Chapter 11

1 0 0
                                    

Adyan ya fito ya iske ta zaune ta na tunanin yanda zata Yi girkin. ya tambaya ina abinci na.

A ranta ta ce ba aikin da mutun ya iya sai ci.

Ta kalle shi ta re da marairaicewa ta ce "Ka ki yarda na ce ma kitchen din cen akwai mutane boye da na shiga yanzu karan plate da spoon na ji.
Ya kalle ta ya nufi hanyar ciki tare da ce wa biyo ni.

Ta tashi ta bi shi a baya suka shiga kitchen din ya duba ya duba sannan ya jiyo ya kalle ta ya ce ni ban ji komi ba.

Ta ce "Wallahi..."

Ya katse ta "Ba na san shirman banza."

Ya juya zai fita ta ce "Dan Allah ka tsaya a nan in dora abincin dan Allah." Ko kallo ba ta samu ba ya wuce.

Ya na fita taji an datse kofar ta firgita tare da kiran sunnan Allah ta yi hanyar kofar ta murda handle din ta ji a rufe ta kara jan kofar taji a rufe.

Sai ta koma kofar baya ta ja ita ma a rufe ta koma daya kofar ta fara bubbuga kofar ta na kiran Adyan da ya budai mata kofar, tana ta bubbuga kofar har ta fara kuka ta na neman dauki daga Allah.

Ta ga dai Adyan bai da niyar budai mata ta mike jikin ta na karkarwa ta dora tukunya ta budai fridge ta dauko kayan miya da dafaffen naman miya ta sa a tukunya ta soya sama sama sama ta sa seasonyngs da Meemaj spices ta zuba ruwa ta rufe tukunyar ta koma ta rabe jikin kofar ta na jiran Ruwan ya tafasa.

Kuka ta ke har da hakki ta na tsoran kar wani abu ya samai ta. Ruwan yana tafasa ta zuba macroni ta kara komawa wurin kofar ta kara knocking ta na kiran sunan sa ba ta san cewa ita kadai ke jin ihun kan ta Adyan ko alamun ta baya ji ta gaji ta zauna a kasan kofar ta na jiran abincin ya karasa.

Ta na nuna ta sa mai ita a warmer ta koma ta zauna a kofar tana kuka ta na neman dauki wurin Allah.

Chan ta ji an budai kofar. Da sauri ta tashi tsaye ta fashe da kuka tare da cewa "ba na son irin wannan abu miyasa za ka rufe ni ka san ina jin tsoran kitchen din dan mugun ta za ka rufe ni in ma abun mutuwa ya kashe ni ko wa ya huta."

Goshi ya dafe sannan ya saki ya rasa gane kan gadon ta kwana biyu kamar wata mai tabin hankali ya ce "Malama ba ni na rufe miki kofa ba."

Da sauri ta tambaye shi "Toh waye?

Bai bata amsa ba ya karasa kitchen din ya dauko plate da spoon zai zuba abinci ta ce ka fa di waye ya rufe kofar in ba kai ba ni dai kar ka kara min haka."

Adyan ya na daga kula ya ga ba abinci rai bace ya juyo ya kalle ta ya ce ",Zo nan.
Ta yi tsaye kamar gunki ya ce ba Magana nake miki ba.

Ta karaso kusa da shi ya tambaya minene haka.

Ta na kai idon ta saman kular ta ga ba abinci ta kalle shi ta kara kallon kula. Sai ta fashe da kuka ta re da cewa "Wayyo Allah na shiga uku wlh..

"Quite! ya Daka mata tsawa.

Ta ce:"Wlh na sa abincin..." Ta nufi wurin tukunyar da ta aje, ta budai zata ce mai ya duba ga tukunyar da ta dafa abincin da mamaki ta ganta a wanke.
A tsorace ta jefar da murfin tukunyar ya fadi kasa ta ja da baya ta cigaba da kuka.

Adyan ya fita ya bar kitchen ya koma parlour ya dau key din motar ya fita ya bar gidan.

Yana fita kitchen din ta biyo shi har parlourn shi zata shiga ya rufe kofar ya shiga ya dau key din mota ya fito ya rufe ta a cikin gidan ya wuce abin shi.

Ta dau wayar ta ta kira Mammy ta lbrt mata abin da ya faru ita ma Mammy na mamakin haka ta ce gobai zata turo mata da magunguna na sha dana hayaki duk sharrin da ke gidan da yarda Allah zai fita ta yi hakuri ta kwantar da hankalin ta sannan ta cigaba da addu'a.

KAZAFI Where stories live. Discover now