Chapter 1

5 2 0
                                    

Bismillahir rahamanir Rahim.

_____yar matashiyar mata wadda shekarun ta ba su gaza 20 ba zuwa 21 ta na zaune bisa kujerar asibiti ta daga kanta tana kallon sama idon ta a rufe jin alamun an tsaya akan ta hakan ya sa ta bude idanuwanta wanda suka mata nauyi, ta dubi wanda yake tsaye a kan ta.

Rai a bace mutumin ya fara mata fada: Dama haka ki ke ban sa ni ba? Duk salihancin ki da shiru shirun ki duk na banza ne ban sa ni ba? Mayaudariya ban sani ba?

Ta gyara zaman ta jkin ta ba karfi ta ce Yaya Adyan miyasa kake jifa na da munanan kalaman nan?

Saukar mari taji a fuskarta har sai da kan ta ya sara ta rike wurin tare da mamakin marin da ya mata ta na gani buji buji a idanuwanta.

Ya kwasa mata tsawa yi min shiru daman ke yar iskace ban san ni ba? Ya wulla mata takardar tare da tambayar ta cikin da ke jikin ki na waye?

Afeeya ta tambaya cikin rishin fahimta; Yaya Adyan ban gane ba, ciki??? wallahi ban…
Adyan ya katse ta; "Bin maza da auranki??

Mutanen da ke wurin suka tawo wurin su tare da ba Adyan hakuri. Cikin fushi ya fita daga reception din asibitin, mutanan suka jiyo kan Afeeya suna bata hakuri.

Bata saurare su ba ta bi Adyan din waje.  Ta karaso wurin motar zata bude kofar ya daga mata tsawa kar ki sake ki shigar min mota ki je chan wurin wanda ya miki cikin... ya ja motar shi ya wuce.

Zafafen hawaye suka saukar wa Afeeya ita kanta lamarin nan ya na bata mamaki taya take da ciki, ga abin takaicin wulakanta ta da yayi a bai nan nasi. Ta  fara tafiya  har wajen asibitin ta rasa ina zata je shin gidan ta zata koma ko gidan su mijin ga duk fadin gari ba in da ta sa ni haka ta cigaba da tafiya jikin ta ba karfi  ga jirin da ke daukar ta bata Ankara ba ta ji ta fadi a kasa.

A bangaren Adyan tuki yake amma ya kasa samun sukuni. Daman haka mata suke dukkan su mayaudara ne, Kamar Afeeya zata yi ciki ta kawo mashi gida, shi dai ya san ko sau daya bai taba muammala da ita ba balle a ce cikin na shi ne. Haka dai ya cigaba da maganganun zuci har ya karaso gida ran shi a bace.

A wurin Afeeya ta falka ta gan ta a gadon asibiti tare da drip a hannun ta. Ta dubi wurin da take. Likitan da ke zaune a office din ya tambaye ta ya jikin na ki?

A lokacin ta tuna da abinda ya faru wasu hawaye ne suka kara sauka bisa fuskarta.

Likitan ya tambaya "Fatan kina lfy mike damun ki?

Murya a shake ta ce:"Ba komi."
Dr ya ce "Toh shike nan, ya sunan ki?

"Safeeya." Ta amsa ba tare da ta dago kanta.

Ya Kara tambayar ta:"Safeeya fatan komi lfy dan kin suma a kan hanya mafarin ke nan na kawo ki asibiti na, ina iyayen ki?

Afeeya tace ba su nan?

"Toh su na ina, ina yan’uwanki?

Ta yi shiru sai chan kuma ta ce mai "Ban da kowa."

Dr yana tantamar ta, wacece ita? Miya samai ta?

Bayan ya gama aikin sa ya Kara duba ta ganin jikin na ta da Sauki ya cire mata drip din sannan ya ce wa Afeeya ta biyo shi.

Ta sauka daga kan gadon ta fara binshi a baya suka fito daga asibitin ya bude motar tare da ce mata ta shiga.

