Part 24

190 10 4
                                    

*Safeeya sadi (mom Zara) kema ga naki page din comments din ki na jijiga ni irin eh din😘*

*MUNEERA KIN KIYI MANA TYPING MUNEERA.... MUNEERA WLHY ABUBUWAN NE SE ADDU'A ALLAH DAI YA BANI IKON KAMALA MUKU LITTAFIN NAN LAFIYA KAMAR YARDA NA FARA SHI LAFIYA*

Page nawa ma zamu tashi😜😂 auu auu na tuna

*YA ALLAH KABAWA DUK WATA BUDURWA DA BAZAWARA MIJI NAGARI AYI AURE MASU AUREN KUMA ALLAH YA KARA MUSU ZAMAN LAFIYA DA MAXAJEN SU YA RAYA MUSU ZURIA*

*YA ALLAH KA DAFAWA DUK WATA UWA DA TAKE KULA DA YARANTA ITA KADAI BA TARE DA TEMAKON KOWA BA ALLAH ITA KADAI TASAN ME TAKE CIKI ALLAH KA DAFA MATA KA HORE MATA KA BATA IKON YIN KYAKYAWA TARBIYYA*

Page  25

Kallon neehal din kawai takeyi tana bala'e Amma Sam ko kadan ma hankalin ta ba'a kanta yake ba ita juyawa tayi zata wuce ciki saboda maganganun Neehal din sun fara saka Mata ciwon Kai Amma mene Se ji tayi neehal din ta janyo hijab dinta ta dawo da ita baya Dan zabga Mata Mari
Lumshe idanu ilham din tayi tana jiran saukar Marin neehal setayi shiru Hakan yasa ta Bude idon ta Kar Akansa ya rike hanun neehal ransa a bace Yana huci kamar wani bujimin sa

Neehal kokari tayi ta Kwace hannun ta tana ouchh karkaji min ciwo mana honey Akan zan Mari wanan kucakar yarinyar shine zaka nemi illata min hannu.
  Ransa ne ya Kara matukar baci Jin ta Kira ilham da kucaka a ransa Kara jin tsana neehal yake yanzu jibi irin shigar da tayi wanda Hakan yake nuna itace kucaka yau Dan uwansa ko kwana bakwai beyi da rasuwa ba Amma ita harta manta ta cigaba da alamuran ta Kuma a haka ake so ya aureta gaskiya baze iya zama da Nihal ba abun nata ya fara wuce gona da iri.

    Juyawa kawai yayi ya kali ilham wace kawai Kallon su takeyi kallo d'aya zaka Mata ka gano tsantsar damuwa a ta tare da ita

  Hanun ta Yaja Dan su bar wurin Amma setake kokarin fizge hanun ta be damu da Hakan ba ya sake jan hannu suka bar wurin Mamy ney tayi musu magana tare da kiran Ilham d'in tayi wurin ta.

"Ilham kiyi hakuri ki sake hakuri akan rashin Nasir tabbas ni na haifa Nasir amma shakuwan da kukayi dole a tausaya miki addu'a Nasir ke bukata wurin ki ba kuka ba kinji 'yar albarka" hawaye neh suke kokarin zubo mata amma hakan nan ta daure ta share su.

"Ba komai Mamy Allah ya jikan Yaya Nasir Allah ya kai haske makwancin shi"

"Ameen Ilham kije daki dan ki huta kinji" kai kawai ta gyada mata tare da nufa d'akin ta wani irin zafi taji zuciyarta na yi mata wai meh tayi ma Neehal neh haka data t'saneta a rayuwa eta na farko ba harkan ta take shiga ba balle kuma wani hidiman ta why all this hate ganin abun ya neman sata ciwon kai yasata dauro alwala tare da fara karatun al-qurani ku zuciyar ta zatayi sanyi  hakan kuwa da tayi ba karamin taimaka mata yayi ba wurin sanyaya zuciyar ta k'arshe taja wayar ta tare da kiran abin kaunar ta bugu biyu kuwa ya dauka.

"Ilham 'yar baba ya kike?

"Lafiya lau babana ya kuke kuma?

"Muna nan lafiya lau 'yar baba yaya mijin naki da sauran mutanan gidan?

"Suma Baba duk suna lafiya sai dai kewar ku da nayi"

"Nasani 'yar baba muma gobe insha Allah zamu zo garin kano da mahaifiyar ki"

"Babana dagaske kakeyi?

"Yar baba ai kinsan baba baya miki karya ko kin manta neh?

"Babana ban manta ba amma a gidan nan zaku sauka koh? Wani hegen dariya Barde yayi.

"Kar ki damu 'yar baba edan mun tashi tahowa zan kira ki kinji koh yanzu akwai abinda zanyi zan sake kiran ki ko zuwa anjima neh"

"Toh babana" kashe wayar tayi tana mai jin farin ciki duk wata damuwa nata ya kau duk bakin cikin da Neehal ta dura mata ya bace koba komai zataga Barde mahaifina ta abin kaunarta tare da mahaifiyar ta hakan nan ta kishingida tana tunanin Nasir.

