haba mana kar ki bada mata bana, ki na zubdawa kan ki kima.

Afnan ta ce "Ni ban damu ba, ni dai Ad na ke so kuma shi nake so na aura."
Ta karasa maganar tare da tashi ta bar dakin ta koma dakin ta.

KAZAFI Where stories live. Discover now