Ta kalle shi  tare da mai alamar tambaya.

Yayi murmishi ya ce "Safeeya ki saki jikin ki zan kai ki gidana ki cigaba da zama har zuwa lokacin da za ki koma wurin iyayen ki."

Aafeeya ta tuna da sakon da Adyan yay mata”Kar ki sake ki dawo min gida ki je ke da Allah." Hakan ya sa ta shiga cikin motar duk da hankalin ta bai kwanta ba.

Dr ya shiga motar suka bar asibitin zuwa gidan sa. Bayan ya shigo da motar ya shigo da ita cikin gidan na sa.

Dr yayi sallama matar gidan yar dattijuwa ta fito.
"Ahh Dr sannun da zuwa."
Ya amsa da "Yauwa."
Ta dubi Afeeya ta ce:"Dr bakuwa mu kayi?

Ya amsa da "Eh, a zuba mata abinci ta ci sannan ki kai ta dakin Afnan ta huta." Ya wuce ciki.

Dr Meenah da ta gama Karewa Afeeya kallo ta ce:"Yarinya ya sunan ki."
Afeeya ta amsa da "Safeeya."

Dr Meenah ta ce:"Safeeya sannun ki da zuwa samu wuri ki zauna bari a kawo miki abinci. Samu wuri ki zauna. Ta Kara da maganar tare da Yi mata nuni da ta zauna.

Ta kira mai aiki ta sa a ka kawo wa Afeeya abinci. Bayan ta fara ci ta tafi wurin mai gidan ta.

Ta iske shi shima yafara cin nasa abincin ta ce Dr ita wannan wace ce da dukkan alamu cikin damuwa ta ke.

Dr ya ce:"Eh amma bata fadi min abinda ke damun ta ba shiyasa na kawo ta nan har zuwa lokacin da zata dawo daidai." Ya labarta mata abinda ya faru.

Daga Dr Ibrahim da matar ta sa ba su san cewa Afeeya matar Muhammad Adyan ce ba sanan ba su san tana da ciki ba kasancewa cikin bai wani girma ba.

Afeeya tana kwance saman gado ta dora hannun ta bisa goshin ta idon ta a rufe tana tunanin lamarin nan taya zata fuskanci mahaifiyar ta da wannan lamarin mai daurin kai, Adyan mijin ta ne amma ba su taba hada shinfida ba sannan ita ba ta taba bayar da kanta da wani ba taya zata samu ciki?

Ta na cikin wannan tunanin taji karan buda kofa wa zata gani ta ga AFNAN.

Da sauri ta tashi zaune tamkar ta ga fatarwa. Ta kara budai idon ta dan tabbatar wa kan ta Afnan ce ko kuma gizo take mata.

Afnan ta karaso cike da kasaita ta Harari Afeeya sannan ta  fashe da dariya kafin ta ce:"Oh daman ke ce wada mahaifina ya taimaka? Ta kara wata dariya sannan ta ce "Ina mijin naki wanda ki ke takama da shi ya na ina ne?

Korarki yayi daga gidan sa? Hhhh da ni ki ke zance AFNAN IBRAHIM.

A lokacin safeeya ji ta yi dama ta niste cikin kasa sbd takaicin ganin Afnan, yau kaddarar ta ta kawo ta gidan ex din mijin ta.

Afnan tayi tsaki ta bar dakin...

Washe gari da safe tin kafin gari ya ida waye wa Afeeya ta bar gidan dan zamanta ba zai yu ba a gidan. Da ga gidan ta wuce tasha tana tunanin ina zata je ita dai ba zata koma garin su ba inma ta je mi zata ce wa mahaifiyar ta wa zai yarda da ita in har mijin ta bai harda da itaba.


Toh readers rate our novel KAZAFI
Ya kuke tunanin zai kasance?
Don’t forget to vote, react, or comment.

KAZAFI Where stories live. Discover now