A raina nace 'Banda abin Abba ai daga lokacin da ka mutu to duk abinda ka bari ya zama na magada, shi kuma gado Allah da kansa ya raba shi babu kuwa mai sakeshi ba tare da Allah ya hukuntashi ba, kuma Abba ma ai duk yasan wannan kawai zafin ciwo....... "

Kakarinsa ne ya dawo dani daga tunanin da nake yi da zancen zuci, na ganshi yana ta fama a nan dai rai yayi halinsa bayan ya furta kalmar shahada kukana ne ya ankarar dasu Zayyad da Badrah suka shigo da gudu suna ganina ina kuka suma suka rusa nasu don sun gane abinda ya faru, na jawo mayafi na rufeshi. Bayan mun koma gida anan aka dasa wani sabon kukan, gaba dayanmu haka muka sashi a gaba muna tayi, na kira babban sakatarensa na tambayeshi ko ana binsa bashi sai ya shaida min cewa Abba kwata kwata baya cin bashi sai dai in na kamfani, nan take kuwa kafin ayi masa sutura sai dana biya duk bashin kamfani, sannan nazo muka yi masa wanka mukayi masa sutura aka je aka kai shi gidansa na gaskiya. Tun da aka yi mutuwar nan wadanda Abba yake bi bashi sukai ta kawowa ana ajiyewa, bayan komai ya lafa sai muka zauna dani da Umminmu nake gaya mata wasiyyar da Abba ya bari.

Tace "Tabbas nima munyi wannan maganar dashi ana igobe zai mutu."

Nace "Ai kuwa abinda ya fada ba zai taba yiwuwa ba domin ko mun ki ko mun so babu yadda za'ayi mu ci gadonsa don Allah bai ce haka ba, a cikin Suratul Ahzab Allah ya bayyana bambancin dan ciki da dan rana, dalilin da yasa aka hana kiran Zaidu bin Haris da Zaidu bin Muhammad da ake ce masa a da. Duk dawainiyar da aka yi damu tun daga kuruciya har zuwa girman mu abinda muka ci ma mun gode Allah ya saka da alkhairi"

Tace "Ni ba kowa nake ji ba irin Yasira don ita har yanzu bata san cewa bani na haifeta ba, idan taji wannan labari ban san yadda zataji a cikin zuciyarta ba watakila ma ta kasa jurewa!"

Nace "Kada ki damu Ummi da yardar Allah komai zai zo da sauki, kuma dama ai komai daren dadewa wata ran sai gaskiya ta fito, komai nisan dare gari zai waye."

Tace "To shikenan, amma ina neman wata 'yar alfarma a wajenka!"

Nace "Ki fadi ko meye Ummi in dai kece ba alfarma a tsakaninmu sai dai umarni, ko me zama ba zan taba daina ganinki a uwa ba"

Tace "Na yarda a raba gadon kamar yadda Allah ya umarta, amma bana son ka sanar da kowa a cikin su cewa an raba gado, ina so ka rike musu kawai tunda kasan kason kowa sai ka ajiye masa a wajen ka kafin zuwa wani lokaci"

Nace "Wannan ai mai sauki ne ki dauka ma kawai anyi abinda kika bukata"

Tace "To shikenan na gode Allah yayi maka albarka"

Mun je wajen wani babban malami ni da Ummi Badrah domin ya raba gadon sai ya bukaci ganin dukkanin magada, sai muka bashi uzurinmu da kyar ya amince, suka gabatar mai da duk wata dukiya da takardun kadarori da sauran duk wani abu da Abba ya bari. Aka hade komai guri daya aka yi jumilla sannan aka raba gida takwas Badrah ta dauki kashi daya a matsayin tumunin takaba, sannan aka sake hadewa waje daya sannan aka sake rabawa gida tara, ma'ana Zayyad da Dayyab da Zayyan da Rayyan kowanne ya dauki kaso biyu, sauran kaso dayan kuma shine na Shukrah. Aka yi abin a rubuce dalla dalla sannan aka bamu muka koma gida.

JAN JAGORANCIN GIDAN ABDUSSATTAR

Jagorancin gida yanzu ya koma hannuna ni nake da ikon zartarwa, sawa da hanawa, kullum taka tsantsan dina kada na tsallake iyaka, sannan wasicin Abba kullum yana raina.

