Chapter 5

2 0 0
                                    

Washegari suka hau hanyar kano da isowar su Mammy ta sa a ka tarbai su. Suka ci suka yi sallah sannan suma suka fara Shirin kamu.

Afeeya tin bayan azzahar suka tafi make up daga wurin make up suka wuce event center. A ka fara event din na masu kidin kwarya.

Sai gab da za agama ango ya shigo shi da abokan sa biyu suka yi hotuna wanda yau ne haduwar su ta biyu.

  Bayan sun gama hotunan abokan sa suka mata sallama shi ko gogan tamkar shine bako a wurin ta.

Bayan an dawo gida aka mai da yanda a kayi gida cike da mutane ana hadahada har Allah yayi gari ya kara wayewa a aka yi Shirin daurin aure. Yan bauchi suka karaso a ka daura auran tare da sadaki dubu dari biyar.

A wurin kowa ce mace ranar daurin auren ta rana ce mafi girman gaske ranar farin ciki ce amma banda Afeeya ji ta ke tamkar an kesta mata ashana da ta kona Dukkan farin ciki na rayuwar ta zama da mutumin da duk duniya ba wanda ta tsana sama da shi suna da gaba tin yarintar su.

Washe gari bayan an daura aure, da safe kafin su tafi mahaifiyar ta mata nasiha a kan ta kula da komi na mijin ta ganin sa hanci sa cin sa da Kuma shan sa.

Sannan ita rayuwar aure 70 percent zaman hakuri ne da kwada Kai 20 percent tausayi da kyautatawa sai 10 percent soyayya.

Umma mahaifiyar Mammy ita ma ta Kara a kan Abinda Mammy ta ce da na Kuma Aunty suwaiba Yaya ga Mahaifinta.

su Aunty yaanah da Adyan sai wasu kadan daga cikin family din su su ka kai ta gidanta wanda yake Bauchi.

Da isar su Bauchi gidan Hajiya a ka sauke su su ka shirya a ka tafi budan kai wadda hajiya ta shirya event din.

Anan ma sai da Hajiya ta tilastawa Adyan ya zo wurin. Haka ya zo wurin budan kan ba dan ran shi ya so ba.

Fuskaar nan a daure ba alamar fara’a tamkar ba ango ba.

Suka gama shagalin buda kai a ka wuce da Afeeya gidan ta. Wanda duk wainada suka zo ganin amarya sai sun Yi addu'ar Allah ya dora su a damshin Afeeya ba yanmatan ba ma masu auren ba Dan gudan ba Karamin haduwa yayi ba.

Tin da su ka shigo ciki Afeeya ta ke ma su kuka tare da rokan su da kar su tafi su bar ta cikin katon gidan nan ya ma za ayi a ce rai biyu za su yi rayuwa a babban gidan zai iya daukar rai goma zuwa 15.

Auty sa’ada yayar Mammy hakuri take bata.

Yusrah da Farha suma kan su kuka suke tin su na ba Afeeya hakuri har suma suka bi ta suka fara kuka.

Aunty sa’ada da kausar suka cigaba da bata hkr ganin bata da niyar dai na kukan Aunty sa’ada ta ce ku taso mu tafi dan ba zama za mu Yi ba a nanyanzu kun ga ango ya shigo.

Kausar ta ce na ma ji gidan tsit kusan kowa ya tafi. Ta karasa maganar tare da mike wa kowa ya mike. Afeeya ma ta mike.

Aunty sa’ada ta ce ina zaki Afeeya? Haba ki koma in Allah ya kai mu gobe za mu dawo.

Afeeya da kuka har da haaki ta ce:"Dan Allah  Aunty kausar ku kwana a nan.

Kausar ta bude baki tare da cewa:"Kwana rufa mana asiri chacha a masallaci ba da mu ba. Ki yi hkr zuwa gobe zaki saki jikin ki." Ku wuce mu tafi.

Aunty sa’ada ta ja su ka fita suka iske aunty Yanaah tare da wasu mata zaune a parlour.

Anuty Yaanah ta ce daman ku mu ke jira dare yayi.

Aunty sa’ada ta ce:"Eh dare yayi mu tafi.

Suka mike suma suka fita waje suka iske ango da abokan sa aunty yanaah da sa’ada suka musu bankwana suka tafi.

Adyan ya sallami abokan na sa ko ciki bai bari suka shigo ba.

Direct parlourn shi ya shiga ya aje ledojin da aka biyo shi ya dora kan sa Saman kan kujera tare da rintse idon sa.

KAZAFI Where stories live. Discover now