11

37 2 0
                                    

               HAWA DA GANGARA

*Daga Kundin ✍️📚✍️*
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman

                       

                        *page 11*

        Badrah tace "To Alhamdulillahi naji dadin hakan, amma abinda nake so da kai idan ka tashi yin auren, ina son ka auri 'yar uwarka Shukrah"

         Yasir yayi saurin kallon Badrah yaga itama shi take kallo, sannan ya kalli Shukrah ita kuma kanta a kasa kamar mai tunanin wani abu, kawai sai yaji gabansa ya fadi, ya maida kallo ga Badrah, yace "Ummi tunda nake ban taba kallon Shukrah a haka ba, ina kallonta a matsayinta na 'yar uwata kuma kanwata"

         Badrah tace "To ai ba wani abu bane tunda baku zauna a mahaifa daya ba, kuma baku sha nono daya ba, kaga kuwa da akwai aure a tsakaninku. Da dai ace Yasira ce ita ba aure a tsakaninta da Zayyad da Zayyan da Dayyab da Rayyan saboda sun sha nono daya"

         Yasir yace "Nasan da haka Ummi, nasan akwai aure tsakanina da Shukrah, to amma da yake akwai alkawarin aure tsakanina da wata!"

         Badrah tace "Wacece ita?"

         Yasir yace "Ba wata bace face Yusrah, mun dade muna soyayya da ita, kuma munyi alkawarin aure tun mamanta tana da rai"

         Badrah tace "To naji, amma ai auren Yusrah ba zai hana na Shukrah ba, kamar yadda auren Shukrah ma ba zai hana na Yusrah ba, zaka iya aurensu gaba daya in dai kana bukatar hakan"

         Yasir yayi shiru daga bisani kuma sai ya kalli Shukrah, yace "Ke yanzu kin amince da hakan?"

          Shukrah tace "Gaskiya nima ban taba kallonka da wata fuska ba face a matsayin da nake kallon Yaya Zayyad ko Yaya Dayyab kuma kamar yadda nake kallon Zayyan da Rayyan, ban taba yi maka wani kallo ba, amma da Ummi ta kawo min maganar, ganin abinda ya faru a shekarun baya da kuma uzurin da Ummi ta kawo da dalilanta, sai naji kawai na amince don gudu ma kada abinda ya faru a baya sake faruwa, kaga idan kana matsayin mijina babu wanda zai sake  rabamu da kai"

         Yasir ya jinjina kai yace "Tirkashi! amma shikenan ba matsala, Insha Allahu ba za'a ji kunya ba"

         A wannan rana haka Yasir ya wuni babu kuzuri, da ya samu guri ya zauna sai ya kama tunani a haka ya wuni. Da daddare yana zaune a dakinsa sai Yasira ta shiga wajensa ko zama bata yi ba sai ga Yusrah itama ta shiga dakin, suna zama sai Yusrah ta watsowa Yasir tambaya, tace "Yaya wai yau me yake damunka ne, gaba dayanka tun safe na lura da sabon yanayi a tare da kai, kana cikin damuwa ko baka fada ba fuskarka ta nuna, me yake damunka?"

        Yasira ta tari zance da cewa "Kin rigani a baki na rigaki a zuci, don abinda ya shigo dani nan kenan amma kafin na tambaya sai kika rigani tambayarsa, yaya don Allah ka gaya mana meye matsalar, nasan ka baka da zurfin ciki, kuma koda ba zamu iya yi maka maganin matsalar ba, ko ba komai ma yi addu'a"

         Yasir ya nisa yace "Gaskiya ne kun fahimci akwai abinda yake damu na, kuma zan gaya muku shi yanzu saboda duk duniya bani da wanda ya fiku" nan take ya sanar dasu duk yadda suka yi da Badrah da kuma Shukrah.

         Yasira tace "To yaya kai kuma me kace musu ka amince ko kuwa?"

         Yasir yayi murmushi yace "To in banda abin ki sister wacce amsa zan bayar in banda nace to"

         Yusrah tayi farat tace "Wai kana nufin ma ka amince? to wallahi ba zai taba yiwuwa ba, ba zan yarda ba! ta yaya zaka yi min kishiya tun kafin muyi aure"

HAWA DA GANGARAOnde histórias criam vida. Descubra agora