chapter 13

2 0 0
                                    

Da fitar ta ta ga gidan a turnike da hayaki. 

Ta zauna a parlour ta dau wayar ta ta kira Mammy suka gaisa Mammy ta tambaye ta ta sha magungunan.

Afeeya ta ce:"Eh Mammy amma Adyan  ya takura min a kan su."
Mammy ta ce:"Ni na sa shi dan na san halinki akan magani."
Afeeya ta ce:"Sannan Mammy da na yi hayakin na dinga tari Kamar rai na zai fita haka ma na wanka jiki na ya dinga kaikai."
Mammy ta ce:"Alhamadullilah lafiya ke nan in sha Allah za ki sa mu sauki inma ture a ka mik zai wargaje ko ma mi ne in sha Allah. Ki daure ki cigaba da magungunnan.
Toh Mammy sai da safe.
Allah kaimau.

Ta amsa da amin ta katse wayar ta koma, ta mike a hankali ta ra sa ina zata je ta kwana sama ko kasa, sai ta wuce sama ta yi Shirin bacci tayi addu'a ta kwanta sannan ta kwanta ba tare da bata lokaci ba ta yi bacci.

Washe gari ta tashi da yunwa ko Sallah ba ta yi ba ta shiga ktchen ta hada tea ta sha sannan ta koma sama ta yi Sallah ta kara koma wa bacci.

Sai after 10 ta tashi ta shiga ta yi wanka  ta shirya, ta varandar sama ta ga motar Adyan hakan na nufin yau ma bai fita wurin aiki ba.

Ta sauka kasa zata shiga kitchen din ta ji faduwar gaba ta yi addu'a ta mika wiya ga Allah ta shiga kitchen har ta gama hada breakfast ba abinda ya razanar da ita. Ta kaimai.

Ta na shiga ta gan shi zaune ya na anfani da wayar. Ta gaishe shi sannan ta aje mashi abinci.

Zata wuce ya ce ci abincin ki dawo.
Ta gama cin abincin tayi hani’an har da hamdallah dan rabon da ta samu natsuwa ta ci abinci har ta manta.

Ta koma ciki ya bata maganin ta sha sanann ya bata na ya haki ta yi kamar dai jiya ta na fara wa ta fara tari haka dai ta daure ta ida sannan ya bata na duka gidan ta yi hayakin a ko ina.

Ya fito ya mika mata na wanka da na tsarki ya ce in kin ga dama kar ki yi kan ki ka yi wa.

Ya koma parloun shi. Ta bishi da kallo har sai da ya shige sannan ta mike ta shiga dakin ta ta tube kayan ta ta shiga toilet ta dauko moda ta zuba maganin ta rufe ta shiga wanka. Yau ma dai kamar jiya ko a ce kaikain na yau ya ma fi na jiya.

Ta fito tayi karamin haukan ta kafin ta dawo dai dai. Ta maida kayan ta. ta fito ta koma sama.

Tana kwance a saman kujera ta na amfani da wayar ta Adyan ya karaso ciki ya ce "Ki sauko kasa Aunty Yaanah na jiran ki."

Afeeya daa jin sunnan Aunty Yaanah ta yi sauri ta tashi zaune farin ciki sosai cikin zuciyar ta. yaushe rabon da ta yi baki.

Ba bata lokaci ta mike tsaye ko tanka ma shi ba ta yi ba ta wuce, da sauri ta ke sauka daga staircase din tamkar wadda zata ga abin alajabi.

Ta sauko tare da karasawa wurin su dauke da fara’a a fuskarta "Aunty yaanah!!
Ta karasa ta rungumai ta.

Aunty yaanah itama ta rungumai ta. bayan wasu dakika su ka saki juna.
Aunty Yaanah Ina wuni, such surprise da kin fada min I will have cook special to you."

Aunty Yaanah ta yi dariya ta ce "Ni  ina ma jin hushin ki."

Da jin haka Afeeya ta dan yi sanyi.
Aunty yaanah ta cigaba "You are not well ba za ki kira ki fada mana ba sai dai mu ji a gari, ko kuma shi ke nan daga kin auri kanena relation din mu na baya ya chanza."

Afeeya ta kalli Adyan ke nan talata ciwon na ta ya ke yi, ta mai da kallon ta wurin Aunty Yaanah ta ce:"A’a ba haka bane, kuma na ma warke dan ciwo ne na kwana biyu."

Ta mike tsaye tare da ce wa bari na kawo ma ku drinks. Ta nufi hanyar kitchen da zumudin ta.

Bayan tashin Afeeya Aunty Yaanah ta ce Gaskiya Adyan  ba ka kyauta ba in  ba ta kira ta ce mana ba ta da lafiya kai ka fadi mana ji yanda ta rame duk ta yi kasusuwa gaskiya mu ba haka mu ka ba ka yar mu ba."

KAZAFI Where stories live. Discover now