Chapter 8

2 0 0
                                    


Ta kwanta tana kuka har bacci ya dauke ta ta manta da ta dora indomine.

Adyan daga parlourn sa ya ji kaurin abu na kone wa. "Ya Allah"  ya furta sannan ya mike tare da cewa wannan yariya na rasa mi zan mata.

Ya na shigo wa ciki ya ga kauri da sauri ya nufi kitchen wanda ya cika da hayaki da kauri tari ya fara yi ya isa wurin gas din ya kashe gas din sannan yabude kofar kitchen din da window din.

Ya juya yakoma dakin ta. Shinfidai ya ganta toilet ya shiga ya dauko ruwa ya zuba mata.

A gigice ta tashi ta na ganin shi tayi sauri ta mike sai kuka ta fara rokan sa da yayi hakuri

Ya ce "Wato dan na hukunta ki shine ki ke so ki babbabaka min gida?

Sai a lokacin ta tuna da indomine ta ce "Ka yi hakuri ay laifin ka ne."
Kee!!! Ni ki ke ce wa haka.

Ta ce'"Da baka murdai min hannu ba ay ba zan manta da ita."

"Zaki min shiru ko sai na farfasa miki baki."

Ta yi tsit. "Useless." Ya ce tare da wucew parlourn shi ya zauna tare da dora kan shi saman kujera. 

Ya tuna da maganar Daddy in dai ka ce za ka mikar da shi to ran ka ne zai ta fadi. Yayi tsaki ya mike ya koma dakin sa.

Afeeya fito ta shga kitchen din, ta karasa wurin tukunyar indomine har tayi baki ta koma kasan tukunyar.

Towel ta dauko ta maida saman sink ta budai fanfon ruwa, ta cika tukunyar da ruwa.

Ta rufe kitchen din da window ta koma daki dan yunwar ma ba ta ji.

Zata kawnta ta tuna da bata yi sallah ba. Ta shiga toilet tay alwalla ta  fito tayi Sallah ko kaya bata chanza ba ta kawnta.

Washe gari da fara Safiya ta kira Mammy, Mammy har ta san in dai Afeeya ta kira ta toh kara ta kawo mata.

Ta na karatun kuranin ta dagata ta daw kiran ta re da ce wa mi kuma ya kara miki?

"Mammy jiya daddare ya murdai min hannu har da ciwo ya ji min".

Mammy ta ce:"subahanallah garin ya mi ki ka mai dan na san ba jin Magana ki ke yi ba?

Ta tabe baki tare da cewa "Mammy shike nan kullun shi ke kan dai dai ni  ba dai dai ba."

Mammy ta ce:"’A'a Afeeya na san halin ki ne fadi min mi ki ka mai.
Afeeya ta lbrt wa mammy Abin da ya faru.

Mamamy ta ce laifin ki ne kin yi wauta dan bai yaba abincin ki ba ay ba kin ki zuwa ki gaishe da abokan sa ba gaskiya biki kyauta,sannan in banda shashanci irin naki mi zai sa ki rufe masa kofa haba afeeyya kar ki bani kunya ki na matsayin iya ta, zama ya gaji haka zo mu zauna zo mu saba, ki dauke shi a matsayin mijin ki ki kula da komai nashi, ki yi respecting din sa as your husband, I always told you zaman aure zaman hakuri out of 100 percent 70 percent hakuri 20 tausayi da kyautatawa sai 10 percent soyayya.

Ki harda ko kar ki harda Adyan yana sama dake ko da ba mijin ki ba ne ya girmai ki, Adyan ya fi ni hakki a kan ki, ya fi ni iko a kan ki, Adyan shi ne shugaban ki kuma jagoran ki ba yanda ki ka iya dole ki masa da’a da biyaya in har ki na son aljannah.

Afeeya ta ce:"Mammy shi ke nan sai ya ta cuta ta..."

Ta katse ta:"To in ya cuce ki kan sa yayi ma wa, shawara da zan baki ki kasance mai hakuri da kauda kai ko da an fito da Magana kar ya kasance ke ki ka cuce shi ya za mo ke a ka cuta. Dan haka daga yau in har jun samu sabani ki zauna ki ka inda ba daidai yake ba ki gyara ta ha ka dai zaki sa ni in yi alfahari da ke kin ji.
Ta amsa da "Toh."

Yauwa Allah muku albarka ya sa wa auran naku albarka.

Ta amsa da Amin sannan ta yanke kiran. Ta goge kwalal idon ta ta na tunanin yanda zata sa wannan bawan Allah cikin ranta har zuwa zuciyar ta wanda in yanzu za ace wa ta tsana duk duniyar na Adyan zata ce amma shi ne wai mijin ta.

KAZAFI Where stories live. Discover now