Anci gaba da rayuwa kamar babu abinda ya faru don babu abinda ya sauya, kawai bambancin da da yanzu shine da akwai Abba yanzu kuma ya kaura, nayi kokari wajen ganin babu wanda ya yasa wani abu, Zayyad da Dayyab duk sun sauya halinsu abinda suke yi da na rashin da'a duk sun daina. Ni da Yasira kuma nayi kokari kullum sai na zuba kudina na albashi a cikin kudin cefanen gida don gudun cin dukiyar marayu. Gidanmu ya cigaba da tafiya kan tsari babu mai cewa mai gidan ya mutu sai wanda ya sani.

*BAYAN SHEKARA UKU*

BAYYANA SIRRINMU

Kwatsam wata rana muka wayi gari da rigimar Zayyad da Dayyab akan sai an raba gado an bawa kowa rabonsa, daga ganinsu wani ne ya zuga su, da har Badrah tace na rabu dasu kada na sauraresu ayi banza da al'amarinsu, amma da naji sun ce zasu kotu dole na tsaya na rarrashesu muka zauna akan maganar. Da fari nayi musu hikima irin ta manya nace idan wasu kudade suke bukata sai a basu inyaso sai a rubuta, amma fir suka ki amincewa, haka dole na nemi afuwar Badrah don bayyana gaskiya gudun kada su tona mana asirin gida, wanda bai san abinda yake faruwa ba ma ya sani.

Sai Badrah tace dasu "Dama an riga an raba gadon tun bayan mutuwar Abbanku kadan, komai yana nan a rubuce da abinda ya bari da abinda kowa ya samu da kuma karin da aka samu akai sakamakon juya su da ake yi"

Ta kalleni tace "Iya nasu kawai zaka basu kayi musu bayani tunda su kadai ne suka bukata sauran ka cigaba da juya mana zuwa wani dan lokaci, idan Zayyan da Rayyan sun gama karatunsu, su kuma Yasira da Shukrah idan lokacin aurensu yayi"

Zayyad yace "Eh hakan daidai ne, amma a fara jin ta bakinsu mana kafin a yanke musu hukunci a ari bakinsu a ci musu albasa."

Ya bisu daya bayan daya Yasira, Shukrah, Zayyan da Rayyan yana tambayarsu, su kuwa kowanne yace yana kan maganar Badrah, a ajiye mai dukiyarsa zuwa wani lokaci.

Sai Dayyab yace "To munyi, amma ai dole sai an gaya mana abinda Abba ya bari da yadda aka rabashi da yadda kowa ya samu mun gani baro baro a rubuce ko?"

Sai Zayyad yayi farat yace "Eh mana ai in dai har abinda suka fada gaskiya ne har copy na takardun za'a bamu"

Badrah tayi farat tace "Kai kada kuyi mana rashin kunya! a cikinmu wa zai yi muku karya ko ya cinye muku hakkinku ni ko yayan naku?"

Nace "A'a Ummi rabu dasu zasuji komai"

Naje na dauko takardun nazo na zauna bude na fara jawabi nace "Abba yabar tsabar kudi kimanin 5 billions da kuma gidaje manya guda biyar cikinsu har da wannan gidan da muke ciki, da kuma karamin gida guda daya, sannan kuma ga kamfani. An raba biliyan biyar gida takwas, Ummi ta dauki kaso daya a matsayin tumuninta shine ta samu wannan gida da muke ciki da kuma tsabar kudi miliyan dari shida da ashirin da biyar, sannan kuma aka hade kaso bakwan ya zama biliyan hudu da miliyan dari uku da saba'in da biyar, sai kuma aka raba tara inda Zayyad da Zayyan da Dayyab da Rayyan kowanne zai dauki babban gida guda daya da kaso biyu na kudin da aka raba tara shine kowanne namiji ya samu kudi kimanin miliyan dari tara da saba'in da biyu da dubu dari biyu da ashirin da biyu da dari biyu da ashirin da biyu da kwabanni, sauran karamin gidan kuma da kaso dayan kudin wato miliyan dari hudu da tamanin da shida da dubu dari da goma sha daya dari da goma sha daya da kwabanni, shine kason Shukrah."

Dayyab yayi farat yace "Yaya ina tambaya"

Zayyad yace "Nima idan ka gama taka tambayar nima ina da tambaya"

Na kalli Zayyad, nace "Kaine babba fara tambayarka, ina sauraron ka"

*Alkhamis KSA*

HAWA DA GANGARADonde viven las historias. Descúbrelo ahora