Zan eya che muku dukkan su ney ar zaune ar parlon family guda sun hallara ana hidima da kai kawo tabbas Neehal taji wani farin ciki ganin babu Ilham ar wurin sannan kuma gashi babu Abubakar wani tunani ney ya fad'o mata ko suna tare sai kuma tayi saurin kawar da wannan tunanin akan ta ta zage wurin baje baki ana hira.

B'angaran Ilham kam wanka ta shiga tayi ba wata kwalliya tayi  a bayan mai data shafa ma fatar ta doguwar riga che sanye jikin ta sai kuma mayafin dake sanye ar kafadarta ji takeyi zaman eta kadai ya iseta mik'ewa tayi tare da zaran wayarta ta fita yadda take jin hayaniyan su gefen Mamy taja ta zauna bayan ta gaisar da mutanan wurin kuma cike da kulawa suka amsa mata banda Neehal da ta tamke fuskar ta tamau kamar bata tab'a dariya ba Mamy che ta duba Ilham tare da mata magana.

"Yar albarka kawo min ruwa nasha kinji"

"Toh Mamy" wayarta ta daura saman cinyar Mamy tare da yin hanyan kitchen Neehal ma tabi bayanta fitowa tayi da ruwan yayinda ta bangajeta ruwan ya fad'i cup d'in ya fashe wani irin kallo tabi Neehal tana dauke kai tare da k'washe cup d'in ta sake debo wani ruwan yanzu kam Neehal ta fita bata kitchen d'in tana wurin parlon tass sukaji saukar cup ar kasa yayinda duk yawan cin su suka juya ganin menene.

"You bastard idiot mara hankali 'yar kauye kina tafiya baki kallon gaban ki hankali na sama kamar wata rakuma da Allah malama edan kina tafiya ki rika kallon gaban ki ba tafiya kaman na tumakai ba" ba Ilham kadai ba hatta Mamy taji zafin abinda Neehal tayi gudun magana yasata zura ido tana kuma fatan Allah yasa Ilham ta maida mata martani tana wannan tunanin taji maganar ta ar sama.

"Wai Neehal menene haka kin biyoni kitchen kin zubar ma k'washe yanzu kuma kin sa min kafa dana fad'i naji ciwo kuma fa hakan bai isheki ba sai kin had'a da zagi da cin mutunci"

"Iyye 'yar kauye yar talakawa tayi baki harni zaki maidawa martani" d'aga hannu tayi zata mareta taji t'sawan shi.

"You fool how dare you, and what'd hell are you trying to do Neehal I'm tired of this you bullshit ki shiga hankalin ki ki gane dawa kike tare kinsan wacece eta, kinsan matsayin ta ar wurina, duk baki sani ba" all eyes on them kallo ya koma kansu Neehal baki sake take kallan Abubakar jan hannun Ilham yayi ya dawo da eta ta wurin parlon yadda kowa zai ganta tare da jawo Neehal etama.

"Neehal ki shiga hankalin ki Ilham ta fiki matsayi ar wurina ta fiki daraja ar idona kinsan mey yasa Ilham matata che igiyar aurena uku ney ar kanta kinga kuwa ta fiki komai ar wurina watch your tongue and stay out of her life"  Ilham kasa da kai tayi tana jin wani abu na mata yawo ar jiki yayinda Mamy ta mik'e cikin shock da jin maganar Abubakar d'in Neehal kam ta zama zombie bata gane komai maganganun shi ney suke mata yawo akai mata fa yace what no way wallahi.

"Abubakar ka fad'a wani abu daya sani cikin rudani matar ka kace ko mene?

"Yes Mami Ilham matata che tun ranar dana kawota cikin gidan nan take mazaunin matata ar ranar kaddarar auran mu ya fara ar ranar kuma Allah yayi ikon ta zama matata gata zata fad'a miki da bakin ta wannan dalilin ney yasata janye wa Nasir bayan ya furta mata kalmar so" tunani Mamy ta shiga yi kafin wani murmushi ya subuce mata ta janyo hannun Ilham tana shafa fuskarta.

"Ilham shin maganar da Abubakar ya fad'a gaskiya che? Kunya ta gama kamata ji takeyi kamar ta nutse ar kasa amma babu yadda zatayi hakan nan ta bud'e baki.

"Ey Mamy gaskiya ney abinda ya fad'a" wani irin hamdala Mamy ta saki cikin ranta dan tabbas tana kaunar Ilham har cikin ranta to amma wacece eta Ilham d'in magana tayi ma Abubakar ya zama Neehal kuwa ar guje ta ruga d'aki tana kuka.

*Fadimatou*

GUDUNA AKEYI Where stories live. Discover now