13

45 2 0
                                    

HAWA DA GANGARA

*Daga Kundin ✍️📚✍️*
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman

*page 13*

Yusrah taje ta zauna jiki a sanyaye.

"To ina sauraronki" Shukrah ta fada tana kallon Yusrah.

"Dama nazo ne na baki hakuri akan abubuwan da suka faru tsakani na da ke"

"Wane abubuwa kenan?"

"Nasan abubuwan da nayi miki ban kyauta ba, kwata kwata bai kamata ma a ce ni na aikata su ba, wallahi sharrin shaidan ne da kuma tsananin son da nake yiwa yaya Yasir gani nake kamar za'a barani dashi, amma yanzu ya wayar min da kai shi yasa nace bari nazo na baki hakuri don na dauki hakkinki kadai na mutu da hakkinki a kaina saboda Allah baya yafe hakkin wani akan wani!"

"Kada ki damu na yafe miki dama kuma ni ban rikeki a raina ba"

"To na gode"

"Amma don Allah me yaja hankalinki kika ga ya dace ki bani hakuri mu daina yin wannan abu?"

"Yaya ya bani labarin abinda duk ya faru tsakaninku, da dalilinsa na aurenki bayan alkawarina dake kansa, sai naji kunyar abinda nayi kuma nayi nadama, sannan yace min abin nan da muke yana taba zuciyarsa sosai, sai naga dama duk abin nan da nake yi saboda shi nake yi, shi kuma ga abinda yace, don haka sai na yanke shawarar gara nazo na baki hakuri akan abinda nayi, mu koma kamar da kafin wannan maganar ta billa"

"To Alhamdulillahi, dama nima ba a son raina haka take faruwa a tsakaninmu ba, kuma na dade ina addu'ar Allah ya hada kanmu, domin kwanciyar hankalinmu shine kwanciyar hankalin yaya"

"Gaskiyarki sister, wannan shi yasa nazo mu hade kanmu mu zauna lafiya, mu nemi aljannarmu domin Annabi yace aljannarmu tana karkashin kafar mijinmu, sai mun bishi sau da kafa sannan zamu samu mu dace"

"Wannan ai mai sauki ne sister ki manta da duk abinda ya faru a baya kawai mu fuskanci gaba da alkhairi"

"Kin taba gayawa Ummi cewa ni da ke bama ga maciji?"

"Haba sai kace wata yarinya karama! ban taba gaya mata ba saboda ita uwa ce, ba zata jure duk wani abu da zai batawa abinda ta haifa ba, shi yasa ban taba gaya mata ba, lokacin da muka dawo daga asibiti rannan sai da naji kamar na sanar da ita, amma sai banyi hakan ba don kada ta kullaceki daga baya kuma mu zo mu shirya ita kuma tana jin haushin abinda kika yi min, shi yasa ban taba gaya mata ba"

Yusrah ta dafa kafadar Shukrah, tace "Gaskiya ke 'yar uwa ce ta gari kamar dai yadda Yasira take, Allah yayi miki albarka" sai ta kama hawaye.

Shukrah tana kallonta tasa hannu ta share mata hawaye tace "Haba sister meye kuma na kuka? ai abinda ya wuce ya riga da ya wuce"

Sai su rungume juna cikin farin ciki, daga nan sai su ji kiran sallar magriba, sai Shukrah ta kama hade kan takardunta da littattafan, Yusrah ta taya ta su kwashe, sannan kowacce ta tafi tayi alwala tayi sallah. Tun daga wannan rana suka dinke komai tare suke yi a gidan, hatta zuwa asibiti kaiwa su Yasira abinci tare suke yi, hakan ba karamin dadi yake yiwa Yasir da Yasira da Badrah ba.


*** *** *** ***

Yau ma kamar kullum Yusrah da Shukrah sun kaiwa su Yasira abinci a tare, a lokacin Hajiya Hala tana cikin toilet, suna shiga Yasira ta nuna farin cikinta sosai.

HAWA DA GANGARAWhere stories live. Discover now