CHAPTER 3

2 1 0
                                    


Da dare Nawfal ya zo gidan su Afeeya suna taadi ya fuskanci Afeeya ba ta ckin nitsuwa. Ya tambaye ta "Bebe kina lafiya?

Afeeya ta dubai shi sannan ta ce lafiyata qalau mi ka gani?

Ya ce:"Na ga yanayin ki ya chanza kamar baki jin dadi."

Afeeya ta sauke karamar ajiyar zuci ta ce:"Mi love wata Magana ce ta tsaya min a rai."

Ya tattaro dukka hankalin shi wurin ta ya tambaya wata maganace?

Ta ce "Ban sa ya za ka dau maganar ba abin da wasa yana nema ya Yu.dyan"My love I have never expected this. I'm thinking of changing this decision dan ba na son shi ba na kaunar sa."

Ganin yayi shiru bai ce komi ba ta ce my love ba ka ce ko mi t td ba in?

Ya furzar da huci tare da janye idon sa daga kan ta Dan Bai ta ba kawo kan sa haka ba;"bebe ban  da ta ce wa maganar wasiya ce kin ga ba yanda  zamu yi.

Kallon shi tayi cike da mamaki ta ce:"Wai kana nufin mu rabu daman za ka iya rabuwa da ni???
W
Ya ce:"Ko daya amma bebe ina so ki nutsu ki saurare ni..

Ta katse shi "Hakan ya nu na min daman ba ka so na."

Da sauri ya ce "Wlh ina son ki so na gaske amma ki saurare ni ki ji Dan Allah.

Babe wani lokacin rayuwa bata zo mana a yanda muke so na san bakay son sa ni ki ke so kuma nima ina son ki amma kar ki manta da ayar da ke cewa zaka so abu ya kasance sharri a garai ka ka ki abu kuma ya kasance Khairi a garai ka wallahu a’alamu wa antum la ta’alamu.

Sannan tun kafin a hallici ananbi Adam (AS) sai da a ka fara halitar al qalami ya rubuta dukkan abinda zai faru tin daga farkon duniyar har izuwa tashin alkiyama to kin ga in da ni ne mijin ki an rubuta haka kuma ba wanda ya isa ya chanza haka sai Allah idan kuma shine mijin ki ba wanda ya isa ya hana ki auran shi dan haka ki kwantar da hankalin ki ki dasa son shi a zuxiyar ki, wasiya ba abin wasa bane ke kan ki za ki so ki ga mahaifin ki na farin ciki duk da yana kwance cikin kasa.

Cikin murya san kuka ta ce:"Yanzu shike nan mun rabu."

Murmishi yayi Mai dauke da radadi ya ce ba mu rabu ba Munanan tare sai dai halakar mu ta rabu yanzu ke a matsayin kanwa ta ki ke ba wai matar da zan aura ba.

Ta dafa kanta cike da takaicin auran ta da Adyan. Ya ce Afeeya ki yi hkr, ba wai ki yi kuka ba. K yi hkr kuma ki yi addu'a Hakan ya kasance alkhairi a garai mu ba ki daya Dan Allah kar ki sa damuwa a ran ki.….

Shi ma idon shi cike da zafafan hawaye sai dai ya Yi kokarin rike su daga fita da ga idon sa ganin yan da Afeeya ta damu...

Bayan ta shigo ciki ba ta tsaya ko ina ba sai dakin su ta cire hijabin jikin ta ta wulla ta kasa sannan ta kwanta bisa gadon tare da dora bayan hannun ta bisa kan ta ta shiga tunanin yanda rayuwarta za ta kasance sai chan kuma ta tuna fadan su na karshe da Adyan wanda ya kasance rana ta uku da mutuwar mahaifin ta daga ranar ba ta kara sa shi a ido ba ko da sun je bauchi ba ta ganin shi ko kuma Idan su Hajiya sun zo Kano.

A bangaren Nawfal tin da ya koma gida ya kasa samun sukuni maganar auran Afeeya ta na ta mai yawo a zuciya ko Abincin dare ya kasa ci haka ya kwanta zuciyarsa cike da damuwa.

Washegari da safe ya shiga wurin mahaifiyar shi ya mata sallama zai tafi wurin aiki. Ta lura da yanayin sa ya chanza sai ba ta mai magana ba har sai  da ya dawo take tambayar shi mi ke damun sa ya ce mata lafiyar sa qalau da ta tilasta shi ya fadi mata abin da ke faruwa ita ma bata ji dadi ba ta ce kayi hkr Allah zai hada ka da wadda ta fita ita kuma Allah basu zaman lafya.

Bayan kwana biyu Alhaji sa’id da Alhaji Yakubu yaya ga Alhaji sa'id sai Alhaji mujittafa da Alhaji Amar mai dala yan’uwa ga marigayi. A ka taru a gidan su Afeeya a ka sa auran wata 3.

KAZAFI Where stories live. Discover now